BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya juya ya kalli Habiba duk da a tsorace yake,yace.

“Ke Kuma tsinanniya matsiyaciya haddina da kika keta min kika cafkar min Al’aura na barki da Allah,yadda kika sa min jinyar Cibiya banji ba ban gani ba insha Allah sai Cikinki ya kumbura Yayi bindiga yace Tushhhhhh….!Lalatacciyar wofi kawai.

Yana fad’in hakan ya wuce fuuuu!yana ta sababi yana cilla hannaye,nan kuwa tsabar kunya ce ta rufeshi,ga Shakkar Habiba da yake ji,don kallon da take masa a lokacin zata iya cafko mak’wallaton wuyansa ma ba Cibiyarsa ba.
Yana wucewa suka kwashe da dariya har da tafawa.

Harira tace.

” Tsinanne mai kama da alade borin kunya fa yake,Gaskiya Habiba kin gurji mutuminnan da yawa,ku dubi gingimemen tumbi irin na Malam Arabi, amma Cizo yasa cikin ya koma Yayi lak’wam”

Suka kuma bushewa da dariya suka nufi Gidan Saratu,Habiba na fad’in.

“Duk gurzar da nayi masa ai bata kai wadda Yayi min ba,kai mutuminnan baida imani ko kad’an Harira,iya k’arfinsa ya zage ya dinga laftar bakina,sanda ya sakar min bulalar nan wallahi na zaci bom aka tayar a bakina,saboda shine shugaban mak’aryata na duniya har da cewa Babalalo wai yaga aljanu a bakina suna rawa da juyi,Allah ne ya taimakeshi ya tunkud’eni amma da niyyata yadda na cafki Cibiyar nan wallahi sai na tsigota,da man gata doguwa Allah yai masa Cibi”

“Shaharani kenan” Shafa’atu ta ambata lokacin da suka shiga gidan Saratu suna k’wala sallama.

Zahra’u ta d’aga murya ta na fad’in.

“Kina ina ne Mace me lek’e,Ko nace Y’ar Malam tak’i halin Malam,fito gamu munzo biko”

Saratu da ke d’aki ta na had’a kayan wanki ta jiyo muryar manyan Aminanta,da sauri ta cillar da kayan ta fito tsakargida da gudunta har zaninta na shirin fad’uwa.

Comments
Share
Pls

BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️
[8/6, 09:42] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????

????️ BAHAGON LAYI ????️

    (GIDAN AMARYA)

TARE DA ALK’ALAMIN✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

MARUBUCIYAR????

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

     *DA KUMA*????

BAHAGON LAYI

BABI NA SHA BIYAR DA NA SHA SHIDA

Follow me on watpad Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

SADAUKARWA GA:

HASSANA D’AN LARABAWA FANS,WANNAN SHAFIN KU NE KYAUTA A GAREKU MASOYANA????????????

Ta na zuwa ta fad’a jikinsu ta na dariyar ganinsu,suka rungumeta suna dariya suna kallonta,Harira ta nufi ktcheen tana bud’e kwanuka ta na fad’in.

“Me zan samu ne?nifa kwad’ayi nake ji yau tunda safe wallahi na rasa abin tab’awa”

Ta bud’e tukunyar da ke kan risho ta lek’a,da sauri ta d’ago tana b’ata fuska tace.

“Wannan gardin fa Saratu?bak’ik’k’irin da shi kamar d’uwaiwan mijinki….

Saratu ta waigo ta harareta tace.

” Harira shugabar y’an iska ta duniya,d’umamen tuwon ne me kama da mazaunan mijina?to babu kyau dai wulak’anta abinci domin wani yana nan yana nema”

Ta rufe tukunyar ta na tab’e baki ta fito rik’e da k’ugu,sannan ta kalli Saratu ta shek’e da dariya tace.

“Au Saratu wai nan kece maiwa mutane wa’azin babu kyau wulak’anta abinci?yau Saratu kece kika dafa tuwo a tukunyarki?kamar ba kece Y’ar malam tak’i halin malam ba?kamar ba kece kwanaki da Salisu ya siyo dawa kika bayar aka nik’o kika kwab’a garin kika juye shi a Masai ba?a k’ok’arin ki na ki tabbatar masa bakin ki ba zai ci tuwo ba sai shinkafa da taliya?ni yau sai naga duk kin canza Saratu,da alamun idanuwanki sunyi Arangama da Malam kunnuwanki sun sha wa’azi ko?

Saratu ta sauke ajiyar zuciya ta shige falonta,duk suka bita a baya suka samu waje suka zauna,amma Harira na tsaye k’ik’am,idanuwansu akan Saratu suna jiran jin maganarta domin alamu sun nuna bakin nata akwai magana.Ta gyara zamanta kafin tace.

” Kamar yadda kika fad’a ne Harira,tabbas Malam yazo gidannan kuma Yayi min maganganu masu shiga jiki,ya tsoratar dani sosai wallahi,shiyasa kwana biyu bakwa ganina ina fitowa,sannan D’an lek’en da na saba ma duk na daina,duk da ina jina tamkar a kurkuku,kuma kamar wadda aka sawa mari aka d’aureta,amma ina ganin duk da hakan gara mu hak’ura da yawace yawacen gidajen juna,kowacce ta zauna a gidanta tayi zaman aure,mu gyara alak’armu da mazajenmu,a hankali zamu saba har ya zame mana jiki,idan ba haka……

“Dakata Saratu….
Habiba ta katseta tana d’aga mata Hannu,sannan ta cigaba da magana tana k’ank’ance idanu.

” D’an k’aramin wa’azin da Malam me almajirai Yayi miki shine ya karya miki zuciya haka?to bari kiji yanzu muka sa d’amba wallahi,duka shekarunmu nawane da za a kime mu a gida a hanamu rawar gaban hantsi,mu dai ba sata ko yawan iskanci muke zuwa ba,ba kuma wani layin ko gidajen muke tafiya yawan gulmace gulmace ba,abin mu iya imu imu ne,in zaki farka daga barci ki farka,in kuma wa’azin Malam ne yasa jikin tak’aura Yayi la’asar shikenan ,mu dai yau ma nan da kika ganmu Gidan Amarya zamu antaya,in kinga zaki bimu ki tashi kisa kayanki,in kuma ba zaki ba mu d’aware mu barki,mu dai yau a Gidan Amarya zamu wuni sai mun maida k’walamar mu”

Habiba na direwa Shafa’atu ta d’ora da cewa.

“K’warai kuwa Habiba,Dan wallahi yau bakina ba d’ad’anon da yake son ji sai na dankalin turawa,Allah dai yasa Angon ya siyo”

Zahra’u ta karb’e zancen da cewa

“ke kuwa Shafa me zai hana ya ajiyewa Amarya dankalin turawa,kinga kuwa nima ina marmarinsa yau idan nayi ido biyu da shi cin k’oshi zan masa billahillazi”

Harira ta kwashe da dariya ta na fad’in.

“Ku jini da Mayun yara,wato kun sa rai za ku ci dankali ko?
Ta k’ara juyawa ta kalli Habiba tana dariya ta cigaba da cewa.

” Ke Habiba shugabar mayu ta afrika ba zaki ci dankalin turawan ba?ko da yake kin fi kauri wajen maitar Diddigar k’uli k’uli ko?
Ta mak’e murya ta na tsokanar Habiba.

“Baba da Diddiga”?

Suka kwashe da dariya suna kallon Habiba,Habiba tayi tsaki tana kau da kai.

Nan suka maida hankali kan Saratu suna ta zuga ta akan ta watsar da wa’azin Malam kawai ta bisu,in yaso sai ta dawo da wuri kafin Salisu ya dawo daga kasuwa,Shafa’atu har da cewa.

” Ni nan da kika ganni ma bak’i zan yi,k’annen Kamilu ne su biyu za su zo yau,tun jiya yake jaddadamin ,amma wallahi ba zan zauna ba sabgar gabana zan tafi,idan sun zo su jirani a k’ofar gida in zasu jira”

Haka su kayi ta zuga ta,amma Saratu tsoro ya cika zuciyarta ta na jin tsoron binsu,gashi tana son aje gidan Amarya da ita a wargaje ,da suka ga tak’i amincewa sai suka k’yaleta suka mik’e Dan tafiya.

Shaed’an ya cigaba da tunzira zuciyarta yana yi mata sak’e sak’e,yana raya mata kar ta yarda a tauye mata hakki,ita Y’ar Adam ce mai cikakken iko da y’ancin yin abin da ta zab’awa rayuwarta,ga su Harira nan babu Wanda aka tauye sai ita?kawai ta tashi ta bisu idan yaso sai ta kiyaye ta iya takunta.

Har sun je Soro ta k’wala musu kira ta tsayar da su,da Hanzari ta zura kayanta tazo ta tarar dasu, suna tayi mata tsiya wai”waya gaya mata borno gabas take”

Saratu tayi dariya,suka fito ta kulle gidanta ,sannan suka nufi gidan Amarya.


Suna ta bin falon da kallo har ta k’araso ta dire musu ruwa da lemon da ta d’akko musu a fridge d’in ta,sannan ta zauna kan kujera ta dubesu da k’ayataccen murmushi akan fuskarta ta gaishesu.
Har rawar baki suke wajen Amsa gaisuwar ta,suna washe baki,ta zuba musu lemon ta basu kowa a cup,babu alkunya suka karb’e kowacce ta kai bakinta ta shanye,suna tand’ar baki.
Wucewar minti d’aya Harira tayi gyaran murya ta gyara zama,sannan ta dubi Amarya tace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button