BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Mu har an gaya mana harkar aljanu,muje gidan nayi ido hud’u dasu yau za suci uwasu a hannuna,a gabanka zanyi fata fata dasu”

Haka suka tafi Malam Arabi yana ta sab’a malum malum,shi kam Babalalo a tsorace yake har suka isa gidan,Suna shiga suka tarar da Habiba har lokacin sai buge buge take,bakinta a bud’e sai zazzaro harshe take,A tsorace Babalalo ya nunawa Malam Arabi Ita yace.

“Kaga yadda take yi ko Malam”

Malam Arabi ya gyara bulalar Hannunsa yayi murmushi yace.

“Nagani Babalalo,aljanun da suke kanta mugwayen shakiyyaine,baka ga har gwalo suke mana ba?irinsu basa jin karatu sai duka, yanzu gasu nan ina kallonsu a tsakiyar bakinta suna rawa da juyi,Dan haka matsa ka bani guri kaga yadda zamu fafata dasu”

Babalalo ya matsa ya mak’e a jikin k’ofa zuciyarsa na lugude,yayin da Hankalin Habiba ya tashi,ta tabbatar wannan azzalumin malamin dukanta zaiyi,amma idan ta sake ta nuna k’arya take yi kuma kashinta ya bushe,tilas ta hak’ura ta cigaba da pretending a matsayin me aljanu.

Malam Arabi yayi Bisimillah ya d’aga bulalarsa Iya k’arfinsa ya Dage ya zambad’awa Habiba a tsakiyar bakinta,kamar wadda ake zarewa rai haka taji don tsananin azabar da ta ratsa kwanyarta,amma haka ta daure bata fallasa kanta ba,tuni kuma zuciyarta ta k’issima mata cewar yana yi mata bulala ta biyu to ta d’auki mataki a kansa.

Malam Arabi ya kuma d’aga bulalar ya sauke mata a leb’en bakinta na k’asa,wuf!Habiba tayi wata zambarwa ta mik’e ta damk’i Malam Arabi ta cukuikuyeshi ta shige cikin malum malum d’insa,da gudu Babalalo yayi tsakargida Hankalinsa a tashe,Malam Arabi ya fara tsalle da ihu jin Habiba ta damk’i k’ugunsa,sannan ta saici dai dai cibiyarsa ta kafa hak’oranta ta sakar masa wani annakakken cizo tamkar zata cizgo cibiyar a bakinta,ya saki wata bahaguwar k’ara saboda azabar da yaji,yayi zillo yana tunkud’eta da tsananin k’arfi,Babbar rigarsa ta hard’eshi sai gashi ya hantsila baya ya afka cikin bokin da ta kammala Tatar kunu,gabad’aya gasarar ta shek’o masa a fuskarsa da jikinsa…….!

BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️
[7/27, 16:08] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????

????️ BAHAGON LAYI ????️

    (MACE ME LEK'E )

TARE DA ALK’ALAMIN✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

MARUBUCIYAR????

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

     *DA KUMA*????

.
BAHAGON LAYI

BABI NA TARA DA NA GOMA

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~


https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

K’ila daga yau ba zaku sake ganin posting ba sai bayan sallah fan’s????????????

Kamar Dodo haka fuskar Malam Arabi ta koma saboda k’ullun kunu da yayi masa kwalliya faca faca,yana ganin yayi wurgi da Habiba ya daddafa ya mik’e a razane ya d’iba da mugun gudu yayi tsakar gida, ya yarda bulalar a nan,jin gudunsa yasa shima Babalalo ya d’iba a guje suka yi k’ofar gida suna rige rigen fita,a zaton Babalalo ko Habiba biyo Malam Arabi tayi,a sukwane suka fito k’ofar gida suna sauke bahagon numfashi da ajiyar zuciya,sannan suka tsaya suka yi cirko cirko suna kallon juna.

Babalalo ya kalli fuskan Malam Arabi a ragowar farin watan da ya haske sararin samaniya,yaga yadda k’ullu ya b’ata masa fuska tamkar Wanda watan Ramadan ya shigo yayi shirin tafiya tashe,k’iris ya rage ya kwashe da dariya sai dai yayi ta maza ya waske da tambayar Malam Arabi cikin haki.

“Wai Malam biyo ka tayi ne naga ka fito da gudu?

Malam Arabi yaji kamar ya shak’e Babalalo Dan k’ufula,ya kuwa dank’ara masa muguwar Harara ya zarce da bashi amsa a fusace.

” Ban sani ba,nace maka ban sani ba,banda wulak’anci daman ka san matarka mahaukaciyace kuma Y’ar iska ce ka kawo ni da sunan cire mata aljanu,yanzu ba Dan Allah ya kiyaye nayi ta maza ba Cibiyata fa taso cire min,kai wannan mata anyi tsinanniya,billahil azimu na zata kaca aka watsa min a Cibiyar,wai Ashe hak’oran ta ta kafta min,in banda Y’ar iska ce tana matar aure amma ta cafki Cibiyar k’aton mutum irina?Haka kawai da gemuna na sunnah ta keta min haddi?a yanzu ji nake Cibiyar na rawa tamkar zata fad’o k’asa,Allah dai ya tsareni kar in je ta zuba min virus da dafin bakinta”

Babalalo Abu biyu ya had’e masa,ga takaici ga shi yana son yayi dariya,tilas ya k’unshe dariyar ya dinga bawa Malam Arabi hak’uri,har da cewa.

“Malam mu koma cikin gidan na baka kaya ka sauya,kaga na jikinka duk sun b’aci da mark’aden gero, kar kaje gida a ganka haka babu dad’i”

Kallon da Malam Arabi yayi masa ko bai tanka ba ya isheshi amsa,amma Duk da hakan saida ya tanka cikin fusata da b'acin rai.

“Babalalo ka san tsirara?to gara na tafi tsirara akan na sake shiga gidanka domin annobar da take ciki,matarka kuwa kada Allah ya k’ara had’a fuskata da tata ko a hanya,domin naga bala’i da masifa a tare da ita yau,haka kurum daga zuwa taimako ta had’ani da jinyar Cibiya,Wallahi Allah ya isa ban yafe ba,Y’ar banza me hak’ora irin na karya”

Yana gama magana ya saita hanya yayi gaba zugudun zugudun kamar zai kifa,da yaga malum malum d’insa na hard’eshi ma tsayawa yayi ya cire ya soketa a hammatarsa,sannan yayi gaba yana ta masifa yana Jan Allah ya isa,Dan ji yake yi kamar Cibiyarsa ta tashi daga aiki.

Har ya k’ule Babalalo na tsaye yana kallonsa,sai da ya dena ganinsa sannan ya kwashe da dariya har da rik’e ciki,yayi dariya me isarsa har da hawayen mugunta,sannan yaji a zuciyarsa ya fara fargabar shiga gidan shi kad’ai saboda tsoro.

Yafi rabin awa a tsaye yana tararrabin shiga,gari yayi tsit dare yayi nisa kowa ya nemi makwanci amma shi yana tsaye ya rasa madafar kamawa,tilas haka ya daure ya fara sand’a ya shiga Dan ba zai iya kwana a waje ba..

        D'aga labulen falon yayi,sai ya hangeta daga gefe tana ta shirgar bacci har da Munshari,yayi ajiyar zuciya a hankali yana godewa Allah,a hankali ya fara sand'a zai tsallaketa ya wuce d'aki,bai kula ba saboda babu haske sosai k'afarsa ta dunguri tata k'afar,a tare suka razana,k'iris ya rage Babalalo ya saki fitsari a wando tsabar tsoron da yaji,ita kam Habiba k'unshe dariyarta tayi,domin tun bayan fitar Malam Arabi da yayi cilli da ita take dariya,sai da taji motsin shigowar Babalalo sannan ta fara baccin k'arya da munshari,kamar irin wadda bata san abin da ya faru ba ta fara murtsika idanu da Hammar k'arya,sannan ta juya ta kalli bokitin gasararta da ya b'are a gefe,sannan ta waiwayo ta dubi Babalalo da ke tsaye yana zare idanu,saura kad'an ta saki dariya amma ta gimtse,tayi mik'a tana kallon Babalalo tace.

“Me ya sameni ne naji jikina da bakina na ciwo?ga kuma k’ullu na ya b’are?

Babalalo ya fara in ina jikinsa na mazari.

” um…um..dama..daman fad’uwa ki kayi…shine kika b’arar da gasarar ..kuma kika bige bakinki”

Ya fad’a yana kallon leb’enta na k’asa da ya zama sharb’eb’e kamar ganda,saboda bulalar da yasha.

Ta mik’e tsaye tana bank’arewa Dan Duk jikinta ciwo yake mata saboda bige bigen da tayi,Babalalo ya d’an matsa Dan har lokacin a tsorace yake sosai,ta kalleshi tana k’unshe dariya tace.

“To taimaka ka gyara gurin nan da ya b’aci,zan je na kwanta saboda jikina ciwo yake min ko ina,k’ila fad’uwar da nayi ne yasa hakan,idan nayi bacci k’ila na samu sauk’in ciwon da nakeji”.

Da sauri ya amsa da .

” to!to!jeki ki kwanta abinki zan gyara”

“Idan ka kammala abincika yana kitchen sai ka d’auka”
Ta fad’a tana shigewa d’aki.

Tana shigewa ya sauke ajiyar zuciya,sannan ya fara gyaran wajen da ya b’aci,ya kauda bulalar da Malam Arabi ya gudu ya bari,ko abincin kasa ci yayi,ya d’auro alwala yayi salla yayi addu’o’i sannan yabi lafiyar ledar dake shimfid’e a falon ya kwanta,domin ba zai Iya zuwa d’aki kusa da Habiba ya kwanta ba,yana ta tunani a ransa a haka har bacci yayi nasarar kwasheshi.

Ita kam Habiba tun da ta kwanta a gado take dariya,ta san yadda Babalalo ya tsorata ba zai sake yi mata maganar kishiya ba,Malam Arabi kam ta tsine masa yafi sau shurin masak’i,domin ya d’and’ana mata azabar da ta jima bata ji irinta ba,ji take tamkar harshenta da leb’enta zasu zazzago,duk da dai tayi masa abin da gobe idan an masa tayin zuwa Ruk’iyya sai ya zunduma a guje,saboda mikin da ta asassa masa a bisa Cibiyarsa,da wannan tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita.


Washegari a gidan Zahra’u aka baje,domin ranar dutin ta ne, a gidanta za a yini a na washshagare walle,Suna baje a falonta su Uku ana shan rake,Zaha’u da Shafa’atu sai Harira da take basu labarin zuwan Maman Samiha gun Sunusi da kashedin da ta bayar,suna ta dariya har Zahra’u ta mik’e ta Shiga d’aki ta d’akko wani turare na tsuguno da Miski ta mik’awa Harira,Ta karb’a tana ajiye raken hannunta sannan tace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button