BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Har wajen la’asar suna gidan bayan sun ci abinci sun yi sallah,Zahra’u ta na ta yiwa Amarya Hauwa lakca,nan take fad’a mata akwai wani maganin mallaka da ta tab’a amfani da shi kuma taji dad’insa,a wajen wata Y’ar sokoto ta siyeshi dubu biyar,amma zata yiwa matar waya a kawowa Amarya Hauwa’u.
Hauwa ta dinga murna sosai,har da shigewa d’aki ta Lalo dubu biyar ta dank’awa Zahra’u a hannunta,nan da nan Zahra’u kuwa ta lalubo wayarta ta dokawa Y’ar sokoto kira,ba a jima ba ta d’aga suka gaisa,Zahra’u ta fara bayani.

“Wata Amarya ce k’anwata take son kulle zuciyar mijinta,ina fatan akwai wannan maganin mallakar da kika tab’a bani nai nasarar kulle zuciyar K’asimu da shi ?”

Y’ar sokoto ta amsa da karad’inta duk suna jiyota saboda wayar na hands free ne.

“Zahra’u zareriyar mata aikuwa akwai wannan had’in,domin kuwa yanzu ma an k’ara da wasu sinadarai Wanda idan mace tayi amfani da shi ko wuta ta nunawa mijinta tace ya fad’a afkawa zaiyi kai tsaye.

Nan da nan Hauwa Amarya ta soma murna,duk da Y’ar sokoto tace kud’in ya ninka ya zama dubu goma amma Hauwa tace zata biya taji ta gani.

Aka gama magana akan washegari Y’ar sokoto zata kawo magani a bawa Amarya Hauwa domin ta mallaki Mijinta.

COMMENTS
SHARE
VOTE
PLS

BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️
[8/7, 11:05] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????

????️ BAHAGON LAYI ????️

    (MAGANIN MALLAKA)

TARE DA ALK’ALAMIN✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

MARUBUCIYAR????

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

     *DA KUMA*????

BAHAGON LAYI

BABI NA SHA BAKWAI DA NA SHA TAKWAS

WATTPAD:Hassana3333
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

GODIYA MARA YANKE WA GAREKU MASOYANA,HAK’IK’A DA BAZARKU NAKE TAKA RAWA,MUSAMMAN GROUPS D’IN????

AISHA BAGUDO FANS
TABITAL PULAKU
ZAUREN JIKAR NASHE
JIDDA REAL FANS
TASKAR FATI TEEJAY
Y’AR MUTAN DIKKAWA NOVELS
WAYE SILAR LALACEWATA FANS
BAHAGON LAYI FANS

DA SAURAN GROUPS D’IN DA BAN AMBATA BA DUK INA SONKU SOSAI,INA KUMA GODIYA GA MARUBUTAN DA SUKE BIBIYAR WANNAN LITTAFI DOMIN KARANTAWA,HAK’IK’A INA JIN DAD’I SOSAI,ALLAH YA BAR ZUMUNCIN MU ????????????????????????

Sai yamma lik’is mijinta ya kusa dawowa sannan suka yi shirin komawa gidajen su,kafin su tafi sai da suka fad’awa Hauwa yanayin tsarin zamantakewar da suke yi a tsakanin su,karb’a karb’a ne tamkar mulkin farar hula,kowacce akwai randa za a yini a gidanta a bararraje ayi girki da hira,hatta da cefane da Kansu suke zuwa basu da almajirai,saboda almajiran yanzu tak’adirai ne a cewar Habiba.

  Nan Hauwa Amarya tace.

“Nima na bada goyan baya akan hakan,domin na kan samu kaina cikin kewa idan Hubby ya fita,bai wani d’au Hutu Dan tayani zama ba,gashi zuwan da akewa amare ni ba a yi min ba,sai naji Gidan yayi min ba dad’i,amma yau idan ya dawo zan masa bayanin abin da kuka ce min Dan ya zama ina fita da saninsa”

Har sunje bakin k’ofa Saratu ta waiwayo a zabure ta dubi Hauwa tace.

“Amma ke Y’ar fari ce a gidanku ko?”

Hauwa ta girgiza kai tace.

“Ah ah me kika gani,ina da yayye da yawa ma,ko yanzu tare da yayata akayi bikinmu”

Saratu ta tab’e baki tace.

“Ganinki nayi kamar wata gab’uwa sak’andama,yo in ba gab’unta ba ta ya ya za ki ce zaki sanar da mijinki wannan maganar?d’azu fa naji kince D’an tarangahuma ne yana da zafi,to akul kar ki masa maganar in ba so kike ya nane miki ido d’aya ba ,ki zama irin uwar Mijina Iya me ido d’aya”

Suka k’yalk’yale da dariya,Hauwa ji take kamar ta bisu domin ba ta gaji da jin shaftarsu ba,Shafa’tu ce ta fara gaba ta na cewa.

“Ni fa Saratu sai da kika ambaci Uwar mijinki na tuna yau k’annen Kamilu za su zo,gashi yamma tayi k’ila sun gaji da jira sun ware ma”

Amarya Hauwa da k’yar ta koma bayan ta rakasu soro,suka yi sallama da Zahra’u akan gobe zata kawo mata maganin har gida.
Suna fita suka hango k’annen kamilu su biyu a k’ofar Gidan Shafa’atu,d’aya siririya d’ayar kuma k’atuwa,me k’ibar ce fuskarta a had’e tasha kunu saboda sunfi awa uku tsaye suna jiran Shafa amma shiru duk da ta san da zuwansu.

Suka k’arasa gabansu, Shafa’atu ta d’an washe ba ki tana Sosa k’eya tace.

“Ah ah Amina Ashe har kun iso?nan mak’ota muka Shiga dubiya dafatan dai baku jima da zuwa ba?”

Amina tayi banza da ita tana huhhura hanci,sai Karima ce ta Amsa da cewa.

“Anty Shafa’atu wallahi wajen awanmu uku muna jiranki,da tafiya ma zamu yi sai kawai muka tsaya”

Kafin Shafa tayi magana har Harira ta rigata tankawa.

“Ku kuwa kuka yi ta zama a rana Dan naci sai kace wasu mayu,maimakon ku d’aware zuwa Inda kuka fito?jibi dai waccan Y’ar sukutar yadda rana ta k’ara hurata?wannan dai da Alkubus ce ke za a kwashi girki,ni da dindimi”

Amina ta waiwayo ta zabgawa Harira wata shegiyar Harara,sannan cikin k’atuwar murya tace.

“Ke Dan kutumar ubanki nice Y’ar Sukuta?da man baki San haushinki nake jiba kaf layin nan ke kika maidasu haka,wallahi kika sake cemin Y’ar sukuta sai nayi wa bakinki lukuni,wallahi zaneki zan yi na zauna a kanki”

Duk ragowar suka ja baya saboda tsoran Amina,Dan ba k’aramar k’atuwa bace,amma sai Harira ta fara fiffik’alewa tana nuna Amina da Hannu tana masifa duk da yadda Shafa take janye ta,domin ta san halin Amina,akwai sanda ta tab’a marinta sai da ta kusa suma,Harira kam tak’i ji ta fara zagin Amina.

“Lallai yarinyar nan ba ki da mutunci ni kike zagi?to bani kika zaga ba Zulailaya me kan tantabara kika zaga,an gaya miki ni tsoranki zan ji,bisimillah idan kin fasa dukana kin ci bantan ubanki….

Kan su Ankara suka ga Harira ta wuntsula ta baje saboda mangarin da Amina ta kai mata,ta haye ruwan cikin Harira ta fara sakar mata naushi a kumatu,ihu Harira ta fara da k’arfi jin Amina zata b’urma mata kumatun ta tsabar naushi,da sauri suka yi kan Amina zasu d’agota, tasa Hannu ta ingijesu gabad’aya suka tarwatse har goshin Saratu ya k’ara dukan bango,ai da sauri Saratu ta mik’e tana murza goshinta me kama da suwaita ta nufi k’ofar gidanta tana cewa.

” ina dalili haka kawai a sake rub’a min goshi,gashi ban ajiye wani a k’ark’ashin gado ba,shikenan dani babu spare “

Harira kam ranar tasha duka a hannun Amina ba kad’an ba,bakinta ya karkace kamar wadda ta kamu da paralyze, hak’ori biyu na gaba suka cire ba ki sai jini,idan ta bud’e baki zata yi kuka sai su ganta tamkar horuwa,Ashe dai hak’ori rufin asiri ne a jikin mutane.

Amina kam da k’yar ta d’aga Harira sai da taga Karima na kuka ganin zata yi kisa,sannan ta d’agata ta na ta d’ura mata ashar,Amina har da cewa.

“Kad’an kika gani yanzu,na rantse da Allah sai na auri mijinki na shigo gidanki na kafa sarauta,duk wani iskancinki yazo k’arshe,Tsinanniya me warin mushen jaki kawai”

Da k’yar Shafa’atu da Karima suka janye Amina suna bata hak’uri sai numfarfashi take,yayin da Habiba da Zahra’u suka janye Harira da kamanninta suka sauya saboda dukan da ta sha,suka nufi k’ofar gidanta Dan Shiga da ita gida,Habiba ta rage murya Dan kar Amina ta jiyo ta tace wa Harira.

“Gaskiya Harira kin daku,amma kin bani haushi da ba ki rama ba,maimakon kiyi aljanun k’arya irin nawa,yarda nonuwanta suke ruguza ruguza kamar jarka ki cafki kan d’aya ki cizgo tsinanne,amma shine kika kwanta duk ta zubda miki hak’ora bakinki duk gib’i kamar k’ofar wambai?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button