BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar kuwa ya san zasu shigo washegari yak’i fita kasuwa ya zauna zaman jiran shigowarsu,ya mak’ale a d’aki ya bawa Hauwa umarnin kar ta gaya musu yana nan,babu b’ata lokaci ya kira wani abokinsa D’an sanda yace yazo gidansa kuma ya tawo da tiyagas,cikin mintuna k’alilan ya iso ya fita ya shiga dashi har cikin d’aki.
Harira kam Dan masifa ta zauna ma tayi jinyar bakinta kasawa tayi,k’afarta na k’aik’ayin fita,gulma na cinta ta na son zuwa gidan Amarya aji yadda aka kaya da maganin mallaka ko yayi tasiri,aikuwa ta fito ta fad’a gidan Habiba,daga nan suka biyawa Zahra’u da Shafa’atu,suna zuwa gidan Saratu fir tak’i fitowa ta na ganin kamar Salisu zai gane ta fita,babu yadda basu yi ba tace gara tayi lek’en ta yafi mata sauk’i akan ta fita.
Sha d’ayan rana a gidan Amarya tayi musu,aka baje a falo ana kwasar hira ana darawa da tafawa,Hauwa ta biye musu suna tayi mata tambayoyi tana basu amsa.
Zahra’u ce me cewa.
“Ni kuwa kulun majadan ya maganin da aka baki jiya?kin yi amfani da shi ya d’ora Kansa a matashin?
Hauwa ta girgiza kai ta na dariya tace.
” Sosai ma,ai wannan maganin sha yanzu magani yanzu ne,yana sa kansa jikin matashin ya rikice,tsakanin jiya zuwa yau duk abun da na sashi yi min yake da Hanzari “
Harira ta kwashe da dariya wawulonta ya bayyana,tace.
“Shegen sama yana tafiya kamar na sammasa kwankwaso,ai wallahi Hauwa tunda kin mallakeshi karki raga masa,kici Uwatar kawai,in ya raina miki ajawali ki wawushi wannan kurtsitsin kwankwason nasa ki maka shi da k’asa”
Habiba da Shafa’atu suka kwashe da dariya,haka suka cigaba da aibata Idrees suna ci masa mutunci a gaban Hauwa,ita kuma tana ta biye musu,basu san ramin mugunta ta had’a musu ba,suna cikin shewa kawai sai ganin Idrees suka yi a gabansu fuskarsa murtuk,suka fara zare idanuwa suna gyara zama,Habiba ta jawo d’ankwalinta da garin hira ya zame ya fad’i,suka hau rige rigen gaisheshi muryarsu na rawa cike da tsoro.
Yayi wani miskilin murmushi na mugunta ya jinjina musu yace.
“Sannunku wakilan Shaid’an,barkanku da zuwa tatattun y’an iska,marhabun daku shakiyyai fitsararru tantirai,ina muku lale maraba da zuwa gidan da za ku sha tiyagas”
Wani d’imemen tashin hankali ya rufto musu a lokacin da suka ga D’an sanda ya bayyana a gabansu da k’aton kulki a hannunsa,k’ato dashi fuskarta bak’a k’irin babu alamun imani,babu wadda bata saki fitsari a wando ba tsabar tsoro,nan da nan suka fara kuka da Neman Afuwa,D’an sandan ya dubi Harira ya na Nuna ta da kulkin Hannunsa yace.
“Ke yanzu Dan ubanki tsofai tsofai dake bakinki duk ba hak’ora kike shuka iskanci?kina shiga cikin y’ay’an cikinki kuna tab’argaza?
Harira ta fashe da kuka tace.
” wallahi yallab’ai ofisa yarinyace ni shataf,mahangurb’a nasha jiya hak’orana suka zube ba tsohuwa bace”
Ya jijjiga kai ya na zagayesu yace.
“Jiya kin sha mahangurb’a yau kuma za ki ci na jaki kuma kisha tiyagas Dan ubanki,shegu daga yau idan an ce ku sake shiga gidan wani kuyi gulma ba zaku yi ba.
Ya kalli Idrees yace.
” ja matarka ku shige d’aki ka barni dasu “
Idrees ya ja hannun Hauwa suka fad’a d’aki suka rufo k’ofa,Hauwa ta na yi musu gwalo,su kuma suna kuka suna Neman ceto da danasanin shigowa,Allah ya taimaki Saratu bata biyo su ba da har da ita za a tarfa.
D’an sanda baiyi wata wata ba ya fara buga musu tiyagas yana lodarsu da kulkin hannunsa,ihu da kururuwa kawai suke yi suna jin tamkar su mutu saboda azabar,idan ya buga tiyagas sai ya daidaici gadon bayansu ya muk’a musu kulki,Harira kam har a baki ya dinga muk’a mata,wai gara ya zubda hak’oran gulma a huta.
Wani mugun ihu Habiba ta saki jin ya sauke mata kulki a agararta.
Comment
Share
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍️
[8/8, 10:00] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????
????️ BAHAGON LAYI ????️
(MAHAUKACI)
TARE DA ALK’ALAMIN✍️
HASSANA D’AN LARABAWA
MARUBUCIYAR????
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
*DA KUMA*????
BAHAGON LAYI
BABI NA SHA TARA DA NA ASHIRIN
Follow me on wattpad Hassana3333
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
????????????????????????????????????????
SADAUKARWA
WANNA SHAFIN NA K’ARSHE NA SADAUKAR GAREKU Y’AN K’UNGIYATA TA PEN WRITERS ASSOCIATION (PEWA)ALLAH YA K’ARA D’AUKAKA KU DA RUBUTUNKU,YA K’ARA HAD’A KANMU CIKIN AMINCI????????????
Yayin da su Habiba ke Gidan Amarya suna shan uban duka da tiyagas,ita kam Saratu tana mak’ale a soron gidanta ta na aikin lek’e,babu komai a jikinta sai pant da zani tayi d’aurin k’irji,ko D’an kwali da riga da breziya babu a jikinta.
Ta na tsaye ta zuro kanta ta na kallon masu wucewa ta layinsu da gefen layin,duk Wanda zai shige sai ta d'aga masa Hannu tana washe baki,duk kuma lokacin da ta d'aga hannun sai an hango hammatar ta amma ko a jikinta.
Ta na nan tsaye wani Mahaukaci ya b’ullo ta layinsu,a al’adar wannan Mahaukaci unguwa unguwa yake bi da zabgegiyar bulalarsa yana b’oyeta a malum malum d’in jikinsa,babu abin da yake nema sai mata masu lek’e,duk macen da ya kama kuwa kan ta ankara ya fito da bulalarsa ya jik’a mata aiki,kamar yana da masaniyar zai tadda Saratu sai gashi Allah ya jefoshi BAHAGON LAYI.Duk da wasu sunce aljanun kansa ne ke sanar da shi guraren da zai samu mata masu lek’e.
Yana yankowa layin da Saratu ya fara yin arangama ta na mak’e a soro ta na lek’e,gadan gadan ya nufota ita kam bata lura da shi ba hankalinta yana d’aya gefen ta na kallon wasu samari da suke zaune suna lido,yana zuwa dab da ita ya shammaceta ya fiddo bulalar ya d’aga ya zumbud’a mata,cikin d’aukewar numfashin Azaba ta zabura ta juyo ta na kallonsa,tana niyyar magana taji ya kuma sauke mata wata a kafad’arta,inalillahi wainna ilaihir raji’un,ai da Saratu ta kurma wani uban ihu jin zai sauke mata kafad’a tayi tsalle ta fad’a gidanta a guje ta na tumami,gabad’aya ta manta bata kulle k’ofar ba,shi kuwa Mahaukacin ganin k’ofa a bud’e kawai sai ya bita cikin gidan, ya tarar da ita ta na zagaye tsakar gida ta na ihu da Sosa kafad’a,ba k’aramar razana tayi ba da ta ganshi a gabanta,ta d’ora Hannu a ka ta saki wani gigitacen ihu da ya zabura wannan mahaukacin Yayi kanta ya soma tafkarta,ko ta ina kai mata duka yake har Saratu ta fad’i k’asa zaninta ya zame daga ita sai D’an diras,birgima kawai take yi yana jibgarta da bulalar hannunsa ta na ihu.
Ihunta ne ya cika layin da k’arar ihunsu Harira da ke tasowa,wad’anda suka yi matuk’ar jigata saboda azabar duka da tiyagas,fuskokinsu sun motse kamar na b’era.
Da hanzari wad’annan samarin masu yin lido suka taso kusan su shida suka nufi gidan Saratu saboda sun ga shigar mahaukacin gidan,da k’yaleshi za su yi ya yagalgalata saboda ta zauna lek’e,domin takaicinsu duk d’agowar da za su yi sai su ga ta kafesu da idanu ko Riga babu a jikinta,to jin ihunta da Neman taimako shiyasa suka taso dan kar mahaukacin ya kasheta.
Suna niyyar shiga gidan sai ga Salisu ya b’ullo layin,Yayi mantuwar wasu kud’i ya dawo d’auka,tunda ya shigo layin kuma yake jin muryar Saratu na ihu,ga kuma mutane a k’ofar gidan,da hanzari ya k’ara so Dan ya zaci gobara ce ta tashi a gidan ta rutsa da Saratun,a gigice yake tambayar samarin abin da yake faruwa,nan kuwa d’aya daga cikinsu ya sanar da shi komai,tun daga zamansu a gefen layin suna yin lido har fitowar Saratu soro ta fara lek’e,har zuwan Mahaukacin layin da jibgar Saratu da ya fara har ta gudu ya bita cikin gidan.