BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Idrees kam bayan ya sallami ofisa unguwar yabi ya samo lambobin mazajen matan BAHAGON LAYI,ya kira kowannen su akan idan ba damuwa yana da muhimmiyar magana dasu, idan da hali yana son kowanne ya baro gurin sana’arsa su had’u a bakin layin domin su tattauna.
Cikakken awa d’aya duk suka hallara,Idrees ya jasu soran gidansa ya shimfid’a tabarma suka zazzauna,bayan sun gaisa suna cike da mamakin kiran da Yayi musu,sai ga Salisu ma ya shigo fuskarsa d’auke da tashin hankali,ya nemi waje ya zauna suka gaisa,sannan Idrees yayi gyaran murya ya fara magana.
“Y’an uwana Assalamu alaikum,dalilin taramu anan muhimmiyar magana ce akan matayen mu dake zaune a wannan layi,duk da kasancewar ni bak’o ne a cikinku amma nayi matuk’ar mamakin ganin yadda kuka bari matanku suke rayuwa tamkar dabbobi ko akuyoyi,kun kasa d’aukar mataki a kansu kuna jin tsoronsu,bayan ku shugabanni ne a garesu kune sama dasu,ku Allah ya bawa wakilcin kula da tarbiyyar su,amma kun zama solob’iyo suna juyaku suna abin da suka ga dama kun kasa d’aukar mataki,zuwan mata ta unguwar nan har sun fara hure mata kunne zasu b’arar mata da tarbiyyar da ta zo da ita,Dan haka ni ba zan jure wulak’ancinsu ba,shiyasa a yau na d’auki matakin da ko ance su k’ara dosar gidana wallahi sai sun ruga a guje”
Daga nan ya cigaba da basu labarin dukkan abin da ya faru har dukan da suka sha a hannun D’an sanda da tiyagas,yayi matuk’ar mamaki da yadda yaga mazan suna murna da dariya akan abin da aka yiwa matansu,K’asimun Zahra’u ne kawai yaji ba dad’i sosai,duk da dai matarsa ce tayi silar kawo maganin mallakar da ya fallasa komai,Shi Babalalo ma sai a lokacin yaji ashe Habiba aljanun k’arya tayi sanda ta ciji malam Arabi a cibiya,Kamilu ne yake fad’a masaa lokacin, wai Sahafa’atu ce ta bashi labarin hakan,Haka nan K’asimu ya fad’awa Sunusi cewa Harira Asiri take masa shiyasa baya iya tab’uka komai take gallaza masa,wai Zahra’u ce ta fad’a masa,nan da nan tone tone ya tashi,kowa yana tona asirin matar kowa,bak’inciki kamar ya kashesu,nan Sunusi da Babalalo suka ce wallahi aure za su yi sun gaji da wannan wahalalliyar rayuwar,nan Kamilu ke cewa Sunusi ai Amina k’anwarsa tana sonsa,tana son ta aureshi ko Dan ta gyarawa Harira zama da tarbiyya,nan da nan Sunusi ya amince yace shima yana son Amina.
Shi kuma Babalalo yace akwai d'iyar K'anwar babarsa da zai aura nan da wata uku,domin gininsa yayi nisa anyi rufi flasta da fenti kawai ya rage,za su tashi daga layin shi da Habiban su tare da galleliyar Amaryarsa.
K’asimu ma yace tashi zaiyi daga layin ya nemawa Zahra’u wani matsugunin me kyau,kyakkyawar unguwa wadda babu irin su Harira a cikinta,domin duk ita ce ummul aba’isin lalata musu matansu.
Shi kam Sunusi cewa yayi Gidan iyayensa zai maida Harira da zama,daman akwai wani d’aki d’aya na gadon Babansa a ciki zai sakata ta k’arata,in yaso yasa Amina a wannan Gidan su more amarcinsu.
Kamilu kam yace zai cigaba da zama a BAHAGON LAYI saboda bashi da halin tashi ya kama wani Gidan Haya,sai dai zai kula da tarbiyyar Shafa’atu ya taka mata birki,tilas ta gyara halayenta,duk da dai ya san yanzu dukan D’an sanda ya firgitasu.
Sai da kowa ya gama maganarsa sannan Salisu ya tofa tasa,ya basu labarin abin da yazo ya tarar tsakanin Saratu da Mahaukaci,Abu biyu ya had’e musu,wato takaici da dariya,nan suka rok’i Salisu yayi hak’uri ya dawo da Saratu,amma ya kafe wallahi sai tayi wata uku a gida malam ya dila ta sannan,kuma shi ma da amaryarsa zai tare,Dan duk iskancin mace da an mata kishiya take nutsuwa ta kama kanta.
Bayan sun gama tattaunawa suka yi addu’a taro ya tashi kowa ya nufi gidansa,kowa kuma ya tadda matarsa cikin tsananin azabar dukan da suka sha.
Tsawon kwanaki kafin kowacce ta warke daga raunukan da suka samu,dukkansu sunyi laushi tamkar damammiyar fulawa,kowacce nadama da hankali sun shigeta,dukkansu suka gyara alak’arsu da mazajensu babu fitsara da rashin kunya,babu yawo, babu rashin mutunci da akuyancin da suke yi,amma fa wad’anda suka samu d’ambar aure sun ce babu fashi.
Tuni Zahra’u da K’asimu suka bar layin zuwa wata unguwar suka tare.
Ragowar da suke zaune a layin suka kama kansu babu wadda take fita balle ta lek’a Gidan wata,Gidan Amarya Hauwa kuwa ko shashin Gidan basa kalla,idan suka tuna azabar da suka sha a hannun D’an sanda har runtse idanu suke,basa fatan su kuma cin karo da D’an sanda a rayuwar su.
Hahaha(D’AN SANDA ABOKIN KOWA).
K’ARSHEN WANNAN LITTAFI KENAN NA BAHAGON LAYI,ABIN DA NA FAD’A DAI DAI ALLAH YA BANI LADA,ABIN DA NAYI KUSKURE ALLAH YA GAFARTA MIN,NAGODE MASOYANA DA JIMIRIN BINA DOMIN KARANTA RUBUTUNA,YANZU DAI NA FITA KO BA SABULU NA WANKE MUKU ZUCIYA A BISA KUKAN DA NAKE SAKA KU CIKIN LITATTAFAINA,SAI KUMA MUN SAKE SADUWA A CIKIN SABON LITTAFINA WANDA NAKE FATAN YA ZARCE DUKA LITATTAFAINA NA BAYA,MA’ASSALAM????????????????
Bayan comment d’in da za ku yi a wannan shafin ina so ku fad’a min abubuwan da kuka k’aru dasu a littafin,da kuma wane waje ne yafi birgeku?wane waje ne yafi Baku dariya?wane waje ne yafi Baku takaici ko haushi?waye jaruminku ko jarumarku a labarin?wane muhimmin sak’o ku ka d’auka a labarin?Ga wad’anda basa group d’ina ko basa cikin groups d’in da nake zasu iya aikamin sak’onsu ta kan watsapp ta lambata kamar haka:08080049548
BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️