BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Sunusi kam yana isowa gabansu da Sauri Harira ta d’aga masa Hannu ta dakatar dashi daga subad’ad’in da ya fara yana dariya,fad’i yake.

“Iyen ba!kaga Harirata da k’awayenta,in ce ko daga wajen cefanen ake?yau kuma wane dabgen zamu sharb’a ne?

Wata shegiyar Harara ta galla masa,ta buga mugun tsaki ta bud’e gidan ta kalli su Habiba tace.

” Ku shiga Ku fara k’ok’arin d’oramana girkin ina zuwa”
Suka shige suna wa Sunusi dariya ganin yadda yayi sakato a gaban Harira,suna shigewa ta waiwayo tana kallonsa ganin k’afafuwansa na rawa ta tabbatar kashin ya matseshi sosai ne,aikuwa kallon raini tayi masa sannan tace.

“To fara sarkin kashi!daga ganin wannan yak’en da kake yi kashi kake ji,kuma na rantse da Allah ba dai a gidannan ba Kasan Inda dare yayi maka,kaga dai inada bak’i yau dutina ne a gidana za a yi girki,ba zan lamunce ka Shiga ka cika musu ciki da d’oyi ba,domin kaf duniya banga me warin kashinka ba Sunusi,hanzarta ka bar nan kar ka sakar min a wando k’uda ya ishemu”

Sunusi ya fara magiya yana rok’onta akan ta taimaka ta barshi ya Shiga domin a matse yake, amma fir Harira tak’i amincewa,daga k’arshe ma shigewa gidan tayi,ya bita a baya yana rok’onta a sanda ta garo k’ofar zata danna sakata,ba zato babu tsamanni k’yauren ya daki goshin Sunusi ya koma da baya yayi fad’uwar y’an bori….!

Pls
Comments
Share

kada Ku manta akwai littafin CIN AMANAR RUHI complete document akan 200 kacal,me buk’ata ya tuntub’eni ta lambata,08080049548.Sannan akwai laces ,atamfa,shadda,takalma da jakunkuna da materials,dogayen riguna,duk akan farashi me Ragusa,siyan data ko sari,sai na jiku masoyana

BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️
[7/25, 10:14] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????

????️ BAHAGON LAYI ????️

    (BABA DA DIDDIGA)

TARE DA ALK’ALAMIN✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

MARUBUCIYAR????

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

     *DA KUMA*????

BAHAGON LAYI

BABI NA BIYAR DA NA SHIDA

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

SADAUKARWA GA????

HUSSAINA D’AN LARABAWA????,SISINA Y’AR UWA RABIN JIKINA????,BARI NA TUNO BAYA LOKACIN YARINTA????(BABA DA DIDDIGA?)????????????

Kamar yayi kuka saboda takaici,Sosai ya bugu har k’ugunsa sai da ya amsa,wai shi da gidansa shine me biyan kud’in haya amma bashi da katab’us,saboda tsabar bala’i da masifa matarsa ma bai isa ya sarrafata yadda yake so ba,ya rasa ina zai sa kansa da masifar Harira.

 Haka ya daddafa ya mik'e domin ya nemi gidan wanka ya gabatar da uzurinsa,Dan tabbas in yayi sake zai iya sakin kashin a wando saboda matsarsa da yayi,Wanda hakan abin kunya ne a gareshi.

Shi kam Salisu yana shiga gidansa yayi ta sakin tsaki yana harare harare,Saratu da ke zaune a tsakar gida da d’aurin k’irji ta juyo tana kallonsa,ganin yaja kujera Y’ar tsuguno ya zauna bai mata magana ba ita ma sai ta share shi,can taji sai sakin tsaki yake yi a jajjere,hakan yasa ta b’ata rai ta kalleshi tana danna masa Harara tace.

“Kayi a hankali dai Salisu,domin duk mutumin da ya cika tsaki to tsaka yake zama,haba! daga fitar ka sai ka dawo ka isheni da tsaki a gida,in wani abun ne ya b’ata maka rai ba sai kaji da lalurarka ba,haka kawai sai kazo ka tasani gaba ka addabeni da tsaki akan me?,Bari kaji na fito maka a mutum,Wallahi ni gabad’aya Salisu bana k’aunar zamanka a gida domin kana takuramin wallahi,kana Shiga rayuwata,kayi min wani shirim a gida ina son shan iska amma ka tare ko ina,wallahi daga fitarka ba kaji inda naga filin gurin ba,amma kana dawowa duk ka babbake ko ina,kai Allah ya rabamu da k’iba irin taka Salisu,Abu sai kace Sunduk’i”

Yayi wani irin murmushi na takaici, yayi mata banzan kallo sannan yace.

“Ai ke kin sani babu abin da zan fita na ci karo da shi ya b’atamin rai irin Akuyoyin k’awayenki,mata marasa kamun kai da nutsuwa,Lafiya k’alau na auroki a matsayinki na Y’ar gidan malamai Saratu,amma zuwanki layin nan kin had’u dasu kuna shashanci da tumasanci,kina Y’ar Malam amma kin k’i halin Malam,ga wata tsinanniyar d’abi’a da kika kwasa ta lek’e,Haka Shekaranjiya Najibu me shayi ya kawo min k’ararki,wai kullum in zai shige ta layin nan kina mak’ale jikin k’ofa da d’aurin k’irji kina lek’e,duk Wanda zai shige sai ya kalleki kin kalleshi,wallahi Saratu ina nan ina addu’a Allah yabi min hakkina na zubar min da mutunci da kike,ina son d’aukar mataki a kanki amma kunyar malam ta hanani yin hakan,amma ki tabbatar idan baki sauya hali ba ina dab da zartar da hukunci mummuna a gareki,maganar k’iba da kike yi to ai ni nagodewa Allah,tunda k’ibata ba ta sa na jibge har bana iya tafiya ba,wasu suna nan a jab’e ko yunk’urawa za su yi sai an d’aga su,sann…

Wani irin ihu da Saratu ta zuba shine ya dakatar da Salisu daga maganarsa,ta mik’e a gigice tana d’ora Hannu a ka har d’aurin k’irjinta na shirin kwancewa,cikin kwaroroto kamar wadda aka yanka ta fara magana.

“Lallai Salisu baka da mutunci,mahaifiyata kake yadawa magana kenan saboda Allah ya jarrabeta da k’iba har ciwon k’afa yana hanata mik’ewa?lallai ka tsokano masifa tunda wulak’ancin ka ya had’o da iyayena,K’awaye na kuma da kake kiransu tumakai kai me za a kiraka dashi ?Bunsuru?Nace Bunsuru za a kiraka dashi ko?D’an rainin hankali kawai,kai ba ka san zaman hak’uri kawai nake da kai ba?abubuwan da suka sark’afeni na rashin jin dad’in zama da kai sun yawaita a gareni,wallahi Salisu ko munsharinka me kama da kukan jaki aka bar mutum dashi ya Shiga uku,shi kuma Najibu me shayi munafukin Allah ta’ala,domin bashi da maraba da Malam Tsalha na (Dad’in kowa)a fagen gulma da munafurci,Wallahi idan ya sake ya k’ara kawo maka gulmata har teburin shayinsa zanje nai masa b’arna,ba abin mamaki bane ya ganni da rusheshiyar tab’arya naje na farfasa k’wan da yake toyawa mutane,daga k’arshe in Sauke masa kafad’ar hannun hagu, Kai kuma Salisu m zuba ni da kai shege ka FASA,Wallahi idan ba ka fasa cin zarafina ba ba zan fasa cin mutuncinka a gidannan ba”

Mad’aukakin b’acin rai ya ruftowa Salisu,wai matarsa ta sunnah ita ce tsaye a gabansa tana fad’amasa mugayen kalamai,cikin tsantsar b’acin rai ya mik’e tsaye yana nuna k’irjinsa yace.

“Saratu ni kike fad’awa wad’annan kalaman?

Ta k’ara hayayyak’o masa.

” Na fad’a d’in,yo tsoranka zanji da ba zan fad’aba?Ko Dan ka ganka rusheshe zubin samudawan farko?Yanzu da ka tashi kana zare min mici micin idanuwanka duka na zaka yi ne?to idan ka fasa ka raina Iya me ido d’aya”

Wayyo Allah!wani kukan kura Salisu yayi ya nufi Saratu jin ta ambato mahaifiyarsa,tana niyyar zillewa ya d’aga tuk’ek’en hannunsa ya sakar mata gitta a gefen wuyanta,kan kace me Saratu ta baje k’asa war was a k’asa tana juya wuya, muk’amuk’inta ya kumbura,kukan ma yak’i zuwa saboda yadda dukan ya gigita k’wak’walwarta,Dan ji tayi tamkar bulo inci Tara Salisu ya muk’a mata.

Salisu kam yana cika aiki ko kallonta bai k’ara ba ya tsallaketa ya fice daga gidan,domin tamkar kumurcin maciji yake kallon fuskarta.


Su Harira kuwa ana can ana girka d’an malele suna zuba hauka,babu wadda ta damu ta tashi tayi sallah a cikinsu,Dan bayan sun gama ma hira da gulmace gulmace suka zauna yi,Har Saratu suka zubawa amma aka rasa mai kai mata,wai duk tsoran Salisu suke yi basa son Shiga gidan idan yana nan,Shafa’atu har da cewa.

“Nifa idan na ganshi sumbuk’ek’e a gabana sai naga kamar zai haye kaina,ni na rasa yadda Saratu take yi da wannan bijimin mutumin,shiyasa b’ata da aiki sai na ciwon hak’ark’ari da k’irji,Yo wannan mutumin ya hau kanka ai ka banu,don tsaf!Numfashi zai Iya gagarar mutum

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button