BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Nice na aika a yi min sallama da kai,domin kaine dai dai dani ba ballagazar matarka ba”

Ya d’aga tocilan d’in hannunsa saboda duhun dare ya haske mata fuska Dan ya ganta sosai,sannan ya zarce da cewa.

“Baiwar Allah daga ina?ban gane kiba”

A fusace Maman Samiha ta fara magana.
“Daman ai bance lallai ka ganeni ba,Sunusi kake ko kamsusi?,Abu mafi muhimmanci shine ka bud’e fala falan kunnuwanka masu kama da na zomo ka saurareni,na kawo maka k’arar matarka ne akan zaluntar y’ata da tayi,daga anzo kitso gunta bata da aiki sai dukan y’ay’an mutane da rank’washi,babbar illarta shine kumburawa mutane ciki da tsinannen warin da jikinta yake yi,so nayi na sameta da kaina,sai kuma naga duk abin da ya biyo baya ni hukuma zata zarga saboda ni na taka naje gidanta,kuma ni in d’auki shegiya in runtuma da k’asa in haye ruwan cikinta ba wahala zai min ba,ba zan yarda da zaluntar Samiha da tayi ba,domin duk da mahaifin Samiha ya rasu nice uwarta nice ubanta,Dan haka sai inda k’arfina ya k’are ga duk Wanda ya zalunce ta,ka jawa matarka kunne ko kallon Banza ta kuma yiwa y’ata ko a hanya ne hukuma ce zata rabamu,mutuncinka na gani shiyasa na raga mata,kitso kuma daga yau insha Allah andena zuwa,tunda ba kitson Shiga aljanna bane”

Haka Umman Samiha tayi ta sababi da fad’a,shi kam Sunusi shiru yayi ya rasa ta cewa,tabbas ya gaji da masifar da Harira take jawo masa,amma kwata kwata ya kasa d’aukar mataki kamar Wanda aka d’aure bakinsa,shi kansa hak’urin zama da ita kawai yake,sannan warin da take yi ya d’auka shi kad’ai yake ji a tare da ita,Ashe har mutane suna ji,wannan wane irin abun kunya ne?

Da k’yar ya bud’i baki ya fara bata hak’uri da Neman afuwarta,a dai dai Lokacin da Babalalo ya iso layin nasu zai shiga gida ya tarar dasu a tsaye,Maman Samiha na k’ara Nanata masa ya jawa Harira kunne,idan ba haka ba duk matakin da ta d’auka su suka jiyo.
Tana kammala maganarta ta figi k’afafuwanta tayi gaba tana zabga tsaki kamar ta bangaje Babalalo dake daf da ita,da sauri ya kauce ya bita da kallo har ta fice daga layin,sannan ya waiwayo ya maida hankalinsa kan Sunusi da yayi kasak’e abin duniya duk ya isheshi,matsowa yayi kusa dashi shi ma jikinsa a sanyaye yace.

“Sunusi lafiya kuwa?me yake faruwa?

Sunusi ya sauke numfashi yace.

” ina fa lafiya Babalalo?Harira so take ta kasheni kawai ta huta”

Babalalo ya zaro idanu yace.

“Kamar ya ya fa?

Sunusi ya girgiza kai cike da takaici yace.

“Babalalo bak’incikin Harira ya kusa kasheni,bata da aiki sai janyo min magana,bata k’yaleni ba bata k’yale mutanen waje ba,yanzu haka wannan matar da ka gani fa k’arar Harira ta kawo min,shikenan ni ba zan san dad’in aure ba kenan?kullum cikin masifar mace da takaici?wannan wace irin k’addara ce?

Babalalo ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalli Sunusi fuska cike da damuwa ya fara magana.

” Tabbas Sunusi Allah ya jarrabemu da mata marasa kamun kai da nutsuwa,yanzu haka da ka ganni a hargitse nima b’acin ran Habiba ne ya tasoni a gaba,idan zan warware maka abun da ta aikata zaka tausaya min akan tozarcin da ta yi min,amma wallahi idan kai kaga zaka jure Halayen Harira ni ba zan jure na Habiba ba,domin mataki babba zan d’auka in yi mata abin da bata so”

“Me zaka yi mata?

Sunusi ya tambaya yana kallonsa.

Babalalo ya amsa kai tsaye yana murmushin mugunta.

” kishiya zan mata,aure zan k’ara domin babu abin da Habiba ta tsana a duniya irin kishiya,yanzu da zarar na fad’a mata hakan idan hankalinta yayi dubu sai ya tashi”

Sunusi ya jinjina kai yana dariya,kowa zai Iya d’aukar mataki akan matarsa amma shi ya rasa dalilin da yasa ya kasa tank’wara Harira,amma zai dage da addu’a idan ma wani sihirin tayi masa Allah ya karya shi.

Ganin dare ya fara yi sai suka yi sallama da juna kowa ya shige gida,gabad’ansu zuciyarsu ba dad’i akan Halin da matansu suke saka su.


Tana cikin gyara zaman bokitin da ta kammala tatar kunu ya shigo da sallama ciki ciki,da Sauri ta d’ago tana yangare hak’ora ta amsa sallamar,sannan ta zarce da cewa.

“Yau ka dawo da wuri,sannu da zuwa”

Ya dafka mata harara,a fusace ya amsa mata da cewa.

“Yauwa sannu jikar alasawa,ko nace sannu jikar mayu”

Ta k’walalo ido jin abin da yace,ta san duk yadda akayi laifi tayi masa,ita kam tana tsoran yiwa Babalalo laifi saboda ba k’aramin jarababbe bane,shiyasa duk wani iskanci a bayan idonsa take yi,sab’anin wasu daga k’awayenta da mazajensu ma basu k’yale ba,musamman Harira da Saratu.

Ta sunkuyar da kai k’asa tana susar k’eya ta kasa magana,da yake zuciyarsa a k’ufule take nan da nan ya hau ta da jaraba yana kumfar baki.

“Ban k’ara tabbatar da yawan iskancinki ya bod’ara ba sai yau Habiba,ni zaki tozarta ki dinga zuwa rok’on Diddigar k’uli k’uli gun me tsire?Ashe baki da mutunci ban saniba?jahilar ina ce ke da baki San muhimmancin aure ba?Habiba nagaji da b’acin ranki ba zan zauna ki jazamin ciwon zuciya a banza da k’uruciyata ba,tunda kunnen k’ashi ne dake bakya jin nasiha da magana zan kawo k’arshen iskancinki,insha Allahu ba zan k’ara cikakken wata biyu ba sai na k’ara aure,ko zan dace na samu macen da ta San darajata,wadda zata yi min biyayya ta kare min martabata da mutuncina,Dom…..

Gigitaccen ihu Habiba ta saki ta fad’i k’asa akan gwiwoyinta tana rusa ihu da tumami,babu abin da ta tsana a duniya irin kishiya,kuka take tana rok’on Babalalo afuwa da yafiya,amma yayi Biris da ita ya dinga rantsuwa akan aure zaiyi kuma bata isa ta hanashi ba,in zata zauna ta zauna,in ba zata zauna ba hanya a bud’e take ta kama gabanta,amma aure babu fashi.

Tsananin tashin hankalin da Habiba ta Shiga mai girma ne,ta san Babalalo da muguwar kafiya a kan k’udirinsa,domin mace bata isa ta juyashi ba,tasan duk rok’on da zata yi masa ba zai kulata ba,shiyasa zuciyarta ta kitsa mata tayi aljanun k’arya kawai ko domin ta hanashi bacci.

Cikin sakan biyar kuwa kawai sai Babalalo yaga Habiba ta baje a gabansa tana wani irin kanannad’ewa da mimmik’ewa,ga wani irin ihu da yare kala kala da take zubowa shi ba indiyanci ba, shi ba fulatanci ba, shi ba yarbanci ba,Babalalo ba k’aramin tsorata yayi ba saboda duk hargaginsa yana tsoran Aljanu,da sauri yayi baya yana kallonta idanuwansa a warwaje k’irjinsa na bugawa,ya rasa me zaiyi yana tsaye yana kallonta cikin tsoro,ganin ta fara zambarwa tana bige bige yasa shi runtumawa da gudu yayi soro yana haki cikin matuk’ar tsoro.

Fita waje yayi yana tunanin abin yi gashi dare yayi kusan k’arfe goma da mintuna,yana nan tsaye cike da tsoro ya jiyo d’aliban makarantar Daren da ke bayan layinsu suna addu’a zasu tashi,sai dabara ta fad’o masa akan yaje ya samo malami guda d’aya yazo yayi wa Habiba Ruk’iyya ko aljanun zasu tafi,da Hanzari ya nufi bayan layin Lokacin har d’aliban sun fara bajewa,kai tsaye babu Wanda ya nufa sai Malam Arabi,saboda tasu tazo d’aya daman shi yake masa aski.

Gefe d’aya ya jashi ya shaida masa abin da ke faruwa cikin tashin hankali,Malam Arabi ya sab’a babbar rigarsa a kafad’a yayi murmushi ga zabgegiyar bulalarsa a Hannu ta dukan d’alibai,Malam Arabi irin mutanen nanne masu cika baki da Nuna komai sun Sani a harkar malanta,alhali bashi da wani ilimi na kuzo Ku gani,haka nan bashi da ilimi akan harkar Ruk’iyya,amma jin maganar Babalalo sai ya ara ya yafa ,ya fara kurari yana Bawa Babalalo tabbaci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button