BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Har suka zo Saratu bata dawo ba,Malam yace su tsaya k’ofar gida suga ta inda zata b’ullo.

Saratu kam Sai wajen taran dare sannan ta Ankara, da sauri ta mik’e ta yiwa mutanen sallama ta fito Dan Shiga gidanta.

Gabanta ya buga dammm!ganin Salisu da Mahaifinta a k’ofar gidanta a tsaye sun zubo mata idanu……!

GODIYA GAREKU MASOYANA????????????????????

Comments, share, pls

BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️
08080049548.
[8/5, 09:59] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????

????️ BAHAGON LAYI ????️

         (A RAN GAMA)

TARE DA ALK’ALAMIN✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

MARUBUCIYAR????

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

     *DA KUMA*????

BAHAGON LAYI

BABI NA SHA UKU DA NA SHA HUD’U

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://www.facebook.com/groups/1533639276725

INA YIWA D’AUKACIN AL’UMMAR MUSULMI BARKA DA SALLAH,DAFATAN KOWA YAYI SALLAH LAFIYA????????

   *GA SAK'O DAGA MATAN BAHAGON LAYI,SUNCE NA SANAR MUKU KOWA YA K'ULLO NAMA YA BANI NA KAI MUSU,HARIRA KUMA TANA YIWA WAD'ANDA SUKA JE KITSON SALLAH WAJENTA BANGAJIYA,DAFATAN WARIN DA SUKA SHAK'A BAI KUMBURA MUSU CIKI BA*?????????????

Jikinta ya kama karkarwa k’afarta na rawa,tuni idanuwanta suka ciko da hawaye saboda ta san Mahaifinta ba yayi mata da wasa,kallon da yake mata kawai a yanzu haka ya isa yasa hantar cikinta kad’awa.
Malam Ya maida kallonsa kan Salisu yace.

“Idan akwai mukulli a hannunka bud’e mu shiga”

Salisu cikin sunkuyar da kai ya amsa da “To Malam” Sannan yasa makullinsa ya bud’e gidan.

Malam ya kalleta fuska a d’aure yace.

“Zo ki shige mutuniyar Banza,kina yawo k’afa kamar kwarkwaro”

Jikinta na rawa ta rab’a ta shige tana Hararar Salisu ta k’asan idanuwanta.

Suka bita a baya har zuwa cikin gidan,tana niyyar bud’e d’akin nata Malam ya daka mata tsawa da cewa.

“Dawo nan Dan ba shiga d’akinki zan yi ba,Mara kunya fitsararriya”

Ta dawo tana sosa kai ta tsuguna,yayin da Salisu ke tsugune shima kansa a sunkuye,cikin matuk’ar b’acin rai Malam ya soma yi mata fad’a.

“Ba k’aramin mamaki kike bani ba Saratu,Mamakin bai wuce na watsar da kyakkyawar tarbiyyarki da kika yi ba kika aro mummuna kika yab’awa kanki,Allah shine shaidata na baki tarbiyya ta gari na baki ilimi na addini Wanda zai miki jagora zuwa bautar ubangijinki da bautar aure,amma a yanzu duk kin watsar babu abin da kike yi sai zaluntar mijinki da munana masa,tun yana hak’uri dake har kin kaishi mak’ura yazo ya sanar dani komai,Saratu kin san yawan zunubin da mace ta ke samu idan ta sake ta fita ba tare da izinin mijinta ba kuwa?kin san yawan zunubin da mace take d’auka akan wulak’anta miji da lek’e idan baya nan?Saratu idan baki yi tunanin ta nutsu ba zaki kai kanki wutar jahannama,mace tayi biyayyar aure tabi Allah da manzonsa ma amma Allah yana jarrabarta balle ta k’etare dokokin sa,kiyi duba ga mahaifiyarki ta zame miki izna a rayuwarki,tabi Allah da manzonsa ta tsare hak’k’ok’in aure yadda ya kamata,ta kasance mace mai bin umarnina da yi min biyayya da kaucewa b’acin raina,amma duk da hakan Allah ya d’ora mata lalurar da ko tashi zata yi sai an d’agata,to ke da kike k’etare iyakokin Allah da na aure idan Allah ya tashi jarrabarki kin san wace irin jarrabawa zai miki?Ba yau na fara yi miki nasiha da fad’a akan munanan halayen da kike ba,amma inason in shaida miki wannan ne na k’arshe,Annabi (S A W)ma ya umarci d’iyarsa Fad’ima (R A)tayi wa mijinta sayyidina Ali (R A)Biyayya,duk da kasancewarta mai girma d’iyar masu girma,ba ke ba karankad’a miya tasono dake,Annabi (S A W)yace”Da Allah zai umarci wani yayi wa wani sujjada,to da ya umarci mace ta yiwa mijinta sujjada”Saboda tsananin girman miji a wajen matarsa,Dan haka ki maida hankalinki Saratu,wannan ita ce hanyar aljannarki,domin aljannar taki tana k’ark’ashin k’afar mijinki,wallahi tallahi idan kinga kin shigeta to sai dai idan ya d’aga miki,to ta ya ya zai d’aga miki kina cutar dashi kina zaluntarsa?ita zuciya ai an halicceta ne ga son Wanda yake kyautata mata,haka nan ga k’in Wanda yake munana mata,duk randa kika yi sake ragowar k’imarki ta zube a idanuwan mijinki kin kad’e Saratu,domin ba zaki tsira da komai ba,kuma ko a lahira ni kaina mahaifinki ba ruwana dake,Dan haka ina yi miki nasiha da kiji tsoran Allah,ki sani Allah yana kallon dukkan abin da kike aikatawa,maganata dake ta k’arshe ita ce, Muddin kika sake Salisu ya gaji da halayyarki ya koroki gida ya sake ki to fa tabbas zaki d’and’ana kud’arki,ba zan koreki a gidana ba saboda ni Mahaifinki ne,amma wallahi zaki gwammace zaman kurkuku da zaman da za kiyi a gidana,wannan ce maganata dake ta k’arshe,ya rage ruwanki ki gyara ko ki cigaba da aikata munanan halayenki,(Imma shakiran,wa imma kafura).

Malam yana kammala maganarsa ya dubi Salisu yace.

“Kai kuma ka cigaba da hak’uri,Sannan ka cigaba da nuna kai namiji ne mai cikakken iko a kanta,kai Allah ya bawa kiwonta,kuma ka tabbata kaima Allah zai tambayeka akan kiwon da ya baka,ka lura da wannan,Ni zan wuce,Allah ya sadamu da alkairinsa”

Saratu tuni jikinta yayi sanyi akan nasihar mahaifinta,har k’walla ta ciko idanuwanta,da sauri ta mik’e ganin mahaifin nata ya nufi k’ofar fita, Salisu ya mik’e ya bishi a baya Dan ya rakashi,da k’yar ta fizgo magana a bakinta da sauri tace.

“Baba nagode, a sauka Lafiya a gaida Umma”

“Madalla” Kalmar da malam ya Amsawa Saratu kenan suka fice a gidan suka barta da sanyayyun k’afafuwa ta na muzurai.


Kwana biyu da hakan har Saratu ta fara nutsuwa ta dena wad’ansu Abubuwan,kuma ba laifi tana jin maganar Salisu,sai dai fa tana jinta a takure sosai,ba lek’e ba zuwa gidan k’awaye shan shafta.

        Su ma k'awayen suka ji shirun yayi yawa basa ganinta,gashi sun shirya shiga gidan Amarya domin su gabatar mata da Kansu,tun washegari suka so shiga amma suka d'aga k'afa,su kuma basa son Shiga ba tare da Saratu ba,burinsu su Shiga gabad'ayan su,hakan yasa suka had'u a gidan Habiba suka tattauna akan gara suje su gano ko lafiya Saratu shirun yayi yawa,ko wayarta aka kira ba a samunta,sun san dai a wannan lokacin Salisu baya gidan ya tafi kasuwa balle suyi Arangama da shi.

 Suna fitowa suka hangi Malam Arabi zai wuce ta layinsu,da sauri Harira ta tab'o Habiba tana dariya tace.

“Habiba ga mutuminki fa”

Duk suka kalleshi ganin yadda yake sauri gemunsa yana tsalle suka tuntsire da dariya,Malam Arabi ya saci kallonsu jin dariyarsu ya k’ara sauri yana d’aga k’afafu yana zungura k’eya,gudun ma kar su kulashi,domin ya san magana ta bazu a unguwar akan Cizon da Habiba ta gallara masa a Al’aura,amma ina!bai samu nasarar Hakan ba,domin kuwa Zahra’u ce da azamarta ta fara k’wala masa kira.

“Malam Arabi,Malam Arabi,Malam Arabi…!

Yayi musu banza kamar bai jisu ba yana k’ara sauri,amma sai da suka had’a da sassarfa suka cimmasa suna shan gabansa.

Ya d’ago yana harare harare yana satar kallon Habiba,matar da ta haifar masa da jinyar Cibiya yana zaman zamansa,Zahra’u ce ta fara zubewa tana gaisheshi,da k’yar ya amsa yana basarwa yana kau da kai yace.

” Ya akayi..?Lafiya dai ko..?

“Lafiya k’alau Malam,Daman muna ta shirin zuwa mu dubaka,Ashe abin da ya faru kenan Malam?to Allah ya tsare gaba ya kad’e tsautsayi da Asara”

Zahra’u ta ambata tana k’unshe dariyar ta.

Malam Arabi ya k’ara had’e rai ya karkata hularsa gefe yana muzurai kamar bai gane me take nufi ba yace.

“Me fa? Me kuma ya faru?ko ance muku bani da lafiya ne?

Harira ta kama hab’a tace.

” Yo Malam muna magana ne akan Aljanun Habiba da suka so tsige ma Cibiya fa,bamu ji dad’in abin ba Malam,Gashi k’anwata ma tana fama da Aljanu muna shirin kawota gurinka a taimaka ayi mata Ruk’iyya Malam,kuma wall…

“Ku bana son d’ibar albarka…

Malam Arabi ya katse Harira cikin sababi yana zare idanuwa da makyarkyata,sannan ya d’ora da cewa.

“Da man labarin da nake ji a kanku gaskiya ne ba k’arya ba? Wato rashin mutuncinku da iskancinku yazo kaina kenan?ni zaku kawowa shakiyanci?na fi ku iya shakiyanci da iskanci,nan da kuka ganni D’an iska ne Lamba d’aya,ni k’olo ne a fagen iskanci,gardi ne a rashin mutunci,Dan haka Ku saita kanku ku kama kanku,in ba haka ba yau idan na hau buzu na billahillazi huwar rahmanu a kanku zan kwana,Girman Allah Yaseen mai dabaibayi da waraddallahu zan ta ja muku,,Allah ya dandab’en min ku,Aradun Allah washegari daga wadda zata tashi a makance,sai wadda zata tashi a lauye,sai wadda zata tashi a k’andare,sai wadda zata tashi a mokad’e,kushiga Hankalinku dani ba a yi min irin wannan,Yanzu sai na maida mutum abin kwatance,Y’an iska kawai gafalallu marasa daraja,Ku jira Ku gani k’arshenku ba zaiyi kyau ba indai Baku sauya hali ba,lalatattun banza lalatattun wofi masu cin Amanar mazajen su”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button