BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

  Ya na gama saurara suka afka cikin gidan shi da samarin,Salisu Yayi mummunan gani,matarsa kwance tumb'ur daga ita sai wando wani k'ato na jibgarta ta na birgima da ihu,kaf halittunta a waje,tayi dama dama da kashi da fitsarin da ta saki don azaba,jikinta Yayi bird'in bird'in na duka da bulala,Salisu ya d'ora Hannu a ka saboda tsananin bak'inciki,shi kuwa da me zai kwatanta wannan b'acin ran a duniya?su Kansu samarin kauda kai suka yi cikin tsananin kunya.

Saratu kam ihu take da Neman ceto, da k’yar wad’annan samarin suka janye Mahaukacin suka fita da shi waje sai nishi yake,Saratu ta na jin ta daina jin duka a jikinta tayi wuf ta mik’e tana Neman gurin buya.

Salisu yana ganin ta mik’e shi ma yayi wuf ya mik’e hawaye na zubo masa na tsantsar takaici da bak’inciki,ji yake tamkar ya shak’e Saratu ya rabata da duniyar saboda muguwar tsanarta da yaji ta mamaye k’irjinsa,a gigice take gabad’anta,duka ya zautar da hankali ta, shiyasa ta nufo Salisu jikinta na rawa da makerkyata tana zunduma ihu tana shirin b’uya a bayansa,surutai kawai take zubowa cike da gigita,fad’i take.

“Wayyo Salisu na shiga uku na lalace,Dan Allah ka b’oyeni kar wannan mahaukacin ya dawo ya tarfa ni,innalillahi wa inna ilaihir raji’una yau naga bala’in duniya da na lahira,hasbunallahu wa ni’imal wakilu yau an min bugun sakwarar yarabawa,subuhannahi talatin da uku ,wal hamdu lillahi saba’in da takwas,wal lahu akubar tamanin da tara,wa subhanallahi bukratan wa asilan miliyan bakwai,la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimina,zalimina mahaukaci,zalimina mahaukaci,zalimina mahaukaci”

Haka Saratu ta dinga subad’ad’i tana dirango nonuwanta na rawa da tsalle tana nufar Salisu da takaici ya kusa shek’ashi lahira a tsaye,shi kansa ya san dukan Mahaukacin nan ya gigita Saratu ba kad’an ba,kamar wadda ta zauce haka take sakin maganganu tana kuka da tsalle.

Dab da zata iso wajensa ya d’aga Hannu yana dakatar da ita,cak! Ta tsaya jikinta na mugun mazari bakinta na rawa tace.

“To ,to ,to,na tsaya Malam Salisu,Alaramma bafaden Malam Munzali me almajirai,An gaisheka titib’iri masomin gardi,takawarka Lafiya na Saratu k’olon Gandujiyya,gaba salamun baya salamun jijjib’i na Saratu alherin Allah…….

” Ke! za ki nutsu ki min shiru ko sai nazo nan na k’ara cin kutumar Ubanki?
Salisu ya ambata cikin zazzare ido yana nuna ta da Hannu,sannan ya cigaba da magana a fusace yana kallon yadda take Sosa jikinta da nonuwanta kamar sabuwar kamun Hauka.

“Da alamun wannan Mahaukacin da ya dakeki ya goga miki Hauka kema,Dan Haka ni nan me hankali ne ba zan iya zama da Mahaukaciya Y’ar macukule ba,ki tsaya nan na cillo miki Riga da hijabi kisa ki ficemin daga gida na sakeki Saratu asararriya,ba don ina jin kunyar Malam ba ma da a haka yadda kike tsirara tunb’ur zan koraki,kinga za a tabbatar da kin kamu da haukan na ainihi,Jaka ,jahila, sak’andama ,wadda bata san ciwon kanta ba”

Yana fad’in hakan ya fad’a d’aki ya d’akko mata doguwar Riga da hijabi ya cillo mata,tana durk’ushe tana ta surutai marasa kai da gindi tana ihu,da yaga zata b’ata masa lokaci sai ya fad’a wani d’aki da yake ajiyar kayan gonarsa,daman duk damina yana zuwa gonarsa yayi noma,yayi dira dira idanuwansa suka fad’a kan gatari da fatanya,da hanzari ya kwaso su a Hannu ya fito ya tadda ita a kwance sai birgima take ta na ihu,ya daka mata muguwar tsawa,ta zabura ta mik’e tana kallonsa,ya d’aga gatarin yana nunata yace.

“Kin d’ibi kayanki kinsa kin fita ko sai na sassaraki?na rantse da sarkin da ke busamin numfashi idan baki b’acemin da gani ba yadda ake sara ice a faskarashi haka zan sassaraki na faskaraki na k’uk’k’ula da wayar kebir,k’ullin ashirin k’ullin goma a zo a siya ayi makamashin wuta dake tun a duniya,kafin aje lahira namanki ya zama abincin wutar jahan…….

Wuf!ta mik’e kafin ya k’arasa ta yayimi rigarta ta zumbula,mamakin Salisu take yi daman D’an daba ne,ko dai wiwi da sholisho da ermo ya zuzzuk’a?
Yana ganin ta zura hijabi ya kai mata fafara da fatanya,da gudu ta fita ya bita a baya ya nayi mata rakiya har bakin layin,samarin nan da ke waje bayan sun kad’a Mahaukacin suna zaune,nan da nan suka mik’e ganin Salisu ya biyo Saratu a guje,kawai sai suka kama dariya da tsalle suna ihun cewa.

” Rakata Salisu,Rakata Salisu,Rakata Salisu”

Salisu bai juyo ba sai da ya rakata har k’arshen layin sannan ya juyo cikin takaici ya koma Gidan,ya zauna ya zabga tagumi hawaye na sintiri a idanuwansa,a hankali ya zaro wayarsa ya danna lambar Malam Munzali mahaifin Saratu,Malam yana jin muryar Salisu ya tabbatar ba lafiya ba,aikuwa nan Salisu ya fara zayyane masa abin da ya faru yana kuka,sannan ya bawa Malam hak’uri a kan shi dai ya gaji da halin Saratu kuma ya saketa,ba zai iya jurar takaicinta ba.

Malam baiji zafin Salisu ba illa tausayinsa ma da yaji,ya dinga bashi hak’uri akan bak’incikin da Saratu ta dinga jaza masa,suka yi sallama zuciyar Malam kamar ta faso k’irjinsa,ya san yanzu Saratu zata iso gidan,shiyasa yayi shirin tarbarta da k’alubalen da zata fuskanta a gidan.

Saida ya tsinto almajirai ashirin masu tsananin k’azanta a cikin almajiransa,yace duk su fito da kayansu wad’anda suka yi daud’a an samu mai wanki za a wanke musu,aikuwa suka yi ta murna suka firfito dasu,kayan bak’ik’k’irin sai d’oyi da zarnin fitsari suke,D’an guntun kashi da fitsari duk sun mak’ale a jikin kayan tuli guda.

Saratu kam a k’asa ta isa gidansu tana ta kuka,duk inda tayi kallonta kawai akeyi kamar Mahaukaciya,tun a zaure taci karo da mahaifinta a tsaye ya goya hannuwa a bayansa yana tsumayin zuwanta,yana ganin ta yayi murmushi yace.

“Sannu da zuwa Saratu,madalla da zuwanki,shigo ki fara abin da ya kawoki”

Ya sata a gaba har zuwa cikin gidan,kuma yak’i sauraran duk maganar da zata fad’a masa,ya nuna mata tulin wankin almajirai yace.

“Fara da wannan Malama Saratu, idan kin kammala na tanadar miki wajen kwana cikin y’an uwanki tumakai”

Ya nuna mata turken awakai da yake kiwo yace.

“Kingansu can y’an uwanki ne domin irin halayyarsu kike yi,Dan haka cikinsu za ki shiga,akwai dusa da harawa idan kinji yunwa sune abincinki”

Yana fad’in hakan ya wuce ya barta a gun tana kuka,sannan ya hana mahaifiyarta kulata balle ta tausaya mata,tilas haka Saratu ta fara wankin Almajirai kamar za ta yi amai Dan tashin zuciya,ga rad’ad’in da jikinta ke mata,ga k’unar zuciya,haka ta yini tana wanki domin Malam yace idan ta sake magariba tayi bata kammala ba sai yasa gardawa sun d’aga masa ita ya zaneta ciki da bai ya k’arasa sauke mata kafad’ar ta.

Saratu dai taga ibtila’i a wannan ranar tamkar ta mutu ta bar duniyar haka take ji,nadama Mara amfani ta risketa a sanda lokaci ya k’ure mata.


A Gidan Amarya kam D’an sanda sai da ya casa su sosai ciki da bai,domin sai da ya karya Habiba a agara,Harira kam hannuwanta duk biyun sai da suka karye,Shafa’atu Yayi mata malolo a wuyanta,yayin da ya kusa saukewa Zahra’u kafad’arta ta hannun hagu,bayan ya gama jibgarsu sun shak’i tiyagas sai Yayi nufin wucewa dasu police station domin a k’ara ragargazarsu,da k’yar Hauwa ta lallab’a Idrees ya bawa ofisa hak’uri,sai dai ya rattaba musu babban horning akan duk wadda ta sake shigowa Gidan sai dai uwarta ta haifi wata,kuka ma kasawa suka yi daga k’arshe saboda masifar da suka shiga,tamkar Akuyoyi haka ya dinga binsu yana kad’asu waje da duka, ya watso su waje yana ta tunkud’a k’eyoyinsu,babu wadda ta kalli wata a cikinsu,kowacce burinta ta kai kanta gidanta,ita kam Habiba me karyayyiyar k’afa da Jan gindi ta kai kanta gida,ko wacce tana shiga gidanta ta zube a tsakar gida ta na maida numfashin wahala da azaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button