BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL
BABY KHAUSAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka aka dau watanni .duniya ta samu ga hjy Amina.
Zuwa lokacinkuwa baby tazama abin tausayi ta rasa kulawar uwa da uba
Sai iya Abu mace me rike amana ita take mata komai .dikda yanzu ba wani abinci arziki ake basu agidnba .don haka dik sun hadu sun rame .saidai iya taje gun masu aiki insun dafa .abincinsu si Dan kara musu.
Shidai dama Alh.bashida obokin shawara in matsalarshi ma ta ciyoshi Mlm Khalil yake zuwarwa da ita . to Mlm dinma .anshiga tsakaninsu .kwata kwata baya son zuwa gunsa
????????????????????
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
MY AFREEN ALLAH YA BAKI LFY .YA KIYAYE GABA.????
2⃣0⃣
Bilal abin da ke faruwa agidansu yana damunsa ganin yanda kanwarsa ta zama kamar wata yar masu aiki agidan ko shi yanzu in yana tare da ita momyn nasa tsawa take sakarmishi .
indai yasamu damar sakewa da ita to a skl ne .amma agida tsakaninshi da ita sai ido . wani lokacin haka zai shiga dakinsa yaita kuka dik rayuwar gidan tamai zafi shima dik ya rame
To ganin irin damuwar da Bilal ke ciki yasa su hjy shawarar. Shima akai sunan shi gaban boka akan shima acire mai kaunar baby arnsa asanya mai tsanarta .
To haka kuwa akai lokaci guda Bilal yaji Sam baya son yiwa khausar magana .ko kallon ta bai kaunaryi .
Inma ta isheshi da magana saiya daka mata tsawa .tun bata damuwa anjima haka zata koma yakuma hantararta .
Daga karshe kuwa saita daina .zuwa kusa dashi.saidai taita kuka tana kallonshi .
Ana tsaka da haka .labari yazowa iya Abu daga kauyansu .babban danta .ba lafiya don haka dole tafiya ta kamata zuwa garinnasu.
Bata soba haka ta tafi tabar baby tanata rizgar kuka .shikenan yanzu zata kara shiga kunci .
Da rarrashi ta tafi tana fadin ina zuwa inna duba jijinnasa zan dawo baby .ko kwana goma bazanba insha Allah.
Tun tafiyar iya Abu komai yakara tsinkewa ya lalace .rayuwa ta kara kunci ga khausar . ko abincin arziki bata samu .arana sau biyu take ci. Abata in zata tafi school to sai kuma da magriba shikenan
Tafi tafi iya ta dawo shiru har tsawon wata guda .sai daga baya mummunan labari ya kara zuwar musu ai ahanyar dawowarta .ta baro garinsu kadan sukai hadari .ko shurawa bataiba .
Nanfa khausar ta kara shiga wata rayuwa .
Har amakaranta kowa ya fahimci yanzu Bilal baya shiri da kanwar tasa .don ko break aka fito .saidai taita zama a aji tana kuka to ko abinci yanzu baa .bata tatafi dashi .balle yan Kayan kwadayi da ake zubawa yara a jaka sutafi dashi kowa haka zai fice abarta ita kadai
Wata Aisha M shareef ce a ajinsu wadda zasuyi saanni. Ce bata iya cin abincinta iya kadai . haka zata sata agaba taita .cewa baby khausar muci abincina tare .to dake tana tare da yunwa haka zata sa hannu suci kuma su shanye Kayan kwalamar tare.
Don haka bata samin wata walwala a duniya inba taje mkrnta ba.
Labari Aisha m shareef ta bawa mom dinta kawarta mamanta ta rasu bata zuwa da abinci don haka ake kara mata abinci Wanda zai rinka isarsu ci su biyu.
A wannan matsin rayuwar lokaci yaita tafiya .wata ranar asabar baby yunwa ta isheta hjy tana parlour a up stairs
Ta lallaba ta shiga kitchen. Abincin dake cikin food flask ta bude tasa spoon ta fara ci .aikuwa dika lomarta uku hjy ta shigo kitchen din salati sosai tasa kamar wadda taga miciji . au khausar tsiyar taki har ta kai ki shiga kitchen kinamin satar abinci ni zakiyiwa sata .to wlh yau sai na lahira yafiki jin dadi .
Wata danka datakai mata tazuba mata mari ta gwara kanta da bango da kafa ta wullota waje aikuwa ta bugu da jikin kujerar dining ai kuwa nan kanta ya gashe jini kamar me haka yaita zuba ya wanke mata fuska amma sabida rashin imani haka taita jibgarta kamar ta samu wata katuwar budurwa.
Tun tana kuka da hawaye harta koma ajiyar zuciya ahaka numfashinta ya dauke ta suma .
Sarai tasan suuma tai amma saita koma kan kujera tazauna ta kunna TV abinta .tsawon 30mint taga Yarinya. Bata motsaba .sai kuma taji fargaba don haka ta kira wayar dakin masu aiki tace Barira tazo .
Tana shigowa tace jeki duba yarinyar can kiga.
Barira ta tsorata da ganin yanda jini ya wanke fuskarta kuma ya daskare
Agigice taje ta debo ruwa ta watsamata afuska tsawon minti biyu ta farfado .kaita bakin fanfo tayi ta wanke mata fuska .
Sannan sika dawo parlour. Tace hajiya .ko zaa kaita asibiti ai mata treatment.
Ke ba wani asibiti da zaa kaita sami kyalle ki daura mata agun jinin ya tsaya shikenan.
Don ubanta ai ita tajawa kanta barauniyar banza da wofi.
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: ????????????????????
????????????????????????
????????????????????????
BABY KHAUSAR
NA
LAYUZA KABIR ADAM
2⃣1⃣
Sabida rashin gata haka ciwonnan ya gama yayinsa ya warke ba wata kulawa . har wani wari wari yakeyi to ciwo a cikin gashi .shi kanshi gashin yafi wata bakwai ba kitso ba wankewa dik ya daddan kare .ba kyan kalla.
Wayyo Allah ka rabamu da maraici a shekarun kuruciya.
To Yarinya fa ta zama ba kyan kalla .dik wannan farin da kyan dik babu .bazaka kalleta .kaga abin ban shaawa tare da itaba .ba wanka wankima saidai intaga me wankin yazo yanayi ta dibi kayanta .takai mishi .ya wanke mata .
Ga Dan karan duka da takesha gun hjy .dik kankantar Abu in tayi a duka yake .wani lokacin ko hada ido sukai .saita bugeta .
Haka Bilal wata rana yana cin abinci .
Tazo gefan kujerar da yake . ta rakube tana jiran yagama ci ta karashe sauran .
Aikuwa yana cikin ci yaji motsi a gefansa .juyowar da zaiyi yaganta .
Wani wawan mari yasakar mata
Yana fadin ni zaki zo kisa agaba ina cin abinci .don uwarki da wannan war in kan naki da warin jikinki .
Banza bakinki .kamar Masai .matsa anan ko na karyaki na huta shegiya kazama .
Jiki na bari tashige dakinta .tana kuka kamar ranta zai fita .
Yarinya karama .amma matsalar manya akanta .
Mlm Khalil .ganin tsawon lokaci Alh bai nemeshiba. Yai tunanin aiki ne yamai yawa don yasan inda matsala ai da gudu yake zuwanmishi
Don haka shima ya kaleshi. Ana haka mahaifinshi ya kwanta ciwo acan garinsu don haka ba shiri suka hada kayansu sukai garinsu can barno .
Ahaka rayuwa taci gaba da tafiya .yayinda baby khausar ta kasance kullum cikin rashin gata da maraici.ga kuntatawar matar uba .data Dan uwa .ba inda takejin dadi sai a school. Gun kawarta Aisha.
Tsautsayi yasa wata rana .hjy Amina tai bakuwa .tazo da yarta karama .ba daki baby itama ta rama .
Yarinyar tasa kuka . me akai miki tace baby ce ta daketa .
Hhhhmmmn ummmmm .wata shawara ce tazo zuciyar hjy .aikuwa nan da nan .ta kira barira .tace maza ki doramin ruwan zafi .kisa barkono da citta suji sosai
Aikuwa baa jimaba .ta dawo tace .ruwan ya tafasa .
Jeki bangaranku ki kawomin buta
Ruwan tajuye a buta ta ajiye
Bayan bakuwar ta tafi .ana kiran sallar magriba zuwa lokacin ruwan ya salance .
Ta kwadawa baby kira jiki na rawa tazo
Yawwa maza dauki wannan butar kije kiyi tsarki kiyi alwala ankira sallah
Daukan butqn tayi tashiga toilet din dakinta baafi minti biyu ta kwala ihu .wayyo Allah na zafi yaji momy kizo ki taimakeni .wlh zafi yaji
Da dariyarta tashiga toilet din .ke dalla yiwa mutane shiru ubanme akaimiki.zaki cika mana gida da ihu.
Momy ki taimake ni yajine acikin wannan ruwan danai tsarki. Wlh yaji nakeji .wayyo momy zan mutu
Yawwa ai nafiso ki mutum in huta sabida ganinki bakantamin rai yake
Dik me imani ya dubi yarinyarnan yasan tanajin azaba a lokacin kuma saiya tausaya mata .
Amma dake zuciyar ta kekashe ko agefan zaninta bata damuba haka .taita dariya .ta fice ta Barta a toilet din
Dabara Allah ya sako mata da sauri ta kunna fanfon ruwan sanyi ta tara .taita tsarki dashi .
Ba lefi ta danji dama dama .haka .ta fito . tanata matse kafa .
Gadonta ta hau taci gaba da kuka ahaka barci ya dauketa .