BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka suka dinga cin mutuncin Salisu suna dariya,sai gefanin magariba sannan kowacce ta nemi komawa gidanta,sai kuma washegari za a kuma had’uwa a gidan d’aya a yini ana tata shakiyanci da gulma da yi da mutane,haka abin nasu yake tafiya kowa da ranar dutinsa,Saratu ce kawai ba a cika zuwa gidanta ba saboda Salisu yace duk wadda ya sake gani a gidansa sai ya karya mata agara,ita kanta Saratun ya hanata zuwa gidansu a zauna zaman hira,sai dai in baya nan ta saci hanya ta fita,wataran har tabarma suke shimfid’awa a layin su zauna zaman hira da shan iska,Saratu kuma ta dinga lek’ensu ta soronta ana caccafkewa da ita,Abu dai ya zame musu kamar bala’i.
Allah ya shiya.
Washegari misalin k’arfe Tara na dare,Babalalo mijin Habiba tsaye a k’ofar shagonsa na Aski yana kullewa don haramar komawa gida,sai yaji ana sallama a bayansa,ya waiwaya a hankali yana amsawa sai yaci karo da Baba D’alha me tsire,
Baba D’alha ya mik’a masa Hannu suka gaisa,Sannan yace .
“Ba dai har ka tashi ba?Ashe da ban Hanzarta ba ba zan sameka ba kenan?
Babalalo yayi murmushi yace.
“Wallahi na tashi , Yau da wuri nake son komawa gida,gabad’aya gajiya ta baibaye jikina yau Baba”
“Haka ne kam!ai Neman na kai akwai wahala,Nima na baro yaro ne ya kula min da wajen sana’ar tawa saboda ina son magana da kai,dafatan kuma zaka bani lokaci kayi wa maganar tawa kyakkyawar fahimta,duk da dai naga yanayinka a gajiye kake”
Babalalo ya kalli Baba ya sake murmushi yace.
“Babu komai Baba ina saurarenka,Allah dai yasa lafiya?
Baba D’alha ya sauke Numfashi yayi k’asa da kai sannan yace.
” Daman na kawo maka k’arar matarka ne,Saboda abin da take min ya isheni,shine naga a matsayinka na mijinta kai ya kamata na samu na gayawa ko zaka yiwa tufkar hanci,don na san baka san abin da ke faruwa ba”
K’irjin Babalalo ya buga dammm!tun baiji abin da Habiban tayi ba ya samu fad’uwar gaba,domin ya San ba alkairi ta shuka ba,kamar Baba D’alha tsofai tsofai dashi ace ya kawo k’arar Habiba?Tabbas abun akwai d’aga Hankali,cikin dauriya gabansa na fad’uwa ya dubi Baba yace.
“Me Habiban ta aikata Baba?Sanar dani naji abinda tayi”
Baba D’alha ya jijjiga kai sannan ya fara koro bayani.
“Wato Babalalo kullum bayan magariba sai matarka ta lillib’o hijabi ta tawo gun tukubar tsirena,a ranar farko ban shaidata ba har ta tsuguna gabana ta gaisheni,na amsa mata na zaci nama zata siya,amma bud’ar bakinta sai cemin tayi ” Baba da Diddiga?na kalleta ina mamaki saboda ban gane maganarta ba,hakan yasa na tambayeta me take nufi,sai tace min “Y’ar Diddigar k’uli k’ulin nakeso Baba,wallahi kwad’ayi nakeji gashi bani da ko silai da zan siya” ban san me yasa ba sai naji tausayinta,nayi tunanin ko ciki ne da ita,ka San masu laulayi akwai kwad’ayi,hakan yasa na tattaro mata Diddigar har da naman ma na bata kyauta,ta dinga godiya ta karb’a ta tashi ta tafi.
In tak’aice maka Ashe wasa farin girki,domin tun daga ranar kullum sai tazo wajena da anyi magariba,ta lab’e a jikin tukubata ta mak’e murya tace “Baba da Diddiga?don Allah a taimaka a sammin Diddigar Baba” kai tun ina d’aukar abin wasa har hankalina ya tashi akan lamarin,musamman da na gano matarka ce,wata rana da tazo nai mata fata fata,nace kar ta kuma zuwa guna idan ba haka ba zanci mutuncinta,da taji hakan sai ta sauya sabon salo”
Baba yayi shiru yana kallon Babalalo da yayi tsumu tsumu kamar ya nitse Dan kunyar da Habiba ta jawo masa,Baba ya cigaba da cewa.
“Ka san Sabon salon da ta sauya?
Da k’yar Babalalo ya girgiza kansa da yayi masa nauyi,Baba yace.
” Kawai rana d’aya sai ta sauya salo,tana zuwa bata k’araso guna ba sai ta tsaya daga gefe ta samu Almajiri ta aikoshi wajena,lokacin da almajirin yayi sallama har da saurin mik’ewa da amsawa na zaci nama zai siya,nace masa na nawa za a baka naman?
Sai ya girgiza kai yace”Ba siyan nama zanyi ba,waccan matar ce ta aikoni wajenka”,yayi min nuni da Matarka a mak’ure a jikin wata Katanga,sannan yaci gaba da cewa”wai tace Don Allah ka sammata Diddiga”
CIN AMANAR RUHI200 KACAL GA ME BUK’ATA,WANDA BAI KARANTA BA AN BARSHI A BAYA,SANNAN AKWAI KAYA NA KECE RAINI,DUK ME BUK’ATAR SIYA YA TUNTUB’ENI AKAN LAMBATA TA WATSAP KAMAR HAKA 08080049548.
BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️
[7/26, 09:57] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????
????️ BAHAGON LAYI ????️
(RUK'IYYA)
TARE DA ALK’ALAMIN✍️
HASSANA D’AN LARABAWA
MARUBUCIYAR????
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
*DA KUMA*????
BAHAGON LAYI
NABI NA BAKWAI DA NA TAKWAS
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
SADAUKARWA GA????
DUK WANI MAI KARANTA LITTAFIN BAHAGON LAYI,NAJI DAD’IN KARB’AR DA KUKA YI WA LITTAFIN DA KUMA COMMENTS D’IN DA KUKE SUBURBUD’O MIN DA ADDU’O’I,ALLAH YA BAR ZUMUNCI FAN’S,WANNAN KARON SALON YA SAUYA BABU KUKA SAI DARIYA KO?IN DAI KUNA TARE DANI ZAKU DINGA GANIN SAUYI IRI IRI,MATAN BAHAGON LAYI SUN CE A MIK’O GAISUWA GAREKU MASOYA????????♀️????????????
A razane Babalalo ya d'ago kai yana duban Baba D'alha,shi ma Baban ya dube shi fuska babu walwala yace.
“Na san kaima mamakin abun kake ko?ni kaina na jima cikin mamaki da ta’ajibi,Kusan kwana uku kenan a jere tana samun almajirai tana aikosu,ni kuma bana bata, amma bata dena zarya akan na sammata Diddigar k’uli k’uli ba,shine nace bari in sameka in gayamaka don a yiwa tufkar hanci,ban sani ba ko bata da lafiyar k’wak’walwa ko tana da lalurar almutsutsai shiyasa take aikata irin hakan”
Babalalo ya share zufar da ta yanko masa yana girgiza kai,cikin shak’ak’k’iyar murya yace.
“Babu abin da yake damun k’wak’walwarta Baba,Lafiyarta k’alau tsabar iskanci ne da son ta tozartani,ban da haka da me na rageta,wallahi Baba ba a sati sai an ci nama a gidana,amma shine Habiba da aurenta zata dinga zuwa gunka rok’on Diddigar k’uli k’uli,amma gaskiya ta cuceni ta zubar min da mutunci na”
Baba ya jijjiga kai yace.
“Gaskiya bata kyauta ba kam!kuma nayi mamaki ace mai hankali yana aikata hakan,kuma kana da tabbacin bata had’a jib’i da maita ba?
Da sauri Babalalo ya dubi Baba D’alha yana zaro idanu,Baba ya d’aga Hannu ya tare shi kafin ma yayi magana.
” Abinne ya d’aure min kai shiyasa kaji na ambaci hakan Babalalo,in ba Hauka ko maita ba me zai sa tayi hakan?
K’irjinsa yana bugawa ya kalli Baba ya sunkuyar da kansa k’asa yace.
“Dole ne ai Baba,dole zuciyarka tayi zargi kala kala akan ta,amma Don Allah kayi Hak’uri akan abin da ya faru,zanwa tufkar hanci da yardar Allah,kuma nagode da karamcinka da har ka sameni ka sanar dani wannan maganar,Kayi hak’uri Baba D’alha”
Baba yayi murmushi yace
“Ba komai,wallahi komai ya wuce,daman don ka d’auki mataki da hanzari shiyasa na sanar da kai,tunda har ta fara zuwa wajena nan gaba ba a san gun Wanda zata ba,nima nagode da ka fahimceni Babalalo,bari na koma na bar yaro,Allah ya kyauta,Allah ya rufa asiri”
Baba ya mik’awa Babalalo Hannu suka yi musabaha,sannan ya wuce ya bar Babalalo a sandare a wajen,tsananin b’acin ran da ya samu kansa a ciki ya girmama,zuciyarsa har tuk’uk’i take yi saboda bak’i.
Da k’yar ya saita kansa ya d’aga sanyayyun k’afafuwansa ya nufi gida,zuciyarsa na tunanin irin Hukuncin da zai zartar a kan Habiba.
Tana k’ofar gidan a tsaye har ya fito yana lek’en me nemansa,ta matsa dab dashi tana gyaran murya sannan tayi magana.