BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari da safe bayan an kawo musu kayan breakfast dik sun gama inna ta sanar dasu dik yanda sukai da Baby nan sukaita mata godiya dasa albarka.
Taku ce
Layuza kabir Adam????♀
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
????????????????????????
ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร
???? Zaku iya samun littafan mu a Facebook ????????
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
???? Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu ????????
Zamaniwriterassociation@gmail.cocom
1⃣1⃣9⃣
Ranar ma cir yini sukai hira cikin so da k’auna irin na yan’ uwantaka.
Yau kam tun yamma Bilal ya dawo gidan don haka ana sallar magriba ya kirata waya akan ta shirya su wuce ba musu ta amsa,mik’ewa tai tana fad’in “To y’an uwa zan gudu saida safenku amma don Allah goben Ku shirya da wuri don naiwa drivers d’in magana k’arfe tara tai muku a gidana don Allah”
Inna asabe ce ta rik”e hab’a tare da fad’in”haba khausar sai kace abin tashi sama karfe tara muzo gidanki ina laifin goma zuwa sha d’aya”
Mami dake gefe tai dariya tai tare da fad’in”Baby rigima kedai wuce kawai sai da safe”.
Amota saida ya biya da ita manya manyan stores tai siyayyan abubuwan da zata shirya na Taransu agidanta,
Basu je gidaba sai k'arfe goma suna zuwa Bathroom suka shiga tare sukai wanka sukai alwalan sallar isha'i bayan sun fito yajasu jam'i suna idarwa ya rik'eta suka haye gado don basu da buk'atar cin abinci, tsam yasata ajikinsa yana magana k'asa k'asa"My blood nai kewanki da Yawa jiyama haka na kwana abin tausayi inata juyi sai pillows naita runguma"
Shafo fuskanshi tai cikin sauyawan yanayi take fad’in my spouses I’m missing u s – – – much”
K’ank’ame juna sukai kamar zasu maida junansu ciki, wasanni ya fara mata tana maida mai martani cikin zak’uwa ahaka abuwa suka mik’a cikin so da faranta ran juna.
Tunda sukai sallan asuba ta tafi kitchen gun masu aiki inda ta taddasu a kitchen d’in kamar yanda tai misu umarni su shirya k’ayatattun girke girke don tarar danginta,hannu tasa suka ci gaba da aikin har zuwa k’arfe takwas sannan ta koma d’aki nan ta tadda shi bai tashi ba don indai week end ne bai tashi da wuri, bathroom ta wuce tai wanka ta fito ta shirya cikin Riga da zani na atanfa super d’inkin rigan yai mata d’ass,fitowa tai balcony d’in gidan inda ta bawa maaikata Maza umarnin suyi decorating d’in filin ta fito musu dik abinda zasu shirya ta koma zuwa d’akin ta zauna jikinsa tana shafa fuskanshi zuwa wuyansa , ahankali ya bud’e ido sukaiwa juna mirmishi ta ruk’oshi ya tashi toilet suka wuce ta had’a mai ruwan wanna sannan ya cire kayansa, ta juyo zata fita ya ruk’ota “ina zaki ki tsaya ki tayani”
Shagwab’e fuska tai tana fad’in ” um um spouses kaga na shirya inna tayaka zan jik’a jikina kaga kuma fa bak’inmu sun kusa zuwa”
Kissing d’in hannun yai ya cikata yana mirmishi,ta fice tana dariya.
Bayan sunyi breakfast ta kira number d’in Hassana tace”haba mana y’ar uwa yaushe zaku taho ne harfa goma tayi”
D’aya b’angaran Hassana ta amsa”gamunan mun shirya “
“OK sai kunzo”
Wajan sha d’aya mota uku na gidan suka kawo su da murnart ta taresu dik parlour ta saukesu tashiga gaidasu cikin farin ciki, Bilal ma ya gaidasu cikin girmamawa nan Kawu jamilu ya shiga yimusu nasiha kan zaman aure yana k’ara jan kunnan Baby kan bautar aure.
Sun baje sunata kwasar hira daga bisani ta jasu zuwa gunda ta shirya musu yin kwaryakwaryar walima , bayan anci ansha anyi k’at suka koma ciki taita zaga dasu cikin gidan.
Yinin ranar duk agidan sukayi shi daga bisani drivers suka maidasu gidan Dad d’in.
Kwana hud'u suka tafi tare da tarin kayan arziki da alk"awarin da Khausar ta musu.
Bayan wani lokaci rayuwan Baby da Bilal tana tafiya cikin so da k’aunar juna , alokacinne Aisha ta sanar dasu Baby tanada ciki farin ciki tsam ransu da dare Bilal na dawowa ta tareshi da zancan mirmishi yai ya rungumota yana mata rad’a “kinga su sunada himma ita da Islam amma ke kink’i maida hankali ki d’au darasin da naketa koya miki”
Turo baki tai tana d’an buga k’afa cikin shagwab’a “nidai wlh ba rashin maida hankali bane nifa “
D’ago hab’anta yai yana kallon idonta” to mene ne ragwantane”
Tureshi ta farayi tana juyawa ya ruk’ota “yi hak’uri Baby nah da wasa nake ke jaruma ce”
D’an mirmishi tai ta ruk’o hannunsa suka shige d’aki.
Ranar wata lahadi yace ta shirya suje Bici gidan Aunty ameera yayarsa suyiwa mijinta murnar cin zab’e da yayi na d’an majalisa tun takwas na safe suka tafi don suje su dawo da wuri, da kanshi yai driving d’in suna tafe suna hiransu cike da so da kauna.
Cike da girma da karamci aka taresu Aunty Ameera tanata murnar ganinsu, mijintama yaji dad'in zuwan nasu, wajan k'arfe d'aya bayan sunyi salla sunci abinci suka mik'e don tafiya Ikram ta mak'alewa Baby wai saita bisu akai akai tace ita saitaje gisansu,Abbanta yace "Bilal kuje da ita tunda anyi hutun skull idan tai sati d'aya zanzo in d'auketa"
Mirna tai tayi Baby cike da murna tace”To Aunty had’o mata kayanta”
Sun d”auko hanya sosai Ikram dake baya sai surutu take zuba musu suna Kwasan dariya don yarinyar akwai surutu da wayo bacci ne ya fara d’aukan Baby don yanzu bacci bai mata wahla kwantar da kujeran tai tana lumshe ido kallonta yai da alamar Tambaya “spouses bacci nakeji”
“OK to yi baccinki”
Maida kansa yai ga tuk’in yasa hannunshi daya yana matsa cinyanta,
“Lah Auncle wai Aunty ma yarinyace kake rarrashinta tai bacci”
Dariya yai ya a babba ce batada lafiya ne”
“Yanzufa ta gama hira kace batada lafiya”
“To yi shiru karki tasheta”
Tsit tai bata k’ara magana ba har suka iso gida.
Zaman ikram ba k’aramin dariya yake sasu ba intana surutu kamar babba, wata rana da dare Bilal ya dawo Baby na bud’e k’ofa ya d’agata sama yana juyata sannan ya direta tare da zira harshensa a bakinta suka shiga kissing juna, dariya sukaji abayansu tana tafi”eeehhhhhh Auncle spouses suna wasan y’an India da Aunty my blood”
Atare suka juyo suna kallonta Bilal yai k’arfin halin fad’in cikin tsawa “ke wayace kizo nan wuce ki koma d’aki kona bibbigeki da d’an banzan surutu “
Da gudu ta shige ciki a tsorace da tsawan da yai mata.
Kallon Baby yai yace”maida yarinyar nan zamuyi tun kafin ta b’aro mana babban zance ke da
d’aki d’aya muke kwana da ita ai da tuni ta fad’i komai”
Mirmishi tai sannan ta wuce d’aki .
Bayan sunzo kwanciya ta kalleshi da tsokana tace"Auncle spouses me wasan y'an India"
Matseta yai yana dariya"kai ai wannan yarinyar sai ahankali ai zancewa Mamanta tasa Babanta yazo ya d'auketa kawai"
“A a ka barta yaufa kwananta hud’u in tai satin zaizo ya d’auketa”
“To ba ruwana nidai”.
Dikkan yanayi dake damun Baby kasancewar ta doctor yasa ta gano ciki gareta amma saiya taja bakinta tai shiru,
Randa Ikram tai sati babanta yazo ya d’auketa.
Bayan wata biyu su Baby sunyi exam sun gama ya rage musu semester d'aya su had'a karatun su duka su fito acikakkun doctors.
Shirin tafiya Adamawa yola take Wanda zata samu rakiyar mami Islam da Aisha tare da Bilal amma su kwana d’aya zasuyi su juyo, kwana biyu ya rage su tafi ,yau tai niyan sanar da Bilal tanada ciki don haka ta shirya k’ayatacciyar letter ta rubutamai kalaman soyayya sannan ta sanar dashi tanada cikin wata hud’u,acikin briefcase d’insa tasa mai bayan ta rakoshi bakin mota ta lek’a kanta jikin window tana d’an mirmishi tace”akwai ajiya a jakanka in kaje ka duba”
Shafan fuskanta yai yace”OK saina dawo”
D’aga mai hannu tai ya fice.
Taku ce
Layuza kabir Adam
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
????????????????????????
ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร
???? Zaku iya samun littafan mu a Facebook ????????
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
???? Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu ????????
Zamaniwriterassociation@gmail.com
1⃣0⃣2⃣0⃣
Bayan yaje office saida yai wasu y’an aikace aikace wajan k’arfe goma ya d’auko jakansa ya d’auko takardar da tasa mai da k’warin gwiwa ya bud’e kalaman soyayyan data rubuta afarko shi yafara karantawa yanata mirmishi sannan ya yazo ga labarin farun cikin ji yai kamar yana yawo Asama don wani mad’aukakin farin ciki daya ziyarci rayuwarsa,ya kife yana mai yin sujjada ga ubangijinsa( sujudushshukur).
Godiya yaita mik’awa ga ubangiji harda hawayensa.
Tashi yai da sauri ya d’auki key d’in motansa ya rufe k’ofan ya fice batare daya waiwayi kowa.
Yana shiga gidan ko parking bai gama dai daitawa ba yai ciki da sauri harda d'an gudunsa,maaikatan gidan dik makaki ya kamasu sika fara tunanin Allah dai yasa lafiya.
Tana d’akin tanata shirya kayanta cikin k’atuwan trolley back,bataji motsin saba saida ya turo k’ofan ya shigo juyowa tai tana kallansa ya kafeta da ido kafin daga bisani ya tako da sauri yazo gabanta tsugunnawa yai tare da d’aga riganta ya zubawa cikinta ido Wanda babu alamar akwai baby aciki, mirmishi yai ya tura fuskanshi cikin nata ya shiga kissing ba k’akkautawa, hannu Baby ta d’ora kanshi tana mirmishi ahankali ya mik’e tsaye yai mata kyakykyawan runguma,
Tsawon lokaci suna rungume da juna sannan ya cikata ya zauna bakin gadon tare da d’orata kan cinyarshi “Baby bansan me Zance ba halin farin cikin da nake ciki ya zarta tunanin dikkan me tunani,Baby wai ni Bilal ne zan samu d’a in zama Abbah,Allah na gode maka ina kara gode maka Allah Kaine abin godiya babu maiyin wannan kyautar sai kai satkinmu Allah”
Hannunta tasa kan leb’ansa tana fad’in “Broth don Allah karka fad’awa kowa wlh inajin kunya kaji”