BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

” Hhhhmmm Baby nah abin farin ciki ake fad’a ban San ta yanda zan b’oye wannan kyautar ba”
Turo baki tai tana buga kafa cikin shagwab'a tace "Allah broth ina jin kunyanefa"
K’ara rungumeta yai yajata jikinsa suka kwanta daga nan suka Lula cikin making love.
Aiki dai bai koma ba yinin ranar haka yaita mutsikata tun tana tayashi harta fara guduwa,
Da dare ya d'au Waya yace"Bari in kira Dad in fad'a mai zaiyi jika very soon"
“Ka bari don Allah ba yanzu ba sai ya kara girma duk zasu gani”
Mirmishi yai yace”To amma fa in basu kula ba zan sanar nanda wata guda”
“Eh na yarda”.
Haka ranar tafiya tazo suka shirya sai yola yamma lis suka shiga garin akai musu tara ta girma da d’aukaka agidan Baffa Adnanu don goggo ma agidansa take da zama tun rasuwar me gidan nata.
Had’addiyar fura aka kawo musu me sanyi tare da danbun shinkafa da gasassun zabi tare da girkuna kala daban daban daga gidajan yan kuwa,
Har dare gidan Baffa bai sarara ba da yan sannu da zuwa, suna masaukinsu mami ta kalli Baby tace”kai gaskiya Fulani akwai karrama baki ji yanda suke tarairayarmu kamar su maidamu ciki”
Mirmishi kawai Baby keyi tana godewa Allah bisa ni’imarsa daya had’ata da dangin mahaifiyarta.
Bilal ne ya shigo zai tafi makwancinsa yaiwa mami sallama dasu Sis Aysha ya kalleni ta gefan ido yana mirmishi, dariya kawai nai don nasan me yake nufi nace”saida safe Allah ya tashemu lfy”
“Ameen “yace ya fice.
Da safe ma haka aka cikasu da kayan breakfasts sai abinda kaso zakaci dikda ba wasu masu k’arfi bane amma sunada rufin asiri dai dai gwargwado.
Kwanan su Mami biyu suka tafi Bilal cike yake da tsananin kewa dik yai wani kalan tausayi itada haka ta lallab’ashi suka rabu.
Baby zagawa take cikin y’an uwa na nesa da kusa har tsawon sati guda Wanda ya rage mata kwana goma ta koma gida don tace saiya rage kwana biyu su koma skull zata tafi, yau Aunty madeena ya’r Baffa Adnanu tazo gida ta yini da dare zata tafi tace”Baby shirya mu tafi nima kimin kwana biyu”
Da Baffa ya hana amma ganin Baby nason zuwa ya barta suka tafi, dik Matan danginsu Aunty madeena tafisu rufin asiri don miji me kudi sosai take aure kuma yana sakar Mata don itace ma karfin gidansu.
Suna zaune sunata hira A parlour me gidan ya dawo shima ya zauna yana taokanan Baby”gaskiya khausar garinmu ya k”arb’eki ji yanda kika xanja”
Dariya kawai tai don tasan Abban Ni’ima akwai tsokana haka sukaita hira har Bilal yakirata awaya ta tashi ta shiga d”aiki,
Suna Waya ya shagwab’e murya”My blood wlh ji nake kamar zan mutu don kewanki marana ciwo kullum takemin”
K’asa tai da mirya tace”nima cike nake da kewanka my spouses bana Iya bacci ko kad’an in dare yai sai dai inta juyi”
“Ki rage kwanakin da zakiyi don Allah”
“A a kayi hakuri kaga inna dawo Zan dade banzo ba”
“To shike nan amma yanzu ki bud’e datanki muyi hira sosai ki shirya yau kwana zamuyi muna chart ammafa ki tanadi kalaman da zakimin Wanda zasu ragemin kewa in sami sassauci”
Tasan me yake nufi don haka cike da tsokana tace”To kawai ka taho mu kwana tare”
“Da gaske aida zan sami jirgi yanzu zaki ganni yanzun”
“To ka tuko motanka mana”
” Hhhhmmm Me zaki bani innazo?”
“Zan baka dikkan farin ciki zan baka kaina in cikaka da soyayya kaga gashi daman twens d’inkama sunyi kewanka sosai”
“Da gaske sunyi kewana?”
“Eh mana har fa hanani bacci sukeyi”
“Me sukeyi ?”
“Um um saika gansu zakaga yanda sika Rame sabida rashinka”
Mirmishi yai yace”bud’e datanki in turo miki wani Abu”
“OK” tace tana cire wayan a kunnanta, soyayya suke sosai cike da kewa don kalaman da suke jifan junansu dashi zai tabbatar ma da hakan har sai karfe biyu sukai sallama.
Gaba d’aya bacci ya k’auracewa idon Baby juyi kawai take cike da tsananin sha’awan mijinta sabida ya motsota da kalamansa, shawaran data yanke ta mik’e ta d’auro alwala tozo tai sallah raka hud’u sannan ta d’auki ruwa tasha tai niyan yin azimi nafila don dama daran alhamis take.
Da safe Aunty madeena taga har k’arfe tara Baby na bacci tazo ta tasheta tana fad’in”Khausar ki tashi kiyi breakfast saiki koma”
Juyi tai tace”Aunty azimi nakeyi ki barni bacci nakeji sosai”
“To ayi bacci lafiya ya’r kuwa”
Ta juya ta fice tana jamata kofan.
Sai goma da rabi ta farka kai tsaye ta shiga toilet tai wanka tazo tai kwalliyanta mai sauki tasa,riga doguwa ta yafa mayafin rigan ta fito parlour, nan ta tarar da Aunty madeena ta kalleta da mirmishi tace” a a mrs Bilal sannu da bacci”
dariya tai ta zauna tana fad’in “Aunty barka da safe “
“sannu da tashi ya azimin,ai bansan kinayiba na shirya miki break fast”
“eh wlh nima sai cikin dare ba d’aura niyanyi”
“ok to allah ya had’amu a ladan”
nan ta zauna sukaita hira har lokacin dauko ni’ima daga skul yai Aunty madeena ta tashi tana fad/in “Bari inje in d’auko ni’ima yanzu zan dawo”
“to saikin dawo”.
bayan kamar minti biyar da fitan Aunty madeena taji ana knoking axatonta ma ita ta dawo ta mik’e taje ta bud’e kofan ! wa zata gani tsaye ? Bilal tsoro ne taji ya kamata aranta tace “Broth harya fara min gizo sabida kewansa danayi?”
amma a fili saita shiga mitsika ido tana son tabbatar da zarginta,
ganin da yai kamar bata ma ganeshi ba yasa ya tako a hankali zuwa gareta ya furta “bikiyi farin ciki da zuwa na ba ko Bloody tsorona kika jima ko?
runtse ido tai ta bude tana fad’in ” wai gaske my lovely broth kai kake magana yanzun”?
ahankali yajata jikinsa yai mata
wani kyakyawan runguma . . . .
.
Takucee
layuza kabir Adam
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
????????????????????????
ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร
???? Zaku iya samun littafan mu a Facebook ????????
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
???? Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu ????????
Zamaniwriterassociation@gmail.com
????????????????????????????????????
1⃣2⃣1⃣
Jinta kwance a k’irjinsa ya tabbatar mata da ba gizo yake mata ba itama k’ank’ameshi tai tana sauke ajiyan zuciya, tsawon lokaci suna tsaye rungume da juna ya d’ago fuskanta yana kallon idonta dake a lumshe ya hura mata iska afuskanta k’ara lumshe idon tai tana fad’in “ohhccc my . . . “
bata k’arasa ba ya d’ora bakinsa kan nata da zummar yayi kissing nata, da sauri tai baya tunawa da tai tana azimi kuma agidan mutane suke adai dai lokacin ne kuma taji tsayuwan motan Aunty madeena, jawo hannunsa tai zuwa cikin parlourn ya zauna kan kujera taje ta d’auko mai lemo da ruwa tare da cup, Ni’ima ce ta shigo da gudu d’auke da jakanta tana fad’in “Aunty Baby na dawo nazo miki da sweet”
ajiye kayan hannunta tai ta d’aga ta sama tana fad’in “oyo yo ni’ima ta dawo”
a lokacin Aunty madeena ta shigo karaf idonta akan Bilal dake zaune ta bud’e baki cike da mamaki tace”Bilal yanzu baka iya hak’urin harta dawo shine ka biyota dika yaushe kuka koma”
bakinsa d’auke da dariya yake cewa ” Aunty madeena kinga lefina ? sati guda bana tare da ita don haka yau nai sammakon biyo jirgi”
“To ya akai kasan tana nan gidan ?”
dariya ya k’arayi yace ” Ina sauka acan Baffa yacemin tana nan gashi gidan ba kowa da an rakoni nace a’a zan gane tunda randa zamu tafi munzo nan don haka kawai na sami mota ta kawoni “
“lalle kayi k’ok’ari to sannu da zuwa “
“yawwa Aunty ya gida ya yara “
“gasu Alhamdulillah ya kukaje gida”
“lafiya qlau”
“To madallah”
kallon Baby tai tace “Khausar ki zuba mai ruwan mana yasha kin biyewa wannan sarkin surutun “
lemon ta zuba mai tana fad’in “broth Dad yasan ka taho?”
“a ‘a bai sani ba haka nace mai naje duban wani obokina a jigawa gobe zan dawo”