BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

 Suna dining ya tuna da Dad yace da safe suzo da  Baby can gida, To taya zai tafi da ita gida haka tana wannan tafiyan da k'yar, wani tunani ne yazo mai ya d'auki wayarsa ya kira Dad d'in, bayan sun gaisa yake fad'a mai abinda yasa basu zo ba  Baby ya dawo yasamu tana zazzab'i har yanzu bai sauka ba, yace to zasizo da dare su dubata.

    Yau kam yinin ranar cikin soyayya da tattalin juna suka k'arar dashi dikkan motsinta akan idonsa ji yake kamar ya maidata ciki don so da k'auna,

Da yamma tare sukai wanka sika shirya cikin shadda shi milk calor ita light blue d’inkin doguwar riga tayi kyau matuk’a mirna dik ta cikata Dad zai zo, shi dai Bilal tuna mata yake da insunzo tai kalan rashin lfy don yace musu bata da lafiyan.

Wayyo Allah ina zata sa ranta don farin ciki lokacin da Dad yazo ta ganshi tare da maminta harda momyn Bilal sai wani mutum abayan Dad dattijo ne Wanda shekarunsa zasu kai hamsin da takwas zuwa sittin kana ganinshi kaga kyakkyawàn bafulàtani, da kamar zata kwasa da gudu ta taresu amma k’afanta ta tuna mata halin da take ciki da kuma shirin Bilal don haka ta tsaya cak har sika iso mami taje ta rumgumeta tana mata sannu,
Bayan sun zauna an gaggaisa sun mata ya jiki ta amsa ka an mar gaske,
Bilal da kànsa yaje ya kawo musu abubuwan motsa baki suka tattab’a,

Baby idanuwanta nakan wannan dattijon tunda ta ganshi  taji tsikan jikinta ya tashi tana tunanin a ina Dad ya samo wannan Dattijon,shima idanunsa  na kanta kallon juna sike afakaice.

Dad ne yai gyaran murya ya fara magana " Da farko dai zan k'ara godewa Allah bisa tarin ni'imominsa garemu awannan lokaci ma ga wata ni'imar ya k'ara mana,Khausar wannan bawan Allah da kika gani Baban kine domin kuwa yayan mahaifiyarki ne cikinsu d'aya da ita"

Da sauri ta maida kalloñta gareshi ido cikin ido suke kallon juna haba sai yanzu ta gane dalilin fad’uwar gaban dataji tunda ya shigo, kallon sanin da take mai tanajin kamar ta tab’a ganinsa ashe kamannin fuskar mahaifiyarta ne da take gani a hoto,wayyo Allah dad’i ashe arayuwa tanada rabon ganin jinin mamanta,abinda ta dad’e da fidda ranta akansa, hawaye ne na farin ciki ya fara bin kuncinta ta mik’e ta k’arasa gabansa ta tsugunna tare da rik’e hannayensa ta shiga rera kuku,shima kukan yake na tunawa da ya’r uwarsa da yayi – – – – – .

Taku ce
Layuza kabir Adam????‍♀
. ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR

    NA

LAYUZA KABIR ADAM

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
(we are here to educate,motivate and entertain our readers)
????????????????????????????????????

        1⃣1⃣7⃣

Kuka suke dik su biyun d’akin yai tsit kowa jikinsa yai sanyi ,Dad ne yai k’arfin hali ya d’aga Baby ya maidata mazauninta sannan ya kalli Baffa Adnan yace ” Baffa kayi hak’uri Hadiza addu’a take naima agunku”
Face hanci Baffa yai yace”Bari kawai Aliyu ina tausawa wannan yarinya ne sannan ina tuna y’ar uwata mun rabu cikin rud’u da yak’i daya cimu ashe mun rabu kenan ‘dikkan danginmu mun k’ara had’uwa hadiza kad’aice bata dawo cikin mu ba ashe ta tafi kushewa”

Rarrashinsu dai Dad yai tayi bayan duk sun tsagaita Dad ya dubi Baby yace” Baby na d’au tsawon lokaci ina neman hanyar da zan nemo miki dangin mahaifiyarki nayi nayi ban samu wani labarinsu ba’ to awannan karon labari tazomin garin ya k’ara had’uwa zaman lafiya ta wadata bayan tsawon shekaru da suka d’auka a tarwatse, da na baza jama’a na basu sunan kakanki da sunan k’auyensu cikin yola ahankali aka nemomin su da wajan zamansu to cikin ikon Allah na d’auki Bilal mukaje garesu nai musu bayanin komai tare da nuna musu hotunan Hadiza don su gamsu sosai to don haka wannan bawan Allah Baffa Adnanu ya biyo mu don yazo yaganki yaga mazauninmu sabida inya koma su taho tare da saurian y’an uwa’ nai musu bayanin kina shekaran k’arshe na karatunki ba daman ki je garesu sai dai in kun samu wani hutun sai kije kiga ya’n uwanki ki zagayasu amma kafin nan duk zasu zo su ganki”

Ajiyan zuciya Baby tai sannan ta fara”Dad bazan gaji da godewa Allah daya azurtani da mahaifi irinka ba koda yaushe burinka kaga farin cikina na gode matuk’a, Abu na gaba Baffa Adnanu ina godewa Allah daya nuna minku yasa inada rabon ganinku kafin inbar duniya,Dik da rashin mahaifiya babban rashi ne ga d”an Adam hak’ik’a mamina ta share hawa yena ta zamemim uwa majinginar d’a mami bata barni naci gaba da kukan rashin uwaba,don haka Baffa ni marainiyace me tarin gata karkasa tunanin wane irin rayuwa nai “

Hamdala ga Allah Baffa yai farinciki fal ransa,
Nan dai sukaita hira yana bawa Baby labarin danginta da irin rayuwar da sukai,

Baby yau kam kamar sallah don murnarta bata b’oyuwa,

Sai wajan goma sukai sallama suka tafi”

Bayan sun rakasu sun dawo suna shigowa parlourn ya rungumota ta baya yana goga mata k’asunbar sa a wuyanta, mak’ale kanta gefe tai tana D’an mirmishi, “my blood ki goyani ki kaini d’aki na gaji bazan iya k’arasawa ba”

Dariya tai tace” Tab yanzu inna goyaka Ai bayana karyewa zaiyi broth”
“Waya fad’a miki ki gwada ki gani Ai mata suna da k’arfi dik nauyin namiji suna d’auka “
Jijjiga kai tayi tace”a a to nidai bani da k’arfin dazan d’aukeka”
Juyo da ita yai ta gaba ya kama hab’anta yana kallon cikin idonta yace” kina da k’arfi Baby don jiya kin d’auke dikkan nauyina”
Da sauri tasa hannunta a idonta tana bibbiga k’afa cikin shagwab’a tace”um um ni ban san wannan zancan broth don Allah ka daina”

Cikin dariya yake fad’in “Allah gaskiya na fad’i kuma kema kin sani”.tureshi tashigayi zata gudu yasa hannu ya d’agata sama cak sukai d’aki.

Bayan sunyi shirin bacci suna kwance a gado kanta yana bisa k’irjinsa shi kuma yana wasa da gashinta ahankali yasa bakinsa a kunnanta yace”badan karna takuraki ba da na nemi k’ari yauma”
Shuru tai bata amsa ba amma saida taji k’irjinta ya bada dammm,
Karo na biyu ya k’ara mai mai tawa , kukan k’issa ta fara tana fad’in “broth kaima kasan fa banda lafiya kasan halin fa da nake ciki kana ganin kafana ma da k’yar nake iya d’agawa”
Bayanta ya shiga pitting yana shafa gashinta da d’ayan hannun”shike nan is ok kiyi shuru ba abinda zan miki kiyi baccinki”

Cikinsu ba Wanda ya k’ara magana sai dai ya k’ara k’an k’ameta jikinsa yana jin d’uminta na ratsashi hankalinsa ya fara tashi amma ya danne ransa da zalamarsa ahaka bacci ya d’aukesu.

Yau kam da wuri suka tashi don Baby tana son zuwa skul,tare sukai wanka suka shirya sannan suka fito dining suka karya, tare suka fita ya ajiyeta a skul d”in shima ya wuce office don yasan zai samu aiki sosai,

Lokacin dataje su Aisha duk sunje isy tana lector Aysha kuma tana bakin hole zaune bata shigaba don lecturer d’in bai k’araso ba ,
Ahankali ta k’arasa gunta,

Dariya taga Ayshan nayi tace”ya dai sis da dariya”

Rufe bakinta tai tana fad’in um um ba komai”
Gyad’a kai tai ta sami gu ta zauna,
Hira sukeyi nan ta bata labarin ganin dangin mamanta da zuwan Baffa Adnanu murna sosai Aysha tai mata tace”kice munada zuwa yola da mun cinye wannan semester d’in”
“Eh insha Allah randa mukai Hutu sai ya k’are zan dawo”
Zuwan lecturer d’in ne yasa suka tashi.

Bayan sun tashi kamar yanda Bilal yace ta wuce gida gun Baffa suyi hira su k’ara gaisawa Inya tashi a office zai biyo ya d’auketa don haka tace Islam ta sauketa gida tace itama ai gidan zata je ta gaida Baffan,jin haka Aisha ta je ga office d’in doctor Al’ameen ta nemi izinin binsu Baby don gaida Baffan itama ba musu ya barta don haka suka d’ugunzuma zuwa Gidan.

Baffa Adnanu mutum ne me Sabo da son mutane gashi yanada hira don haka ya sa su agaba sukaita hira yana basu labarai kala kala,
Bayan la’asar su Islam da Aisha sukaja motocinsu ko wacce tai gidanta,
Baby kam k’ara zama tai ga Baffanta yana bata labarin yak’in garinsu, wani abin inya tuna yana fad’a mata yana kuka itama sai matsar ido take.

Sai bayan magriba Bilal yazo suka taho gida.
To haka tsawon kwana uku Baby daga skul agida take yini sai dare yaje ya d”aukota don haka ad’an kwanakin suka shak’u da Baffa take k’ara jin itama yanzu ta zama cikakkiyar y’a me dangin uwa Dana uba.
Kwanan Baffa biyar ya shirya tafiya, kayan tsaraba sosai Baby ta shirya mai kayan sawa nashi da Wanda zai rabawa dangi ,Dad kuwa kayan abinci ya cika masa but dashi yayin da Bilal ya samai kud’i dubu Hamsin cikin envelop ya bashi,Mami ma da momy sun had’a mai tsaraba, aranar Baby sukai sallama dashi.
Washe gari k’arfe bakwai na safe driver yajashi suka d’au hanya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button