BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Rungumota yai .yasauko da ita daga sama yana fadin
iya Abu iya Abu .da gudu ta fito tana mitstsika. Ido .na masu bacci .
Subhanallahi Alh meya sameta .
Nima haka na taddata .zamuje asibiti ki kula da Baby kuma kishiga dakinta ki gyara inda ta bata.
To hadiza sannu Allah yasauwake
Ciwo farat daya lfy fa mukai sallama taje ta kwanta .ikon Allah Kenan.
Likitoci manya suka tsaya akanta .akasa mata ruwa da alluran. Tsaida amai da kuma gudawar. .
Ga ruwa yana tafiya amma fa tana kasayardashi
Gudawa take .kamar ruwa . karama aman ya tsagaita .kadan
Ta galabaita matuka don ko idonta bata iya budewa .sai numfashi .sama sama
Hankalin Alh fa yakai matuka wajan tashi tun yana salati .har yasoma hawaye .
Awa uku ana Abu daya . zuwa sallar asiba kuwa .ranta yafita .
Likitan dake kanta ne yai salati .tare da jan zani yarufe mata fuska .
Wannan ne yafargar da Alh. Ai kuwa ya kaiwa doctor n .danka yana fadin me kakeso kacemin wai .kana nufin hadiza ta rasu
Hannunsa doctor din ya riko . yashiga. Bibbiga kafadarsa yana be a man Alh .kayi hakuri Allah daya karbeta ya fika sonta .
Wani irin kuka yasa .yana fadin wayyo Allah na .hadiza hasken rayuwata kin tafi kinbarmu .nida baby cikin maraici .wayyo mata ta .Allah ya hadaki da manzon tsira .
Tsawon lokaci yana kuka sannan yai ajiyar zuciya .yace doctor Ku .bani gawar nan yanzu intafi da ita.
Nan da nan suka gama cike cikensu sukasata Ambulance. Shima yashiga . aka kulle motansa aka ajiyeta ana Abu .don bazai iya tuki awanna halinba.
Ganin ambulance tashigo gidan yasa .dik maaikatan gidan da suka fito daga masallaci .karasowa jikin motan don sunsan Alh.ya tafi da me dakinsa asibiti.
Toba sai anmusu bayani ba daga ganin .yanda Alh ke rizgar kuka .
Suka hau salati .nan da nan aka fito da gawar akan makarar. Asibi kama kama sukai zuwa bangaranta .
Bubbuga kofar falon da ake ne yasa Iya Abu saurin zuwa ta bude .ganin maza dauke da makara .yasata sakin salati hade da wani gigitaccen kuka .haba hadiza meyasa zaki mana haka .daga ciwon kwana daya saiki mutu........
Don Allah ki tashi kinga fa Baby
Karki tafi kibarta cikin maraici mana.
????????????????????
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
1⃣8⃣
Malam haruna ne .yace bari fadin haka Abu .wannan bashi yadace musulmi yafada ba .inyai rashi maza yi ta fadin Innalillahi wa inna ilaihi rajiun
Allah shi yabukaci abarsa a wannan lokacin kuma .dole miyi hakuri.
Nan dai aka shiga fadawa mutane sarkin gidane ya dauki wayan Alh.yarinka kiran .mutanansa yana fada musu .
Ita kanta hjy ta razana da jin mutuwar hadiza farat daya .nan dik jikinta yai sanyi lalle Allah abin tsoro rayuwa abin tsoro.
To haka dai aka shiryata aka kaita gidanta na gaskiya .
Kullu nafsin za’ ikatul maut(dikkan me rai mamaci ne )
Mutuwa dai kam mutum uku akayiwa mijinta .yarta.da kuma iya Abu data dauka amatsayin uwa.
Su hjy.Halima ma da me gidanta dik sunzo daga Lagos
Haka akai zaman makoki tsawon kwana bakwai .kowa ya koma .inda ya fito
Kuma aranar ne Hjy Amina ta shigo part din na marigaiyiya . a falow ta sami Alhajin zaune ya rungume baby khausar yanata kuka .ga iya Abu ma tana kasan kujera tana .rusa nata.kukan.
Waje tasamu ta zauna .tsawon 10mint sannan tace Alh.dama wata shawara ce nazo da .ita .ina ganin zaman Baby da iya Abu agunnan su kadai bazai yuyuba .sabida matukar suna zaune anan to zuciyar su bazata taba yin sanyiba kullum zasu rika tunaninta.
Yanzu su koma bangaranmu ga dakuna nan akasa saisu .zauna a daya .tunda kaga khausar bazata yarda ta zauna ba iya Abu ba .
Ko ko ya kace?
Jijjiga kai yai yana fadin hakan zaayi Amina nima insun bar nan sai hankalina yafi kwanciya.
Don haka iya ki had a muku dik wani Abu da kuke bukata .zuwa gobe .sai akara shirya muku dakin ko_?
Yafada yana shafa kan baby dataketa kallonsa . itadai baby tunaninta bai kai yagane mata tana cikin rashiba saidai . dik Alhini ya damu jikinta .kulum da xaxkabi take kwana tayi sanyi qlau .ko abinci bata son ci sai an takura mata
Da wannan shawarar.ya mike rike da hannun baby yai stairs da ita .don tunda akai rasuwar adakin hadiza yake kwana rungume da baby .
Da safe yakira masu aiki suka ziba sabbin Kaya da gadon yara acikin dakin aka shirya musu .komai itada iya Abu .suka kwaso sutturunsu .da sauran abinda suke bukata. Aranar sika koma bangaran hjy Amina. Alh. Ya kulle part din hadiza.
Tofa tunda ga wannan lokacin zaman baby yadawo nan.kullum inba makaranta suna tare da yayanta Bilal a fallow wannan yakara musu shakuwa.
.yanzu Alh.ya rage tafiye tafiye kullum yana tare da baby khausar .yana kokarin debemata .kewan mom dinta .
Dik wani motsinsa .yace baby dik tausayinta yakeji.
.wata rana da yamma yana zaune a a harabar gidan Rungume da baby .yazuba uban tagumi. Yana tunani. Hjy. Maryam tashigo. Gidan .bayan tayi farking din motanta
Harta karaso besani ba tana ta gaidashi amma ina .baima sani ba.
Jijjiga kai tayi .ta wuce .ciki.
Bayan sungaisa da aminiyarta .ta gayara zama tana fadin hjy Amina wai shikenan haka zakiyita zama da mutumin nan ya zamemiki kamar mutum mutumi. Kefa da kanki kikace yanzu ko hiran kirki baya yi dake .tunda akai rasuwarnan .bashi da lokacin kowa saina wannan aljanar yar.
To wlh bari kiji infada miki wani labari najiyo cewa jamaa sunata . yimai tallan yayansu ya aura .
Kuma kinsan yanzu .yana karbar ayinsu. Ya zo yakara aure . dik wadda ta shigo .itama haihuwa zatayi.
Kinga Kenan alamu sun nuna kece bakya haihuwa an tara kudi dake .
Wasu zasu Tara magada .ke kina zaune .ga wannan yaron Bilal haka zaku tashi ba komai.
Don haka kawata ina jan hankalinki akan .lokaci yayi da yazama dole .kicire akidar kin bin bokaye
Asamu ajanye hankalinsa akan kowace .mace .yaji Sam baya shaawar kara yin wani auran
Sannan akau da hankalinsa akan wannan yar tasa .yazama ke . kadaice agabansa
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
Allah ina rokonka da sunayanka tsarka da ikonka madaukaki
Da ka jikan ginshikai biyu a rayuwa ta.
Mlm Dahiru Ibrahim mar mara
Amina Yusuf *(Aunty Amina)
Allah ka sasu cikin Aljanna madaukakiya ????????????????
1⃣9⃣
- Jibeki don Allah .kina zaune namiji zai hargitsa mini kwakwalwa Dik cikinmu ba Wanda mijinta ya kama kafar mijinki a rziki.nesa ba kusa ba .tsakaninsu. Amma kuma dik munfiki kwanciyar hankali Abin nufi bamu da wata damuwa tsakaninmu da mazajanmu .sai yanda mukace suyi zasuyi .(wa’iya zu billah)
Don haka kamar yanda na fada miki. Lokaci yayi da zaki tashi ki nemi kanmijinki
Inba hakaba wlh kina gani zaicemiki zai kara kaure. Kishiyoyu suyita zuwa suna cika miki gida da yaya
Shi Kenan ke kintashi a banza a iska.
Don haka ki saki jiki ki kawo kudi . kinadaga gida aiki zai ta zuwarmiki .zakiga canji .wlh sai abinda kikace. Shi zaiyi. Ke ko yanda zai tafiyar da dukiyarsa .saiya tanbayeki yanda zaiyi.
Tofa ziga ta gama shigar hjy Amina .jiki na mazari tashiga bedroom dinta ta debo dami damin kudi Wanda batasan adadinsuba ta baiwa hjy maryam tana fadin kawata ayi dik abinda ya dace
Aha itakuwa hjy maryam aiki yasamu bata bata lokaciba ta mike sai hanyar gidan bokansu cike da murnarta .na tayi nasarar dora kawarta a hanyar malamai
(Allah ka rabamu da mugun aboki.????)
Sunkai tsawon wata biyu suna tafka asiri ba dare ba rana kudi .hjy Amina take durawa boka kafin asirinnan yafara cin jikin Alh don shima ba azaune yakeba yana tsare jikinsa
To amma dake su tsafinnasu harda kauce hanya .kuma sunyi amfani da kasurguman Aljanu sai gashi sun fara cin riba .
Kuma cin ribarsu ya kara samin karfi ne .ta sanadiyar sanyi da yayi .da adduoinsa na azkar . wannan yasa suka kara samun dama akansa.
( _Sabida_haka yan uwa mu kula da addua.)
Sai gashi yanzu Alh.sai abinda hjy tace .yakeyi ko fita zaiyi saiya fada mata inda zashi .inta yarda yaje intace a a kuwa dik himmanynci fitar ya fasa ta Kenan.
Zuwa yanzu ko saiya kwana biyu bai nemi Inda baby take ba.
Dik wata nutsuwarsa an kau da ita
Yazama susu su.
Su jamaa dik tunaninsu har haryanzu zafin mutuwa ce bata gama sakinsaba