BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

[7/23, 09:45] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????
????️ BAHAGON LAYI ????️
(GIDAN KITSO)
TARE DA ALK’ALAMIN ✍️
HASSANA D’AN LARABAWA
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K’AI,TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU K’ARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD (S A W)DA ALAYENSA DA SAHABBANSA
MASOYA GANI NA DAWO DA WANI SABON LITTAFINA,DUK DA CEWAR GAJERE NE BA DOGO BA,AMMA INA FATAN SAK’ON YA KAI INDA NAKE SO HAR MA YA WUCE,KAR KU MANTA INA BUK’ATAR COMMENTS D’IN KU DOMIM YANA K’ARAMIN K’WARIN GWIWA
K’aramin Tsakar gidan mata ne a zaune mabambanta,surutai da shewar su kawai ke tashi kamar su fasa gidan Dan hargowa,ga gyad’a marau marau da tub’us tub’us baje a gabansu sai b’arewa suke yi suna jefawa a bakunansu,Zagaye suke da Harira Me kitso wadda take kitse kan wata Yarinya da ba tafi shekara takwas zuwa tara ba.
Hirarsu ta katse a lokacin da suka ji yarinyar ta fasa kuka saboda azababben rank’washin da Harira ta zuba mata a tsakiyar kanta,duk suka maida hankalinsu kan Harirar da take kumfar baki tana yi wa yarinyar masifa tare da matse kanta a tsakanin cinyoyinta.
“Ke Dan Ubanki zaki tsaya na k’arasa miki kitson nan ko sai na k’ara zuba miki rank’washin da zaki ga k’wak’walwar kanki tana yarari?tunda kika zo nace miki ki bari nayi miki zane amma kika ce ke kwando(Doka) kike so,Dan haka tilas kisa kanki tsakanin cinyoyina in kina son kitsonki yayi kyau,ban da ni ma waye zai tab’a wannan kan da sunan kitso,aikin banza kai duk gunji da almajiran k’eya,billahillazi kika sake d’agowa ban gama ba idan na zuba miki dundu fes zan b’urma miki baya”
Ta k’ara matse kan yarinyar sosai tsakanin cinyoyinta tana ta bala’i da masifa,yayin da yarinyar ke kuka hawaye shab’e shab’e Dan azabar da take ji,ba kuma komai ke sata mutsu mutsu ba sai azabar wari da d’oyin da ya addabeta,da ta saka kanta kan cinyar harira sai wani masifaffen wari ya daki hancinta,ta rasa warin menene haka yake tasowa,ita dai ba zata ce warin tusa bane tunda ba taji k’ararta ba,haka nan ba zata ce warin kashi bane tunda Harirar babbace balle tace kashi tayi a zaune,gabad’aya warin ya dami hancinta har cikinta ya fara ciwo da kumburi saboda warin.
Habiba ce ta hure gyad'ar da ta b'are a hannunta ta cilla bakinta ta taune,sannan ta kalli Harira tace.
“Gaskiya Harira ke azzaluma ce,haka kawai sai lodar yarinyar mutane kike yi Dan tazo kitso wajenki?kin matse mata fuska ta ya ya ba zata so d’agowa Dan ta shak’i iska ba?wallahi ina ganin k’ok’arin mutanen layin nan da unguwar nan da suke turo y’ay’ansu da sunan ki musu kitso,basu san azabar da kike ganawa y’ay’an bane,idan nice kika yiwa y’ay’ana haka ai kotu ce zata rabani dake,wannan rank’washin da kike mata idan tsautsayi ya gifta kika lotsa mata mad’iga fa?
Zahra’u ta kwashe da dariya tana tattara b’awon gabanta tace.
” Kin san kuwa Habiba har na hango idanuwan Harira gaban kuliya manta sabo,ni da gwagwalada.
Shafa’atu ta karb’e zancen da cewa.
“Ni fa banga laifin Harira ba,ai tana ma k’ok’ari wallahi wajen kama kan yaran Unguwar nan da layin nan,yawancinsu kan a diddige yake,ga tsinannen amosani da kwarkwarta amma haka take daurewa ta kitse musu kai,duk fa yawanci yaran ita ce silar fito musu da gashin kansu,duk diddigewar kai sai ta san yadda ta fito musu da shi,ko kun manta kirarinta ne?wato Hariratu mayyar gunji”
Duk suka kwashe da dariya suna kallon Harira da ta kammalawa yarinyar kitso tana soke kibiyar a gefen kunnenta,ta samu dai dai k’eyar yarinyar da ta kame tsaf har wani ja tayi Dan kamuwa,ta saita hannunta ta d’ala mata wani shegen d’ad’o me shiga kwanya,a zabure yarinyar ta d’ago kanta tana zillo saboda yadda dukan ya shigeta sosai,ta kai hannunta tana murza k’eyar hawaye na silalowa a idanuwanta,Harira ta kwashe da dariya har da rik’e ciki tana kallon yarinyar,ta dubi matan da ke zaune a tsakar gidan tace.
“Dan Allah ku kalle min goshin Samiha yayi wani rantalele kamar goshin jirgi,wai Dan ma kitson ya rufe goshin kenan,kai gaskiya yarinyar nan Allah yayi miki baiwar gingimemen goshi kina fama,rantaka k’wale kenan”
Ta kuma fashewa da dariya matan na taya ta,suna kallon goshin Samiha da yake ta k’yallin man kitso yana shining, Samiha ta share hawayenta ta mik’e tana d’aura d’ankwalinta Dan tafiya gida,ta d’auki man kitsonta tana ficewa a gidan da sauri Dan ciwon da cikinta ke mata ya isheta,suka bita da kallo suna dariya yayin da Habiba ke cewa.
“Wannan yarinyar idan har goshinki na arzik’i ne mijin da zaki aura ya more,domin zai dangwali arzik’in goshinki tabbas”
“In kuma goshin tsiya ne ya shiga uku ba” cewar Zahra’u tana matsawa gaban Harira,sannan ta cigaba da magana tana kallon Harirar tace.
“Yi min shiku Harira,amma gaskiya kar ki matse min kai domin ni ba Yarinya bace,wallahi kika matseni ba zan ji kunyar gasa miki cizo a cinya ba,ba dan k’asimu yace yana son ganin shiku a kaina ba wallahi da Zane kawai zaki yi min na huta”
Harira ta kyalkyale da dariya tace.
“Au wai shi nan k’asimu har ya san ya zab’i kitson da za ki yi Dan ya gani yaji dad’i?ina ganinsa sumummuka sau Ashe shi ma k’wallon shege ne?wallahi Zahra’u idan na fita na had’u da shi a hanya sai na ganshi sululuf yana tafiya yana mik’a wuya mabayyani,na zaci ko Hannu kika sa masa a baki ba zai gatsa ba”
Zahra'u ta dallawa Harira harara sannan ta murgud'a baki tace.
“Amma Harira baki da mutunci wallahi,mijin nawa ne k’wallon shege?ke yanzu idan na zagi Sunusi za ki ji dad’i?kece kike kallon mijina sahorami amma wallahi lamba d’aya ne,Wannan maganin fa da kuka k’i siya a wajen dillaliya da na siya na gwada kinga yadda K’asimu ya rud’e?abin da bai tab’ayi ba jiya sai da yayi min”
Dukansu suka zaburo wajen had’a baki suna tambayarta.
“Me yayi miki?
Ta wani juya idanu tana fari tace.
” Wallahi har kid’an k’warya yayi min”
Suka kalli juna da mamaki,Habiba tayi hanzarin cewa.
“Kid’an k’warya kuma?da me yayi kid’an k’waryar Zahra’u?
Ta kwashe da dariya tana turo d’ankwalinta gaban goshi,sannan ta sake yin fari da idanu tace.
” Da d’uwawuna mana,ai kamar kalangu ko k’warya haka ya dinga buga kid’a da hannuwansa a gun yana raira min wak’a saboda tsabar zaucewa”
Me kuwa za su yi in ba dariya ba?Harira har da fad’owa daga kujerar kitson ta Dan dariya,wai kid’an k’warya da d’uwawu,kai gaskiya ya kamata su ma su siyi maganin ko sa zauta mazajensu kamar yadda Zahra’u ta zauta K’asimu.
Habiba garin dariya har da k’warewa,tari ya sark’e ta amma ta kasa tsaida dariyarta,sai Shafa’atu ce ta dai dai ci tsakiyar bayan Habiban ta d’urma mata shegen dundu tana fad’in.
“Luf!Luf!Luf!”
Habiba tayi sufa ta mik’e ta wawuro ruwa a randar Harira ta kafa kai tana kwankwad’a,sai da ta gama sha sannan tarin ya tsagaita har da hawaye a idanuwanta na dariyar mugunta,sannan ta fuskanci Shafa’atu ta galla mata harara tace.
“In bakiyi mugunta ba ta ya ya za a san ke ba aminiyar Harira ba ce? Ni jaririya ce da zaki d’uma min dundu kina wani Luf Luf ?mugunta kawai ke damunki Shafa,kuma Allah bashi kika d’auka sai na rama”
Shafa’atu tayi dariya tace.
“Sai dai ki rame,daga taimako sai ki hau sababi?da na sani na k’yaleki da k’warewarki,wallahi sai dai ki jiki a k’abari Dan zaki iya zarcewa daga wannan k’warewar”
Habiba ta zaro idanuwa tana rik’e bakin ta,za tayi magana kenan Zahra’u ta rigata.
“Don Allah ni dai Harira ki min kitson,Dan gaskiya na fara jin yunwa,gashi ko cefanen ba muje mun yi ba”