BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

 yanzu kam da gaske ta ke kukan tana bubbuga mai kanta tana da fad'in " wlh kaine ka rik'eni da k'arfin tsiya kayi abinda kake so ka b'atamin azimi na  amma ni ko ma . ." shiru tai bata k'arasaba don zuwa yanzu kukan gaske take,

ganin hawaye shar yana gudu a idonta yasa ya shiga rarrashinta yana bata hak’uri ” Don
Allah bloody kiyi shiru kiyi hak’uri na rabaki da aziminki ni da wasa nake nima nasan ni namiki fin k’arfi amma ba’a son ranki ba nima rashin hak’uri ne irin nawa dana kyaleki gashi harma anyi sallan”
shiru tai tana sauke ajiyan zuciya a wahalce don k’ishin ruwa takeji matuk’a ga wata azababbiyar yunwa da take saka d’anta ga gajiya, mirya a dashe tace “zansha ruwa “
da sauri ya tashi ya bud’e ledan da sukazo dashi ya d’auko mata ruwan faro ta bud’e yasa mata abaki ta mummud’a tasha da yawa sannan ya janye ya bata fresh milk shima tasha kad’an yace “bari inyi waya reception akawo miki wani abu me d’imi .

Taku ce
Layuza kabir Adam????‍♀
. ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????
BABY KHAUSAR

      NA

LAYUZA KABIR ADAM

????????‍????????????‍????
ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​​

​???? ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ ????????
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

???? ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ ????????
Zamaniwriterassociation@gmail.com

????????????????????????????????????
Allah Ubangiji me yanda yaso asanda yaso ina godiya gareka daka bani ikon kammala littafina na ‘BABY KHAUSAR’
wanda na d’au tsawon lokaci ina rubutashi to gashi yau na kammala Allah kaine abin godiya ,
ina k’ara godiya ga masoyan wannan novel bisa jimirin bina da kukai tsawon wannan lokaci tun daga ranar 7/9/2017 har izuwa wannan rana ta 13/2/2018 hak’ik’a kunyi hak’urin bina tsawon watanni bazan manta daku ba mosoyana muna tare ???? tsawon rayuwa kuna raina ❤,
kasancewata sabuwar marubuciya yasa na d’au wannan lokaci amma ina fatan littafi na gaba me taken (YAN’ ARABIC )in kammalashi cikin gajeran lokaci????,
Bazan manta da gudunmawarku gareni ba akan wannan rubutu ????

1- FATI AFREEN
2-ZAMANI WRITERS ASSOCIATION,
da bazarku nake rawa,

Ina rok’on Allah ya yafemin dikkan kuskuran da nayi acikin rubutuna abinda na rubuta dai-dai Allah ya bani ladanshi amin.
????????????????????????????????????????

       1⃣2⃣2⃣

Abinci aka kawo mata tare da farfesun kayan cikin rago abaki yake bata tana jikinsa yanayi yana mata hira me dad’i harta kammala ya kwantar da ita yaje Bathroom yai wanka a gaggauce daya fito har an fara kiran isha’i ya d’aga ta zuwa toilet yace” kiyi wanka ki d’auro alwala maza kinga mun makara har an fara isha’i “
fitowa yai ya tada sallan magriba bayan ya idar itama ta fito tai sallan magriban sannan yajasu jam’i sukai isha’in bayan sun idar ta dubeshi ” saimu hanzarta mu koma ko “
girgiza kai yai yana mirmishi “a’a ai anan fa zamu kwana ba inda zamu koma”
d’an zare ido tai cikin mamaki tace”ban ganeba “
“eh yanda na fad’a haka nace anan zamu kwana “
“haba mana my spouces ya zamuyi haka ai sai aga rashin kunyarmu “
“a’a ba mai ganin hakan kawai dai munyi missing juna ne dole mu gwangwaje abinmu mu kwana muna ummmm”
ruk’o hannunsa tai cikin shagwab’a tace “my broth ka rufamin asiri kasanma cikin fulani muke abu kad’an suke ganin rashin kunyar mutum”
“ba wani abu nasan dabaran da zanyi”
wayanta ya d’auko ya fara deling number Aunty madeena dayaga tai seving bayan ta d’auka yace “Aunty madeena kinjimu shiru ko muna masaukina ne don Allah kiyiwa Baffa waya ki sanar dashi Baby tana gidanki ni kuma na tafi masauki”
dariya tai tace” Ai kuwa yanzu yamin waya wai kana gidan nawa ne nace eh”
“yawwa Auntynmu inya k’ara kiranki don Allah saiki fad’amai abinda nace”
“ok ba damuwa Allah ya tashemu lafiya”.

bayan ta gama wayan ta kalli me gidanta tana mirmishi “kai Bilal da khausar masoyan asali ana can ana mirje k’auna”
lakace mata hanci yai yace”ke kuma y’ar sa idon Aunty ko”
“hhhhmmmmm” kawai tace suka shiga wata hiran.

yau kam dai da gaske Bilal sayya maye gurbin ranakun da yai missing don haka kusan kwana sukai yana timirmisarta ko ince suna  turmisa juna,
  da asuba suka tashi ya  jasu sallah bayan sun idar ya k'ara rungumeta suka hau gadon idonta cike da bacci  ya shafi gefan fuskanta yana mirmishi yace" my blood nida nake son in k'ara ko sau d'aya ne kike rufe ido zaki koma bacci"

d’an turo baki tai cikin miryan shagwab’a tace ” my wlh dik ka zama wani iri yanzu baka gajiya ko d’oya baka sassauta min”

k’asa yai da miryanshi yai sosai “To Baby nah ai kece kin k’ara dad’i kuma yanzu kin koyo ragunta daga nayi kad’an sai kice abarshi haka”
idonta a lumshe tace “hhhmmmm wai broth ka manta ina d’auke da Baby ne kuma fa ba’asan atakura mai “
shafo cikin yai yace “wayyo my unborn kayi hak’uri na takura ma ko wlh mamin taka ce akwai dad’i sai mutum yai tayi ba gajiy. . .
da sauri ra rufe bakinsa da hannunta ” kai don Allah wai bakajin kunya kaita irin fad’an haka”
dariya yai yace “kunyar me tsakanina da mata ta meye bamuyi ba meye bamu gani . . . . .
“wayyo ni dai banjin me kace”
dariya yake sosai yana shafa kanta itakam bata k’ara magana ba ahaka bacci ya d’auketa ya zubawa fuskanta ido yana jin wani sanyin dad’i aransa.

sai k’arfe goma suka tashi sukai wanka sukaci abincin da aka kawo musu sannan suka fito yaje reception ya basu key d’in d’akin sukai gidan Aunty madeena.

Lokacin da sukaje gidan sai ita kad’ai ni’ima na skul me gidan na office, cikin jin nauyi Baby ta shiga tana gaidata dariya kawai rai tace ” amarya agidan Bilal ansha k’auna ko”
“kai Aunty ba wani k’auna bacci kawai mukayi”
“hhhmmm sannunku da bacci yana ina shi”
“yana gate waya yake na shigo na bashshi,
hira suke d’an tab’awa ya shigo tare da sallama ya zauna suka gaisa da Aunty ya mik’e yana fad’in “bari inje gidan Baffa mu gaisa”
“ok saika dawo”
yana fita Baby ta shige d’aki ta kwanta don dik a gajiye take jinta.

A gidan Baffa   kuwa hiransu suketa sha da Bilal Baffa yai gyaran murya yace "Bilalu baka ganin ko zaku wuce da ita khausar d'in tunda manufarmu na ta sadu da dangine da abokan arzik'i kuma tai hakan kaga ku  wuce tare nan gaba in an k'ara samun wani hutunma saiku zo koba haka ba"

kansa a k’asa yace “a ‘a Baffa ai inaga abarta ta k’arasa kwanakinta tunda nima yau d’innan zan bi jirgin k’arfe sjida na yamma in wuce”
“To shike nan Allah yai muku albarka Bilalu “
“Amin amin Baffa”.

sai k’arfe biyu yabar gidan Baffa bayan yaci kasu da alkairai ya dawo gidan Aunty madeena don sallama da habibatinsa.
Aunty madeena tace ” Sai yanzu Bilal “
bayan ya zauna ya amsa da “eh wlh Aunty muna can munata hira ne da Baffa yanzu ma zan muku sallama ne in wuce”

Bayan sunyi sallama da Auntyn Baby ta rakoshi gate sukai sallama cike da soyayya ya hau napep zuwa Airport.

Bayan tafiyar Bilal da  kwana biyar Baby ma ta shirya tayo gida cike da kewar danginta da garinsu sun had'ota da tsaraba me tarin yawa irin tasu ta fulan,i tabi jirgin safe don haka sha biyu a kano tai mata inda ta tarda Bilal yazo d'aukanta ya sa mata kayanta cikin motan sukai gida,

  Bayan tai wanka tai sallar azahar ya kawo mata take away d'in dayai mata sunaci tana mai hira shi kam sai mirmishi yake don yau jinsa yake rass zuciyansa ta dawo don tunda ta rafi gidan bai mai dad'in zama sam kamar maraya ya zama,
bacci take sonyi dayaga alama tajata jikinsa yana shafa kanta yace" Kiyi bacci naga idonki yana k'asa k'asa".

 Da dare bayan sunyi  sallan magriba ya kaita gida ta gaida su Dad sai wajan k'arfe goma suka dawo gida, 

suna dawowa wanka sukai suka kwanta.

haka rayuwan su taci gaba da tafiya cikin Baby yana girma zuwa yanzu kowa yasan dashi.

Bayan wasu watanni islam ta haifo d’anta santalele tubarkalla su Baby ansha bidirin suna inda yaro yaci suna Abubakar sadeeq.

bayan sati d’aya da sunan sadeeq su Baby suka
gama skul cike da tarin nasarori sunyi murna sunyi farin ciki ansha hidimomi aranar Bilal ya siyawa Baby sabuwar mota k’irar yau ya gwangwajeta.

   Gama skul d'insu yazo musu a dai dai don cikin Aisha da Baby ya tsufa sosai haihuwa yau ko gobe,
Bilal shiri yake sosai na haihuwan Baby  daga k'asashen waje yasa akai mai odan kayan  jinjiri kama daga nasawa na wanka da dai dik abinda ake buk'ata na taran new born baby har katan fitan suna da Baby zata sa saisa ya had'a akwati uku cike da tsadaddun kaya fatan dai Allah ya sauketa lafiya.

Yau litinin Baby na zaune k’asan kujera kan cafet ta mimmik’e k’afan da suka kumbura cikinnan yayo k’asa k’asa alaman haihuwa ta kusa, Bilal ya fito daga kitchen ri’ke da cup ya zubo mata fresh milk yazo ya zauna ya mik’a mata ta amsa tana sha yana matsa mata k’afa, k’ur take kallonsa tana jinjina hidimansa gareta tunda cikinta ya fara tsufa ya d’auke mata komai na d’awainiya dashi maimakon haka ma shike mata komai har wanka ,yana d’ago kansa suka had’a ido ya d’aga mata gira yana mirmishi yace’ ya kallo haka”
girgiza kai tai tana fad’in “My broth Allah ya saukeni lafiya in koma faranta rmaka yanzu kwata kwata ban samun ladan aure”
“waya fad’a miki haka bikisan wannan rainan cikinma acikin ladan aure yake ba don haka kisa aranki jihadi kike”
kwantar da kanta tai jikin kujera tana godewa Allah daya bata miji me sonta da tattalinta”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Leave a Reply

Back to top button