BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yawwa yau me zamu dafa ne?
Cewar Habiba tana Neman gun zama.

Shafa’atu tace.
” Kawai muyi D’anmalele,Dan sha’awar cin manja da yaji nake “

Zahra’u ta matsa jikin Harira da ta damk’i kanta ta fara tsagar kitso sannan tace.

“Aikuwa mun dad’e ba muyi ba,tun randa akayi har garin zubawa ya k’ona Saratu a k’afa,don Allah yau a yi mu wawwarb’e shi”

“Wai ina Saratun ma yau shiru bata shigo ba?
Harira ta tambaya tana kallonsu.

Habiba tace.
” Da zan kullo gidana na ganta tana lek’en da ta saba,tana hangoni ta yafitoni,shine da naje take gayamin wai Salisu ne baya jin dad’i yana kwance yak’i fita ba zata samu damar fitowa ba,yanzu ma da take lek’e bacci ne ya kwasheshi,amma wai duk abin da muka dafa akai mata nata rabon”

“Allah sarki Saratu yau ba sakewa,yadda rumfarta take tsukakkiya ga Salisu jibgege yayi shame shame ya za ta yi?wallahi idan nice duk wucewar da zanyi sai na dai daici muk’amuk’inka zan take a matsayin ban gani ba,ko in samu zundumemen kumatun nan naka na bi ta kai kunga ya sace”
Inji Harira da ke wa Zahra’u kitso,
Har ta kammala na gaban saboda tana da sauri,duk suka yi dariya yayin da Harirar ta fizgo kafad’ar Zahra’u tana cewa.

“Sai ki juyo mu k’arasa na bayan Malama”

Ta juyo tana tsaki,sannan tace.

“Harira ina jaddada miki kar ki matse min kai wallahi”

“Ke dalla Malama sai na matse d’in,k’wandalarki ba biyana kike ba sai wani sharad’i kike kafa min,na rantse da Allah kika isheni ba zan k’arasa ba sai dai ki kwana da rabin kai a tsefe,in yaso K’asimu ya k’arasa miki,Don ba wahala zai masa ba tunda har ya k’ware a kid’an k’warya da d’uwawu”

Zahra’u ta yi tsaki tana kife kanta kan cinyar Harira,da wani mugun sauri ta d’ago tana toshe hancinta,ta harari Harira tace.

“Kinji jiki wallahi,baki da aiki sai tusa,har wani mak’ak’i take yi kamar nayi amai”

Duk suka kwashe da dariya,yayin da Harira ke rantsuwar wallahi ba tusa tayi ba.

Zahra’u tace.

“To wai idan ba tusa kika yi ba me yake wari haka a tsakanin cinyoyinki?kinji warin kuwa Harira?wani gumus yadda kika san ana kwasar turai”

Habiba tace.
“Kuka sani ko headquarter ne yake hamami da samami?ai kun san Harira ba ta damu da wajen ba bata gyarashi,shiyasa duk yaron da ta kifawa kai a cinyarta yaita mutsu mutsu,Ashe wari ke addabarsu,gaskiya Harira ki canja hali duk kud’in da kike samu na kitso ai ko d’an miski na d’ari biyar kya siya ki dinga tsaftace gurin,ba dad’i Sunusi ya kai kansa ko bakinsa gun yaci karo da d’oyi”

“Harira ta tab’e baki tana hura hanci,cikin basarwa ta share maganar ba tare da ta tanka ba,kawai sai ta mik’e tana sababi tana hararar Zahra’u .

” Kin San Allah,ba zan k’arasa miki ba,tunda iskanci ne abin naki tafi Habiba ko K’asimu su yi miki,wadda taga dama ta tashi muje muyo cefanen,tunda akwai ragowar tsaki ba sai mun siyo ba,wadda take da man ja ta d’akko a gidanta,ni dai ina da yaji,in yaso muje gun D’an Damaso mu siyo tumatur da albasa kawai”

Duk suka mik’e,Zahra’u ta d’aure kan ta da ba a kammala kitsewa ba,Shafa’atu ta fara magana da cewa.

“Yadda rana ta take yanzu gun D’an Damaso a cike yake da yara wallahi,ko kawai muje titi mu siyo?

Habiba ta zaro idanu tace.
” Tafd’ijam! wallahi ba zamu titi ba,kin fa san Babalalo yana shagonsa na aski,idan ya ganni a titi ban tambayeshi ba ai na banu,kawai muje gun D’an Damason,kayansa ma yafi arha da kyau,idan muka ga da cikowa ba sai muyi abin da aka saba ba”
Inji Habiba kenan tana zura hijabin ta da ta rataye a kan igiyar shanyar Harira.

Tana dire maganarta Zahra’u ta k’yalk’yale da dariya tace.

“Aikuwa dai gara ayi abin da aka saba,amma Dan Allah yau Ku barni ni zan mintsini D’an Damaso ko nayi masa cakulkuli,nima dai yau naji abin da kuke ji idan kun mintsineshi”

Duk suka sa takalmansu suka yo hanyar soro suna dariya,Shafa’atu tace da Zahra’u.

“Ke wallahi D’an Damaso yanzu ya kile baya bari a mintsineshi,kina kai mai mintsini ko cakulkuli zai sa gwiwar Hannunsa ya k’ule ki,Dan haka in kika mintsineshi ya kai miki mangari tsaf zai zubar miki da hak’oran gaba,me zaki gayawa K’asimu?wallahi kuma cas duk soyayyar da kuke da K’asimu kina ganin kin mallakeshi zai iya k’aro aure,Dan banga ta yadda zai zauna da ke ba baki duk wawulo”

Suka kuma kwashewa da dariya kamar mahaukata sabon kamu tsabar shakiyancin da suke yi,Zahra’u ta kaiwa Shafa duka tana cewa .

“Amma Allah ya isa tsakanina dake Shafa,insha Allahu kafin a k’aro min amarya ke Kamilu zai fara yiwa amarya”.

Dai dai lokacin suka fito waje, kowacce ta kalli gidanta da ke kulle,sannan suka dubi gidan Saratu da yake a bud’e an d’an sakayo k’ofar,sai ragowar d’aya gidan da ba a tare ba shi ma a kulle,amma ance sati mai zuwa za a kawo wata amarya ciki,shiyasa suke ta d’okin zuwanta,a ganinsu zasu k’ara yawa su zama su shida.

  Rukunin gidajen a layin guda shida ne,na wani me kud'i ne wai shi Alhaji Ibraheem,ya kan gida gidaje ya saka y'an haya,gidajen basu da girma sosai,duk da dai suna da tsayi,kuma guda shida ne a jere reras,Harira da mijinta Sunusi na d'aya,Habiba da mijinta Babalalo na d'aya,Zahra'u da Mijinta K'asimu na d'aya,Shafa'atu da mijinta Kamilu na d'aya,sai Saratu da mijinta Salisu na d'aya,sai kuma ragowar d'ayan da wani satin za a tare a cikinsa.

Dukkaninsu babu wadda ta cika shekara d’aya a gidan miji,illa Harira da take a shekara ta biyu,shiyasa Duk unguwar anfi saninta akan sauran,musamman da ya kasance tana kitso,kuma kusan duk y’an unguwar ita ce take musu kitso,gidanta ya kasance wajen dabdalar mata da gulmace gulmace,haka nan Harira bata tab’a haihuwa ba,su ma d’in Shafa’atu da Zahra’u ne kawai masu k’aramin ciki.

 An sawa layinsu suna *BAHAGON LAYI* ne saboda yadda layin nasu yayi k'aurin suna wajen tattara mata marasa kamun kai da shashanci,tamkar ba matan aure ba,duk inda kuma ka Shiga a unguwar zaka tarar ana zund'ensu da maganarsu akan rashin kamun Kansu tamkar wasu mahaukata ko marasa ilimi......!

 Da gudu Samiha ta shiga gidansu ta cillar da robar man kitson da ke hannunta, tayi bakin rariya ta tsuguna ta fara shek'o wani irin amai kamar hanjin cikinta zai fito.

Ummanta da ke tsintar shinkafa tayi fatali da farantin ta mik’e a zabure ta nufi y’arta kamar ta kifa….!

Ya kuka ji Labarin fan’s?ya bambanta da salon Labaran da nake kawo muku ko?to daman nayi shirin wanke muku zukata ne saboda kukan da kukeyi a litattafaina,da yardar Allah wannan ba za ku yi kuka ba sai dariya,daman haka rayuwar take,tab’a kid’i tab’a karatu,ku dai ku sank’amo sharhinku hakan zai sa na gane kuna son labarin kuma na cigaba ????????????????

  *Akwai Littafina me suna CIN AMANAR RUHI,Amma na kud'i ne 200,ga mai buk'ata zai Iya tuntub'ata ta lambata akwai completed document yanzu haka,Labarin da yake d'auke dashi Baku tab'a cin karo da irinsaba,da zarar kun biya kun karanta zaku gane hakan,ga lambar da zaku nema kamar haka* 08080049548.

 *sannan akwai kaya irinsu laces,atamfa ,shadda,material,takalma da jakunkuna,dogayen riguna,duk zaku same su akan farashi mai sauk'i,siyan d'aya ko sari,kuma muna aikawa ko ina a fad'in tarayyar Nigeria insha Allah,nagode sai na jiku akan numbata kamar haka ta watsapp* 08080049548.

BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️
[7/24, 10:53] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????

????️ BAHAGON LAYI ????️

    (D'AN DAMASO)

TARE DA ALK’ALAMIN✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

MARUBUCIYAR????

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

     *DA KUMA*????

BAHAGON LAYI

BABI NA UKU DA NA HUD’U

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

SADAUKARWA

GAREKI HAFSAT GARKUWA????HAK’IK’A NAJI DAD’IN COMMENTS D’INKI????KUMA HARIRA TACE NA FAD’A MIKI TANA JIRANKI KIZO TAYI MIKI KITSO????????????????

Ta tsuguna gefen Samihar ta d’agota bayan ta kammala aman,Hankalinta a tashe ta dubi d’iyarta ta da ta galabaita,sai gumi take yi ga hannunwanta dafe da cikinta tana yamutsa fuska hawaye na gangarowa a idanuwanta,Buta ta jawo ta tsiyayi ruwan ciki ta d’auraye wa Samihar bakinta,sannan ta kora aman zuwa rariya,daga nan taja ta zuwa kan tabarmar da ke shimfid’e a tsakar gidan suka zauna tana ta zabga mata sannu,da k’yar Samiha ta amsa sannan ta zame kan cinyar Ummanta ta kwanta tana nishi.

Umma ta juyo da fuskarta tana kallonta,cikin damuwa tace.

“Samiha lafiyarki kuwa?me ya same ki kika yi amai?ko wani Abu kika ci a gidan kitson?

Hawaye ya kuma gangarowa Samiha,tasa hannuwanta tana gogewa,cikin shesshek’a tace.

” Gaskiya Umma ni ba zan kuma zuwa gidan Harira kitso ba daga yau,gara na koma gidan Suwaiba ta cigaba da yi min”

Umman ta d’an zaro idanuwa sannan ta girgiza kai tace.

“Ba zai yiwu ba Samiha,kina ganin yadda kanki ya lalace a hannun Suwaiba fa,amma tunda Harira ta fara yi miki kitso kanki ya fara kyau yana tsawo yana gyaruwa,duk wani gunji da kike dashi Harira kame shi take yi bata barinsa,yanzu dubi fa….
Ta zame d’ankwalin kan Samihar tana kallon kitson,Sannan ta cigaba da magana da cewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button