BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Harira ta zabgawa Habiba Harara ganin basu taimaketa da komai ba an lallasata,said a suka je k’ofar Gidan Harira ta bud’e k’ofa zasu shiga sannan ta waiwayo fuska a kumbure,ta bud’e wargajejen bakinta ta d’aga murya ta na Nuna Amina tace.
“Allah ya isa tsinanniya,Y’ar daba me kama da buhun kwaki,ban yafe miki ba annamimiya matsiyaciya,Y’ar sukuta kawai”
Amina tayi kukan kura ta fizge daga hannun Shafa’atu ta nufi Harira,da sauri Harira ta shige soro ta banko k’ofarta tasa sakata,ta garawa Habiba da Zahra’u k’ofar a fuskarsu,suka koma da baya suka fad’i,a dai dai lokacin da Amina ta k’araso gabansu,Zahra’u ta mik’e da azama tana tatata ta afka gidanta,yayin da Habiba ta fara rarrafe ta kasa tashi,tuni fitsari ya kubce mata a wando don tsoron Amina ganin tayi mata sank’ank’an aka,ba ta san lokacin da ta fara murmushi ta na kad’a kai ba,ta na kallon Amina tanai mata wak’a wai duk don’ ta k’yaleta.
“Amina Amina fanteka,Amina Amina Fanteka”
Dariya ta kama Amina ganin fitsarin da Habiba ta saki,ta juya ta na tuntsira dariya har da rik’e ciki,a hankali Habiba ta zame da rarrafe ta shige gidanta kan Amina ta sake waiwayowa,bata San abin da ya sanyayar da k’afafunta suka kasa mik’ewa ba.
Allah ya taimaki Saratu ta tsallake wannan sirad’in,Domin Salisu bai Ankara da fitarta ba lokacin da ya dawo,kuma yadda yaga kwana biyu ta nutsu ta na yi Masa biyayya sai ya zaci ta gyara halinta.
Ita kam Harira ranar a kan Sunusi ta huce haushin dukan da tasha gun Amina,ta dinga surfa masa masifa da bala'i ta hanashi sakat,da ta addabeshi sai ya fice ma ya bar mata Gidan,bai dawo ba sai da tayi barci,da ya fita ne ma suka had'u da Kamilu yazo ya bashi hak'urin abin da Amina k'anwarsa tayi wa matarsa Harira,a nan yake jin dalilin da yasa yaga Harira da wawulo a bakinta,tunda dai ya san ta girma da famfara balle yace.
A gaban Kamilu ya dinga tuntsira dariya yana murna da abin da Amina tayi,daman ya gaji da halinta yana ta so ya samu Wanda zai masa maganinta,aikuwa sosai yaji dad’in hakan,shi Kansa Kamilu saida ya dinga mamakin dariyar da Sunusi yake shek’awa babu damuwa a ransa ko kad’an.
Washegari da safe sai ga Y’ar sokoto ta bayyana a gidan Zahra’u,sai da Zahra’u taga rana ta take sannan suka kwashi jiki suka fad’a gidan Amarya,a lokacin sun san mijinta baya nan,ba k’ara min murna Hauwa tayi ba da ta gansu,ta kawo musu ruwa da lemo har da cincin sannan ta samu waje ta zauna suka gaisa.
Y’ar sokoto ta bud’e k’atuwar Jakarta ta na fito da magunguna iri iri,na Hausa da na turawa,ta kalli Hauwa tana dariya tace.
“Tunda ke Amarya ce bakya buk’atar maganin matsi,Dan na san a matse kike gam,kawai zan baki maganin da zaki k’ara ni’ima,da kuma uwa Uba na mallaka,abin da zan baki idan har kika yi amfani da shi a yau bisa k’a’ida to ina tabbatar miki mijinki ya shiga zuciyarki kin kulleshi ba shi ba fitowa sai yadda kika yi da shi “
Hauwa ta k'ara washe baki dad'i ya cikata sosai,ta dinga jijjiga kai ta na kallon Zahra'u ta na murmushi.
Y’ar sokoto ta zaro wata farar roba sannan tace da Hauwa.
“Kinada reza?Dan aikin na buk’atar reza da zare da allura,amma ni akwai zare da allura a jakata”
Da sauri Hauwa ta amsa.
“Eh akwai reza,in d’auko ne?”
“Eh d’auko,sannan ki had’o da matashin da kika san Mijinki yana d’ora kansa akai ya kwanta idan za ku yi bacci”
Hauwa ta mik’e da Hanzari ta nufi d’aki,Jim kad’an ta fito da matashi a hannunta da reza,Y’ar sokoto ta karb’i matashin ta cire rigar jikinsa,sannan tasa reza ta D’an farkashi kad’an,duk Hauwa da Zahra’u suna kallonta,ta bud’e wannan farar robar ta fito da abubuwan da ke ciki,Hauwa ta zaro idanuwa ganin layoyi da wani kwad’o da mukullaye,Y’ar sokoto tasa mukullin jikin kwad’on ta bud’e shi, ta kalli Hauwa tana murmushi tace.
“Kinga yadda na bud’e kwad’on nan ?to a yanzu haka mun bud’e zuciyar mijinki”
Sannan ta d’akko layar ta sak’ala a jikin kwad’on tasa D’an mukullin ta kulle tsaf,ta kuma kallon Hauwa da ta tsura mata idanu tace.
“Haka nan yadda na kulle kwad’on nan mun kulle zuciyar mijinki kenan,sai yadda kika yi da shi “
Ta jawo matashin inda ta b’ula ta zura kwad’on da layar da mukullayen nan a cikin matashin,sannan tasa allura da zare ta d’inke tsaf,ta maida matashin cikin rigarsa ta mik’awa Hauwa,Hauwa ta mik’o hannu ta karb’a tana sauraren bayanin Y’ar sokoto.
“Matuk’ar yau mijinki ya aza kansa kan matashin nan kin gama mallakarsa a tafin hannunki,ina tabbatar miki biyayyar da zai miki ko uwar da ta haifeshi ba zai mata ba”
Saboda jin dad’i dubu goma ne kud’in maganin,amma Hauwa dubu sha biyu ta bawa Y’ar sokoto har da turmin atamfarta gallele na cikin lefe,Y’ar sokoto ta dinga murna,da suka fita ta dinga yiwa Zahra’u godiya da ta had’ata da mutuniyar arzik’i.
Amarya Hauwa akayi kwalliyar tarbar miji aka yi girki mai dad'i yaji onga da tafarnuwa,Ango Idrees ya dawo ya kwashi girki kunnuwansa na motsi,ko irin hirar Daren nan Hauwa bata bari sunyi ba ta isheshi akan suje su kwanta bacci take ji,tana wani langab'ewa,shi kuwa ji yake ai gaba ta kaishi tunda ta nemi aje a kwanta da kan ta,suka sauya kayansu zuwa na bacci suka haye gado.
Tashin farko Idrees yana d’ora kansa kan matashi yaji Abu ya tsireshi,da sauri ya muskuta ya ajiye kumatunsa kan matashin,ba zato ba tsammani yaji tsinin Abu yana k’ok’arin b’urma masa kumatu,Ashe tsinin mukulline,da Hanzari ya mik’e yana zare idanu,ita kuwa Hauwa ta zaci maganin ne ya fara ci har ta fara murna a zuciyarta,sai gani tayi ya d’ago matashin yana kallo,sannan cikin b’acin rai yace.
“Wato masu saida matashi sun zama maha’inta mugwaye,a maimakon susa katifa mai laushi sai su dinga zuba yayi da tsummokarai,ina tunanin allurai ne a ciki bakiji yadda suke tsireni ba”
Hauwa ta zaro idanuwa k’irjinta na bugawa ta kasa magana,Idrees ya dinga tattab’a matashin yana girgizawa,kawai sai yaji kacar kacar kacacar a ciki,mamaki ya kuma kamashi,ya kalli Hauwa da gumi ya fara yanko mata yace.
“Jiddatu na wani motsi nake ji da k’ara a cikin matashin nan,d’akko min reza na farke naga abin da ke ciki mana”
Ta sauke gwauron numfashi tana zare ido ta fara in ina.
“Wal…wallahi….banga ..banga rezar ba,babu ..reza a gidannan…ma”
Ya D’an kalleta yaga yadda take a rud’e,kawai sai ya mik’e da azama ya nufi ktcheen ya d’akko wuk’a,yana shigowa d’akin Hauwa ta daka tsalle ta b’uya bayan gado saboda yadda taga wuk’ar na walwali kar taje ya Burma mata,domin yana da zafi bai iya fushi ba,ko kallonta bai yiba yasa wuk’ar ya farke matashin yana zazzago shi,kawai sai kwad’o da mukullaye suka fad’o har da layoyi a jiki,ya yarda matashin yasa Hannu ya d’auko mukullayen yana kallo zuciyarsa na bugawa,a zafafe ya kalli Hauwa da ke mak’ure yace.
“Fito nan”
Ta kasa fitowa jikinta na rawa har ta fara hawaye,ya daka matsa tsawar da ta sa hancin cikinta curewa guri guda jin ya danna mata ashar.
“Ba za ki fito ba sai nazo nan naci kutumar ubanki?
Ta jawo jiki ta fito tana kuka,ya d’aga abubuwan hannunsa ya nuna mata,cikin fushi yace.
” menene wannan?
Bakinta na rawa ta fara magana,a ganinta gara ta gaya masa gaskiya kurum,shiyasa cikin kuka tace.
“Maganin Mallaka ne”
Ya tsura mata idanu kamar ya gaura mata mari yace.
“Maganin mallaka?ni za ki wa Asiri Hauwa?wane D’an iskan ne ya baki maganin domin wayonki bai kai kiyi tunanin yi min asiri ba?
Ta rushe da kuka sosai ta na rantse rantse,sannan ta gaya masa duk abin da ya faru,nan da nan zuciyarsa ta k’ara k’uluwa sosai,ya fara yi mata tambayoyi akan matan bahagon layi ta na ba shi amsar abin da ta sani,so sai hankalinsa ya tashi ganin zasu lalata masa tarbiyyar matarsa,Ashe da gaskene abin da ake fad’a a Kansu?mutane da yawa sun sameshi akan ya kula da matarsa kar tayi huld’a da matan,ya zaci sharri ne Ashe gaske ne,aikuwa tilas ya d’auki mummunan mataki a Kansu ta yadda ko ance su k’ara shigowa gidansa sai sun zura da gudu.
Haka Hauwa ta dinga ba shi hak’uri da nadama,da k’yar ya hak’uri da niyyarsa ya korata gidan iyayenta a k’ara koyamata tarbiyya,tunda cikin kwanaki k’alilan shashashun mata sun fara fatali da tarbiyyarta,amma da ta rungumeshi cikin kuka ta kanainayeshi tilas ya hak’ura ya tarbeta,babu kuma abin da yake jira illa gari ya waye yaga wad’annan mata sun shigo,Lallai zasu ga tijara ganin idanuwansu.