BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Wannan fa na menene?
Zahra’u ta zauna ta kalleta tace.
” Harira shawarar da zan baki kidinga gyara jikinki,kin San Allah tunda aka fara da haka wataran zaki nemi masu zuwa kitso ki rasa,kuma dai kin san ba k’aramin rufin asiri kike samu a cikin sana’ar ba,wannan turaren dubu d’aya kenan,ki daure ki siya ki dinga turara k’asanki kina shafa miskin,ina tabbatar miki duk wani wari da d’oyi da kike yi zaki dena,wajen zai dinga k’amshi ko fitsari kika yi sai yayi k’amshi,ko ba don masu zuwa kitso ba kya gyara ko don mijinki yaji dad’i,ke ko Dan kiji dad’in jikinki kya gyara Harira”
Da kyar Harira ta amince zata siya sai da Shafa’atu tasa baki tukun,Zahra’u tana ta cusa musu ak’idar amfani da magungunan mata na mallaka da na jin dad’i,domin a wannan b’angaren tayi zarra,shiyasa k’asimu yake ji da ita,kuma bata b’ata masa rai biyayya take masa kamar ta kwanta ya takata,ta wannan b’angaren kam tafi su Harira wayo saboda bata raina mijinta ba, kuma ta iya siyasa.
Suna nan zaune sai ga Habiba ta shigo kamar an jeho ta,duk suka bita da kallo hankalinsu a tashe ganin yadda leb’enta ya zama lafcece yayi tsawo yana reto,kamar sun had’a baki wajen tambayarta.
“Habiba Had’ari kika yi ne?
Ta zauna tana girgiza kai leb’en na rawa saboda suntumar da yayi,sosai tayi muni kamar wata horuwa,cikin takaici tace.
” ina fa Had’ari!wannan dukan Malam Arabi ne kawai”
“Wane Malam Arabin?ke kuwa wane laifi kika yi masa tashi d’aya ya sauya miki halitta?Habiba kin duba mudubi kinga yadda bakinki ya zama kuwa?sai kace gandar da taji dahuwa a cikin tukunya”
Inji Harira ta ambata tana kallon bakin Habiba da yake k’yalli saboda basilin d’in da ta lafta.
Shafa’atu ta karb’e maganar da cewa.
“Lura dai Harira!ai wannan bakin yafi kama da ragadadar da aka gama dafata aka bajeta a faranti,gaskiya Habiba duk Wanda yayi miki wannan abin yayi miki k’arshen cuta,nifa ba don na sanki sosai ba da wuya na shaida fuskarki,wai!sunan wani gari!wai shi Kumbotso”
Suka k’yalk’yale da dariya.
Habiba ta hararesu tace.
“To!marasa mutunci,idan kun gama yankata sai Ku tsaya na Baku labarin abin da ya faru”
Nan ta Shiga basu labarin komai da komai da ya faru a Daren jiyan,Subhanallahi!dariya dai me suna dariya ranar sun shata har da birgima,shakiyanci iri iri,Zahra’u har da cewa idan K’asimu ya dawo zata sa ya siyo lemo da Ayaba suje su dubo Cibiyar Malam Arabi.
Da sun dubi leb’en Habiba kuma su shek’e da dariya,Shafa’atu ta saita wayarta ta d’auki bakin Habiba hoto wai zata sa a status d’in ta,haka suka addabi Habiba da tsokana kala kala,kuma a ranar ma Saratu bata fito ba saboda gargad’in da Salisu ya gindaya mata,tilas ta hak’ura saboda bata manta da gittar da Salisu yayi mata a muk’amuk’inta ba.
Tana tsaye a soron gidanta daga ita sai zani da k’aramar Riga Duk k’irjinta a waje,babu d’ankwali a kanta,ta d’an sakayo k’ofar ta zuro kanta tana ta lek’en waje da masu wucewa,daga gefen layin nasu wasu yara ne suke ta wasanni suna buga ball,tana ta kallonsu suna kokaye kokaye tana musu dariya,duk da Salisu ya hanata fita ta shiga cikin k’awayenta hakan ma yana d’ebe mata kewa,can yaro d’aya ya hard’e d’ayan da k’afarsa garin buga ball har ya tuntsira ya fasa baki ,nan yaron ya fara kuka,ta tuntsire da dariya ganin jini a bakin yaron tana fad’in “Allah ya k’ara,shegu kun baro Layin Ku kunzo kun addabemu da ball a namu layin”
D’aya yaron ya kama dariya ganin ya FASA masa baki,a fusace wancan ya mik’e ya d’auki wani rank’walelen dutse yana kuka ya saita yaron da ya tureshi ya cillo masa dutsen da nufin jifansa,da sauri yaron ya falla da gudu ya kauce,cikin ikon Allah dutsen bai sauka a ko ina ba sai a goshin Saratu dake lek’e,ji kake Dammmmm!
Bala’in da ya ratsa kan Saratu bashi da misali,har ga Allah ta zaci rodi aka maka mata saboda tsananin yadda dukan ya ratsa ta,a razane ta saki k’ofar soron tayi cikin gida da gudu tana ihun azaba,jini tuni ya wanke mata fuska saboda yadda goshinta ya fashe,tashi d’aya kuma ya kumbura suntum kamar an dasa mulmulallen lemon zak’i,haka ta dinga safa da marwa a tsakargida tana kuka tana tallafe goshi jin yana shirin zazzagowa ya fad’o k’asa Dan har wani zillo yake,ganin jini yana sharara da gudu ta nufi famfo ta Tara fuskar tana wankewa,da k’yar jinin ya tsaya ya dena zuba,amma hawaye bai dena sharara a idanuwanta ba, Dan zafin da take ji kamar wadda a ke dafa k’wak’walwar kanta a kurfoti,haka ta lallab’a ta shige falonta ta ware fanka ta kwanta shame shame ta Shanya k’aton goshinta domin yasha iska……!
A K’ARA YAWAN COMMENTS FAN’S????????♀️????????♀️????????♀️
BY HASSANA D’AN LARABAWA✍️
08080049548.
[7/28, 10:51] Hassana D’an Larabawa????: TYPING????
????️ BAHAGON LAYI ????️
(CHEMIST)
TARE DA ALK’ALAMIN✍️
HASSANA D’AN LARABAWA
MARUBUCIYAR????
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
*DA KUMA*????
BAHAGON LAYI
BABI NA SHA D’AYA DA NA SHA BIYU
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
???? PEN WRITERS ASSOCIATION????️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
SABODA YARDA KUKA K’AGU SHIYASA NA K’ARA MUKU WANNAN SHAFIN,INA JIN DAD’IN YADDA KUKE SON LITTAFIN,HAR WASU SUNA CEWA WAI DA MA SUNAN LITTAFIN MAGANIN HAWAN JINI????????????JINJINA GAREKU MASOYANA,DAGA YAU SAI BAYAN SALLAH IDAN DA RAI DA LAFIYA????????♀️????????♀️????????♀️MATAN BAHAGON LAYI SUNA JIRAN KU AIKO MUSU DA NAMAN SALLARSU????????????
Har Yamma da Salisu ya dawo gida Saratu na fama da rad’ad’in goshi da ciwon kai,haka tayi ta b’oye b’oye Dan kar ya gani amma sai da idanuwansa suka gane masa. Ya zuba mata idanu yana tambayarta.
“Me ya samu goshinki haka yayi tulele yayi tsini?
Ta fara inda inda har ta samo amsar da zata bashi.
” Daman fad’uwa nayi a band’aki,santsin sabulu ne ya kwasheni da zanyi wanka shine na buge goshi da bango”
Yayi kasak’e yana kallonta zuciyarsa bata amince da abin da tace ba,saboda ya san ta muguwar mak’aryaciya ce,amma duk da hakan sai ya share ya bita a yadda ta fad’a.
Magriba tayi ya d’aura alwala ya fice masallaci,bai dawo ba sai da ya sallaci isha’i sannan,yana shigowa ya tarar da Saratu tana zagaye a tsakargida,goshinta ya addabeta da ciwo kamar tayi hauka,sai k’ara hawa yake yana kumburi kamar Wanda aka zubawa yeast,ga hawaye yana sharara a idanuwanta,kawai sai yaji tausayinta duk da iskancin da take masa,tsakanin miji da mata sai Allah,ya kalleta sosai yace.
“Wai goshin har yanzu bai sace ba?
Ta gyad’a kai hawaye na k’ara zuba,da k’yar tayi magana.
” K’ara kumbura ma fa yake,ni dai Allah ya tak’aitamin wahala kar na zama mai kawuna biyu”
Yayi d’an murmushi sannan yace.
“D’akko mayafinki muje gun D’ahiru me chemist, ko akwai maganin da zai taimaka ya baki don goshin ya sace kuma ya rage zugin da yake”
Da hanzari ta shige d’aki ta yayimo hijab ta saka suka fita, Salisu ya kulle gidan suka fice daga layin zuwa bakin titin unguwar,Da yake Salisu yana da jiki kuma yana da sauri sai ya shige gabanta ya barta a baya,duk taku d’aya idan zaiyi sai mazaunansa sun juya,Saratu duk da ciwon da take ji hakan bai hanata dariya ba,ganin sai sukutur sukutur mazaunansa keyi,nan da nan ta fara wak’a da Y’ar k’aramar murya tana fad’in.
“Sittin, saba’in,sittin,saba’in,sittin,saba’in”