BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

cikin daran ranar nak'uda ta kamata sukai asibiti ba'afi awa biyu ba ta haifo d'anta kyakykyawan gaske nan take Bilal ya fad'i yana sujjada ga ubangijinsa,
ana sallar asuba ya shiga kiran waya yana shaidawa Dad ai kuwa ba'afi minti ashirinba sai gasu shida mami da momy nan sukaita murna Dad ya shiga shaidawa mutane shima Bilal ya sanar da Nazeef da Doct,Al'amin yace dik su fad'awa matansu.
Baba matar malam ce zata zauna da ita don haka aranar Dad ya aika aka d'aukota ,gida sai shiga ake ana fita, tun aranar Bilal yaiwa yaron hud'uba da sunan marigayi Nabeel kowa yaji sunan yaron sayyayi murna dayiwa Nabeel addu'a,
kwanan Baby Hud’u da haihuwa Aisha ta haifo ya’ta mace me kama da ita nan murna ta k’arar musu hidima ta kuma kankama,
Ran sunan Nabeel k’arami ansha hidima anyi b’arin naira Dad ma saida yai mai akwati hud’u yaiwa Baby biyi mami da momy ma sunyi musu kaya sosai , haka ma daga gidansu Yaya Nabeel ummynsa ta kawo kayan barka ga Nabeel k’arami kai abin dai sai san barka ahaka aka watse kowa murna.
yar Aisha taci sunan kakarta maryam suna kiranta Hanan.
Bayan shekara Biyar
can na hango Hajiya doctor khausar rik’e da hannun wata y’ar yarinya y’ar shekar uku ga wani wanda bazai wuce shekara d’aya ba a kafad’ar Abbansa Bilal fad’i yake, ” Jenior kaifa muke jira”
da gudu ya fito yana fadin ” sorry
Abbah gani na”
bud’e baya yai ya shige inda Nanah ke zaune sai Mamansu dake gaba azaune agaba da Haidar kan cinyarta sukaja motan zuwa shopping,
mirmishi nai araina nace oh su Baby khausar har anyi y’ay’a uku lalle rayuwa ta mik’a.
wai wayawa nai gidan Aisha na ganta da y’ay’anta uku itama dik mata,
islam kuwa dake konika take yayanta hud'u naga alamar ma da yaron ciki????.
????????????????????????????????
Tammat bi hamdu
????????????????????????????????
ina sanar da fans sabon littafina na nan tafe me taken (Y’AN ARABIC)
ina sonku ina k’aunarku masoya na
mak’iya ma ina gaidasu.
Taku ce
Layuza kabir Adam????♀????♀????♀