BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Bari na gabatar miki da kanmu tunda na san baki sanmu ba kuma baki ganemu ba,ni dai sunana Harira me kitso,wad’annan kuma ga Habiba,ga Shafa’atu,ga Saratu ,ga Zahra’u,dukkanin mu a wannan layin muke zaune kowacce da gidanta,kuma duk mun saba da juna ke ce sabuwar zuwa shiyasa muka ce zamu had’u mu shigo Dan mu gabatar miki da kan mu ki sanmu zumunci ya k’ullu tsakaninmu”
Amarya tayi murmushi kanta a k’asa saboda kunyar amarci,cikin sanyin murya ta fara magana.
“Amma nayi farinciki da zuwanku,daman nima ina da niyyar Shiga gidajenku idan an kwana biyu,to sai gashi kun rigani zuwa ma,to ni dai sunana Hauwa’u,kuma ina fatan zaku rik’eni Hannu bibiyu a matsayin ku na yayyena wad’anda suka girmeni ,sannan ina fatan zumuncin mu ya d’ore ku dinga saitani a hanya da zarar kunga zan kauce”
Habiba tayi dariya tace.
“Ashe ma sunan kakata ne dake,kulun majadan Y’ar tsohuwa me ran k’arfe,to ki shirya za ki bani kud’in shara kuwa,kuma kar ki damu da Hannu d’ari zamu rik’e ki ba hannu biyu ba,ke dai kawai ki saki jikinki damu rayuwa muke mai dad’i babu takura kai”
Ta jinjina kai tana murmushi a lokacin da suka ji sallamar Mijinta,ya shigo falon rik’i rik’i da ledoji,su Harira aka had’a baki ana gaisheshi,ya amsa yana murmushi duk da dai bai sansu ba,Amarya ta mik’e tana kwarkwasa da yanga ta nufeshi ta karb’i ledojin hannunsa,ya sakar mata murmushi yana d’aga mata gira,Su Habiba aka saki baki ana kallonsu ana k’iftawa juna idanu,Yana shirin wucewa d’aki Amarya ta fara magana cikin yanga ta na yi Masa bayanin su Harira,ya washe baki ya juyo yana yi musu godiya, ganin ya samu masu kula masa da matarsa da yake tsananin so da k’auna.su kam dad’i suka ji ganin yadda ya sakar musu fuska,Saratu kam kallo take ta bin su da shi bakinta a sake har suka shige d’akinsu suka barsu a falon.
Zahra’u ce ta lura da Saratu da hankalinta ya tafi wani wajen,ta d’aga hannunta ta zubawa Saratun d’ad’o a cinya,firgigit ta dawo hayyacinta tana sosa cinyar da sauke ajiyar zuciya,duk suka dubeta suna tambayarta da idanuwansu.
Tayi murmushi ta rage murya a hankali tace.
“Wallahi mutuwar ido biyu nayi fa!kunga mijinnata wani D’an sumulmuli da shi ,sai naji gabad’aya na k’ara raina Salisu wallahi,gaskiya wannan ta cab’a da yawa,sullutuwa kenan”
Zahra’u ta doke bakin Saratu tana harararta tace.
“Amma Saratu baki da hankali wallahi,da aurenki ki dinga yaba mijin wata?nifa duk iskancina Bana tab’a mijina ya kamata ki dinga lura,kullum cikin raina Salisu kike kuma ni banga aibunsa ba,nifa duk munin mijina ganinsa nake yafi kowane namiji kyau a idanuwana”
Duk suka yi dariya a hankali,Harira ta cafe zancen tana kallon Zahra’u.
“Kinga Zahra’u nifa banga laifin Saratu ba Dan ta fad’i ra’ayinta,gaskiya da nice Saratu ba zan tab’a bari malam me almajirai Yayi nasara a kaina wajen tursasani auren gardi irin Salisu ba,Nifa har bana k’aunar na had’a ido da shi sai na ganshi tamkar damisa a gabana,ai Saratu kam kina hak’urin zama da Salisu har ki kalleshi a matsayin miji,wai!ni da titib’iri…”
Suka kwashe da dariya,Saratu ta kalli Habiba tace.
“Habiba ba babban Mara mutunci irin Babalalo ,Dan Allah kice masa idan Salisu yazo aski wajensa ya daina yi Masa tal kwabo,billahillazi huwar rahmanu rannan da Yayi masa ya shigo min na zaci bayan k’warya ya kifa a kansa saboda yadda Yayi tol da shi,nayi mamaki nace masa” kai kuma ina ka samo k’warya ka kifa a kanka kamar wata hula”ya shafa kan yana dariya yace “Ke Hajiyata Aski na sha fa,malamina ne ya bani sa’ar wani magani yace idan nayi Aski na shafe kaina da maganin,idan na fita duk budurwar da naci karo da ita rud’ewa za tayi a kaina tamkar na kwanta taita lasar Tolin kaina,budurwa zan samu zakad’ed’iya wadda zata tarairayeni ta riritani” dariya ta kamani kamar me,nace masa”Amma duk budurwar da zata ganka da wannan tuk’ek’en kan yasha soli taji ta na sonka ta d’ibga asara wallahi.
Domin ni banga abin so da sha’awa a wannan k’walelen kan kamar duro ba”
Suka kwashe da dariya jin maganar Saratu,gaskiya ta na cin fuskar Salisu da yawa.
A dai dai lokacin Amarya da Ango suka fito,su Harira a kayi k'us ana sunkuyar da kai,Yayi musu sallama da shirin wucewa kasuwa,Harira ce kan gaba wajen yi masa fatan dawowa lafiya,abin da bata yiwa nata mijin.
Amarya ta dawo ta zauna bayan ta rakashi har bakin k’ofa,suka cigaba da hirar duniya da labarai kala kala,tun bata sake ba har ta sake ta fara kwasar dariya kamar cikinta zaiyi ciwo saboda hirar da suke,da alamun matan suna da abin dariya sosai,suna zaune har azahar tayi babu shirin tafiya,Amarya ba taji wani Abu a ranta ba ganin sun shantake babu wadda ta nemi komawa gidanta,ganin kar ta barsu da yunwa sai ta mik’e domin shiga kitchen ta d’ora girki,ta d’ebo kayan miya za ta gyara nan da nan uwar kankanba Harira ta mik’e ta amsa ta na cewa.
“Bari na gyara miki Amarya, mu na zaune ai ba ma bar Amarya da aiki ba”
Tayi murmushi ta mik’a mata ta na cewa.
“Ai da kin barshi na gyara,kar na saki aiki,gashi Hubby ma ya fita bai mik’a min markad’en ba,ba wuta balle na markad’a a blender”
“Har kin samu Almajiri D’an aike kenan?”
Habiba ta tambayeta.
Ta amsa ta na k’ok’arin d’akko tukunya a drawer d’in kitchen.
“Ah ah me kika gani?”
Habiba tayi Hamma saboda yadda cikinta ya fara kiran ciroma tace.
“Naji kince Hubby bai kai miki markad’e ba,na zaci Almajinki ne Hubby d’in”
Amarya tayi dariya sosai sannan ta dubi Habiba tace.
“Haba dai!Almajirin zan kira da Hubby?ina nufin mijina fa,Hubby ai sunan Soyayya ne”
Zahra’u ta shek’e da dariya ta na fad’in.
“To ke Amarya waye ya fad’a miki Habiba ta san wani sunan soyayya,yadda kowa yake ambatar mijinta Babalalo ita ma haka take ambatarsa,dukkansu nan babu wadda take b’oyewa mijinta suna sai ni kad’ai,domin ban raina mijina ba,shiyasa na mallakeshi a hannuna sai yadda nayi da shi “
Duk suka fara hararar Zahra’u,yayin da Amarya ta matso ta zauna kusa da ita ta na washe baki da fad’in.
“Gaskiya Anty Zahra’u tafiyarmu ta zo d’aya,Dan wallahi kinga dai ban dad’e ba amma ina masifar son mijina kuma ina son na mallakeshi sai yadda nayi da shi,duk fara’ar nan da kuka ga yana yi muku shi mutum ne mai baud’ad’d’en hali wani zubin,duk soyayyar da yake min zan iya yin laifi ya rufe idanu yaci zarafina,to ni kuma bana son ta kaimu ga haka gara ki d’orani a hanya yadda zan mallakeshi kamar yadda kika mallaki mijinki”
“Anzo gurin Hajiyata” Zahra’u ta fad’a ta na mik’a mata Hannu suka tafa, ta nuna sauran da bakinta ta na duban Amarya tace.
“Kin gansu nan babu yadda banyi na d’orasu a hanya ba amma sunk’i,sun riga sun sawa zuciyarsu cewar ba zasu tashi tsaye su mallaki mazajensu ba wai gara suci uwar juna,basu san y’an alallab’a bane,sai da siyasa ake kamasu,mazan yanzu ba k’ananan y’an iska bane sai da wuta”
Saratu ta tab’e baki tace.
“Ni dai da na tsaya mallake Salisu gara na siyo D’an bunsuru na ajiye shi na mallakeshi Yayi min biyayya wallahi,yo ni kam meye abin mallaka a Salisu banda d’ibga asara?
” Balle kuma Sunusi,ina ruwan tsami gaye”inji Harira ta na bushewa da dariya.
Habiba ta lashi baki ta na kanne idanu tace.
“Kina ambatar tsami gaye naji sha’awarsa wallahi,ina ma zan ganshi na sha”
“To k’walamammiya……
Shafa’atu ta katseta ta na dariya sannan ta cigaba da cewa.
” Zo in rakaki ki siyo,ana siyarwa a gidan Malam Arabi”
Habiba ta dalla mata harara ta na sakin tsaki,basu da buri illa su tsokaneta akan Malam Arabi.