BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

” Kalli yadda kanki yayi kyau Sosai ko wane gunji ta shigar dashi,sunkuya naga k’eyar taki”ta duk’ar da kan Samihar tana duba k’eyar.
Da sauri ta d’ago cikin tashin hankali ganin wani zabgegen shati a k’eyar Samihar yayi bala’in ja ,k’eyar har ta kumbura,Hannu ta kai gurin tana shafawa yayin da Samiha tayi zillo tana fad’in.
“Wash!Umma dena tab’awa da zafi wallahi”

“Ke Samiha me ya cijeki haka a k’eyarki?kinga yadda gun yayi ja ya d’ad’e kuwa?
Umma ta tambayeta tana zare idanu.

Samiha ta fashe da kuka,cikin kukan ta fara magana.

” Wallahi Umma shiyasa nace miki na dena zuwa kitso gidan Harira,Ita ce fa da ta gama min kitso ta saici k’eyata ta lafta min d’ad’o,Allah Umma Harira muguwa ce “

“Harira ta dakeki?to me kika yi mata haka Samiha?
Umma ta tambaya cike da mamaki da al’ajabi.

Samiha tayi shiru tana kuka tak’i magana,har sai da Umma ta daka mata tsawa tace.

” Za kiyi magana ko sai na sharara miki mari?nace me kika yi mata ta dakeki?rashin kunya ko fitsara kika yi mata ?Dan na San haka kawai ba zata kamaki ta jibga ba”

Samiha ta fara rantsuwa da cewa.

“Na rantse da Allah Umma babu abin da nayi mata,matse min kaina take a cinyarta shine nake mutsu mutsu,wallahi Umma haka tayi ta zuba min rank’washi a tsakiyar kaina tana zagina,kuma Umma abin da yasa nake mutsu mutsu da na sunkuyar da kaina a kan cinyarta wani wari da d’oyi ne yake da mu na,cikina yayi ta murd’awa yana ciwo,shine idan na d’ago sai ta dakeni ko ta rank’washeni,yanzu haka bakiji yadda cikina ke ciwo ba Umma,sai da na d’an yi aman nan naji dad’i fa”

Umma tayi kasak’e tana sauraron Samiha,ta tabbatar gaskiya ta fad’a ba k’arya ba,ba yau ta fara jin zancen wari da d’oyin da mutane ke shak’a gun Harira ba da zarar tazo yi musu kitso,taji zancen a gurare da dama,to wai shin wane irin wari ne haka?Sannan Dan mugunta ta dinga zaluntar yara tana dukansu kamar bayinta,tabbas idan tana yiwa wasu sun hak’ura ita kam ba zata jura ba,ba zata yarda ta dinga cutar da d’iyarta tana ji tana gani ba,wallahi sai ta d’auki mataki akan dukan da Harirar tayi wa Samiha.

   Janyo Samihar tayi tana rarrashinta da share mata Hawaye,Sannan tace mata.

“Kiyi shiru Samiha,insha Allahu daga yau kin dena zuwa kitso gun Harira,kuma ba zan k’yaleta ba sai na bibiyi kadin dukan da tayi miki,domin ban haifi jaka ba,haka nan ke d’in ba baiwa bace kina da gatanki kuma ina sonki,Dan haka kiyi shiru da bakinki za ki ga matakin da zan d’auka,yanzu tashi muje d’aki in shafa miki Robb a k’eyarki ko zata warware,Dan tabbas zata iya sakar miki kaluluwa ko wuyanki ya k’andare”

Samiha ta mik’e suka nufi d’aki ita da Ummanta,zuciyarta k’al saboda an ce tadena zuwa kitso gun Harira,Ummanta ta lalubo Robb ta mulka mata a k’eyarta,Samiha ta dinga Hawaye saboda zafin da take ji,da ta gama shafa mata tace ta kwanta ta huta,Samiha tabi lafiyar katifa tana runtse idanuwanta,kanta ciwo yake saboda azabar rank’washin da ta sha,ga k’eya duk ta d’aure tasha d’ad’o,a zuciyarta Allah ya isa kawai take jawa Harira.

Umma kam tsakar gida ta koma tana tattare shinkafar da ta b’arar,sai faman sababi take tana tsinewa Harira,Haka nan Zuciyarta na tunanin matakin da zata d’auka kan Harirar.


      Suna isa gun D'an Damaso me kayan miya suka tarar da layi kamar yadda suka yi hasashe,amma ga mamakinsu sai suka ga yayi wata k'ofa ta langa langa gajera ya katange tsakaninsa da mutane,illa wata b'ula da ya bari ta nan mutane ke mik'a masa kud'i yana basu abin da suka zo siya,wato D'an Damaso ya gaji da mintsini da cakulkulin da yake sha gun mutane shiyasa ya d'auki mataki,a baya idan cikowa tayi yawa kowa yana son a sallameshi haka za a yi ta mintsininsa ana hayagaga da kiran sunansa akan ya sallamesu,da ya fuskanci cutarsa suke yi kawai sai ya fara d'aukar matakin ramuwa yana k'ular duk Wanda ya mintsineshi da gwiwar hannunsa,to a yau kuma sai ya fidda sabon salon katange kansa,don ya tsira daga muguntar mutane.

Suna tsaye a gefe suna ta shakiyancin su,kowa zai wuce sai ya kallesu yayi Allah wadarai da su,ganin D’an Damaso yak’i kula su yana ta sallamar yara sai Habiba ta matsa tana ta ture yaran jama’a ,sannan ta d’aga murya kamar ba matar aure ba tana yiwa D’an Damaso masifa.

“Tun d’azu muka zo nan amma ka share mu sai sallamar wasu kake, idan ba zaka siyar mana ba kawai mu k’ara gaba”

Ya d’ago kansa ya dubeta duk ya had’a uban gumi fuska ta cakud’e,daman tubarkalla gashi bak’ik’k’irin har shuni yake yi,ya girgiza kai yace.

“Duk wajen nan kune k’arshen zuwa,ya kamata Ku bari a sallami wad’anda suka riga Ku zuwa domin ayi adalci,amma tunda ku y’an wutar ciki ne fad’i abin da za a Baku in sallameku Ku tafi”

Haushi ya kama Habiba,wato ma sune y’an wutar ciki,aikuwa tilas su fanshe wannan rainin hankalin da yayi musu,shiyasa cikin izgili ta murgud’a baki tace.

“Tambaya kake yi abinda zaka bamu?to me irin sunanka zaka bamu”

Yayi shiru yana tunanin abin da take nufi,da ya kasa ganowa sai ya dubeta yace.

“Me irin sunana kuma?daman a cikin kayan miya akwai me suna Jabiru ne?

Su Zahra’u da suka matso suka kwashe da dariya suna tafawa,Sannan Harira ta bud’i baki cikin shakiyanci tace.

” Au wai Daman sunanka Jabiru?ai mu billlahillazi da Tattasai D’an Damaso muka sanka,kuma da haka muke kiranka”

Jabiru me kayan miya yaji ya muzanta sosai,saboda dariyar da yaran gun suka kwashe da ita,amma babu yadda zaiyi haka ya gyad’a kai yana dubansu yace.

“Dan kanku!Aniyarku ta biku!na nawa zan Baku?gara na baku ku kauce min da gani?

Shafa’atu tayi masa gwalo tace.

” Mun fasa siyan me Sunan naka, bamu Tumatur da Albasa kawai na Hamsin”

Ya zuba musu ya basu,suka bashi kud’in suna ta yi masa tsiya da shakiyanci kala kala,wai ya rage ciki ,a cikin kud’in da yake samu ya siyi man bleaching ya goga,ko ya rage shunin da yake “

Ransa ya kuma b’aci,har bai San lokacin da ya saki tsaki ya tanka musu ba.

“Allah ya tsareni da shafe shafe,ko an gaya muku ni d’an Daudu ne da zanyi bilitin?shashashun mata marasa hankali,wallahi kunyi asara,mazajenku basu yi sa’ar aure ba,domin gara su Auri akuyoyi su San abin da suka aura,tumakai kawai da basu San darajar aure ba”

Gwalo suka yi masa suna tuntsira dariya,Habiba na cewa.

“Can da yawarka,wahalar kace,matsalar kace,can ta matse maka a matse Matsin bak’ar Hammatarka,ka taimaki kanka ka shafa man bilitin ko ka dawo asalin sunanka na D’an Damaso,kaga dai shi tattasai D’an Damaso ja ne,kai kuwa bak’ik’k’irin kake tamkar sabulun nan me suna Baba da d’oyi”

Haka suka dinga yiwa Jabiru wulak’anci har suka tafi,suka barshi yana cizon yatsa kamar yayi kuka,ya d’auki alwashin tilas ya kai k’ararsu wajen mazajensu domin ayi masa tsakani dasu su dena zuwa wajensa siyayya,domin duk lokacin da suka zo sai sun wulak’antashi zuciyarsa tayi bak’i,to ina dalilin haka kuwa?tilas ya d’auki mataki ya gaji da jurar wulak’ancin Matan da bashi da wani had’i dasu.


 Har suka isa gida suna dariya da zancen Jabiru D'an Damaso,suna b'ullawa layinsu suka hango Sunusi k'ofar gidan Saratu a tsaye shi da Salisu suna magana,Shafa'atu ta tab'o Harira tana cewa.

“Saita sahunki ga Mijinki can,shi kuwa me ya dawo dashi da tsakar ranar nan?

Harira ta tab’e baki tana hararar bayansa tace.

” Oho masa magulmaci,duk maza suna gun Neman abinci amma shi da tsakar rana ya kamo hanya ya tawo,kuma ni na san abin da ya dawo dashi ,kuma wallahi yanda ya dawo haka zai koma ba zan barshi yayi ba”

“Wai kina nufin har yanzu Sunusi bai canja halinsa ba?duk jarabar da kike masa?
Cewar Habiba tana kallon Harirar.

Harira tayi tsaki tace.

” Ta ina zai canja?yana nan yana halinsa na tsolantaka,Ku dubi Nisan wajen da yake aikin bulo, amma ya gwammace ya tawo gida a k’afa yayi kashi idan ya matsoshi ,akan ya biya naira talatin ya Shiga gidan wanka yayi,to wallahi yau ko zai yi a wando ba zai min kashi a Masai ba”

Suka tuntsire da dariya a lokacin da suka iso k’ofar gidan Harirar,da sauri Sunusi ya bar Salisu ya nufo su yana washe Baki kamar wani dolo,Salisu ya kad’a kai ya shige gidansa yana tsaki,ba k’aramar tsana yayi wa matan ba saboda a ganinsa su suka lalata masa tarbiyyar matarsa,burinsa bai wuce ya mallaki gidan Kansa ya tashi daga wannan bahagon Layin ba,yanzu ma ya fito waje ne Don yasha iska saboda zafin da Saratu ta had’a masa, shine har Sunusi yazo ya tadda shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button