BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON LAYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Salisu yaji kamar magana take yi shiyasa ya juyo yace.

“Magana kike yi ne?

Ta k’unshe dariyarta tace.

” Eh!cewa nayi dama a gaba ka sakani,wallahi kayi min d’irmeme a gaba ko hangoni ba a yi”

Ya zabga tsaki ya juya ya cigaba da tafiyarsa,domin yayi zaton wata magana ce mai muhimmanci,Ashe iskancin da ta saba ne,tana fama da goshi amma ba ta bar shakiyanci ba,Saratu ta k’unshe baki tana dariya har da yi masa gwalo.

Suna isa shagon D’ahiru basu samu jama’a ba sai shi kad’ai,Bayan sun gaisa,Salisu yayi masa bayani,sai ya buk’aci Saratu ta matso ya duba goshin.

Ta matsa kusa da shi ya bata kujera ta zauna,yayin da Salisu ya zauna a wani benci da ke gefe,D’ahiru ya d’akko wata( torchlight) me haske ya haske goshin Saratu,ta runtse idanu saboda hasken fitilar,ba zato ba tsammani Saratu taji D’ahiru ya kai Hannu ya latsa goshin da d’an k’arfi,wani shahararren ihu ta saki tare da bud’e idanuwanta ta mik’e a gigice saboda zafin da ya ziyarci k’wak’walwar kanta,ba tayi wata wata ba ta fidda Hannu ta zabgawa D’ahiru wani bahagon mari har sai da hular kansa ta fad’i shi kuma ya tuntsira k’asa hajijiya na d’ibarsa.

Salisu ya mik’e a firgice yana dafe kunci kamar shi aka Mara,cikin tsananin tashin hankali ya dubi Saratu dake maida numfashi yace.

“Saratu baki da hankali ne?kin san abin da kika yi kuwa?ko kin sha kayan maye ne?

” Eh!Burkutu nasha,wadda ka sha ka rage min a matsayin karin kumallon safe ba,banda shi mugu ne azzalumi ta k’ak’a ina fama da goshi na zai k’arasa b’urma min shi,Ashe ba k’arya bane da ake cewa likitoci azzalumai ne,to in yayi wa wasu mugunta ya kwana lafiya ni yayi kad’an in k’yale shi, wallahi daddala masa mari zanyi, in sace masa k’aton kumatunsa mai kama da naka”

Salisu Haushi da takaici ya kamashi ya nufota kamar zai dake ta,wai me yasa komai a ka had’a da jaki sai yaci kara?Da sauri D’ahiru ya mik’e jikinsa a sanyaye saboda Marin ya shige shi ba kad’an ba,Dan shi a zatonsa ma ya makance Dan tsinin D’an yatsanta saida ya tab’a idon sa,amma da yake mutum ne mai yawan Hak’uri sai ya fara bawa Salisu hak’uri,ya d’ora laifin a kansa a matsayin hannunsa ne ya kufce har ya danna mata goshin da k’arfi.

  Tilas Salisu ya koma ya zauna yana ta numfarfashi,ba k'aramin b'ata masa rai Saratu tayi ba,ji yake kamar ya sake yi mata gittar da yayi mata randa ta ambato Mahaifiyarsa,in yaso ya bajeta a chemist d'in kowa ya huta.

Shi dai D’ahiru dole ya hak’ura da tab’a goshin Saratu ,kawai ya harhad’a mata magani da na sha da na shafawa,sannan ya juya ya dubi Salisu yace.

“A bayaninka da kuka zo kace min fad’uwa tayi a band’aki ko?to gaskiya abin da nagani wannan goshin nata ba fad’uwa bace,Marmara ce ta kawo masa ziyara,da alamun wani muk’ek’en dutse ya sauka a gurin”

Hankalin Saratu ya tashi jin maganar D’ahiru,haka kawai zai tona mata asiri,shiyasa ta figi ledar maganinta ta zabga tsaki ta kalli Salisu tace.

“Idan ka gama sauraron k’aryar da yake shirga maka ka biyoni ,ni dai nayi gaba”

Ta fice daga shagon tai tafiyarta,sai da taje k’ofar gidan ta Ganshi a kulle sannan ta tuna Ashe mukullin na hannun Salisu,tilas ta tsaya tana tsaki ku san minti goma sannan ya k’araso,kallon banza yayi mata yasa mukullin ya bud’e gidan,ita kam k’eya ta juya masa,tana ganin ya shiga ta bishi a baya ta na yiwa k’eyarsa gwalo.

Da suka shiga sosai ya dinga yi mata fad’a akan Marin da tayi wa D’ahiru me chemist,sannan ya fara tuhumarta ya akayi aka jefeta a goshi?amma Saratu ta gaddame akan D’ahiru k’arya yake yi kawai fad’uwa tayi.
Tilas ba don ya yarda ba ya k’yaleta ya shiga sabgar gabansa.


Sati d’aya bayan hakan leb’en Habiba da goshin Saratu ya warke,haka nan babu abin da ya sauya a hallayarsu ta tumasanci da akuyanci,sunk’i hankali su gane hanyar dai dai.

Zahra’u ce ma ta d’an fisu hankali,domin ko ranar dutin ta da zarar yamma tayi take korarsu gidajensu,saboda bata son b’atawa K’asimu rai ko kad’an,ta yarda suyi shargallensu amma bata amince a Shiga hakkin mijinta ba.

Ranar ta kasance Lahadi,suna zaune gabad’ayansu a gidan Safa’atu,har da Saratu da ta samu fitowa saboda Salisu baya nan ya tafi d’aurin auren wani Abokinsa a Katsina,Hira suke sha suna gulmar yadda suka ga ana shigowa da kaya na garari da za a jerawa amaryar da zata tare a d’aya gidan,a labarin da suka samu mijinne bai k’arasa gininsa ba,shi kuma mahaifin amarya yana so ya had’a bikinta da na yayarta,shine dalilin da mijin yazo ya kama haya su zauna na wani d’an lokaci kafin ya kammala NASA ginin,daga ganin kayan da ake shigowa da su Jere sun san yarinyar Y’ar gata ce,kuma ance mijin yana da abun hannunsa sosai,da alamu zasu dinga sharb’ar romon dimukrad’iyya kenan,musamman idan suka yi nasarar janyota cikinsu.

Harira ce ta shiga kitchen d’in Shafa’atu da niyyar d’ora musu girki,garin tab’e tab’enta ta hango bak’ar Leda da kifi a cikinta,ta k’walawa Shafa kira tana cewa.

“Au Shafa wasa tare ci bambam ko?da ban shigo kitchen d’in ba ba zamu San kina da kifi ba balle ki bamu rabon mu,to Allah ya toni asirinki”

Shafa’atu ta taso tana k’ok’arin fizge ledar tace.

“Rufamin asiri Harira!wannan kifin da kika gani Kamilu ne ya siyo wai in yiwa Goggo Zulai farfesu da daddare za mu je dubata bata jin dad’i,Dan haka bani nan ba nawa bane na Uwar masu gida ne”

Harira ta danna mata Harara tace.

“Kutri!Ai ba Goggo Zulai ba wallahi ko Zulailaya me kan tantabara ce sai munci kifin nan,ke kin san ko mage ta saramin wajen k’aunar kifi, Dan haka ja jiki Malama wannan kifin haramiyar uwar masu gida wallahi”

Ba irin magiyar da Shafa’atu bata yi ba amma suka hanata,tana ji tana gani suka sarrafa kifin nan aka saka a dafadukan taliya me manja da romo,kan kifin kuma Zahra’u taje ta d’akko k’uli k’uli suka daka kafikaza suka sa a ciki,Shafa’atu dai tunanin k’aryar da zata yiwa Kamilu kawai take yi,ya siyo Abu Dan mahaifiyarsa amma sun cinye.

Basu bar gidan ba sai da suka ga dawowar Kamilu yamma lik’is,kowacce ta shuri silifanta tayi gaba,suka bar Shafa da susar k’eya da Neman abin da zata kare kanta.

Har Kamilu ya shirya bayan dawowa daga sallar isha’i,ya nemi Shafa’atu ta d’akko mayafinta su wuce tuni ya karb’o Aron mashin d’in abokinsa,ta tsaya nuk’u nuk’u,ya nufi kitchen yana cewa.

“A wane flask kika zuba farfesun ne?zo kibani in saka a Boot saboda kar ki rik’e a Hannu romon ya Zube”

Jiki a sanyaye tace.

“Nifa ba wani farfesu da nayi”

Ya juyo a hanzarce yana dubanta yace.

“Kamar ya ya ba wani farfesu da kika yi?ban gane ba”

Ta d’an zumb’ura baki ta Sosa k’eya tace.

“To ba muna ciki muna hira ba bamu sani ba Ashe magunan bayan layi sun shigo sun shiga kitchen d’ina sun cinye kifin”

“Kan uban can!kifin mahaifiyar tawa ne maguna suka cinye?magunan bayan layi ko magunan k’awayenki,amma Shafa kin mugun rainamin ajawali,ki Tara d’ima d’iman mata Ku cinye kifi kizo ki ce min wai maguna sun cinye?ni sa’an wasanki ne da zaki kawo min d’ibar albarka?

Shafa ta cono baki ta fara maganganu.

” Kaga Kamilu kar ka nemi ka zageni akan kifin da bai wuce na d’ari uku ba,ka jirani zuwa gobe zan biyaka d’ari ukun ka Dan kar ka kaini gaba”

Ta saki mugun tsaki ta shige k’uryar d’aki ta barshi da Baki a sake,tsananin mamakin k’arfin halin Shafa’atu ya kid’ima Kamilu.

“****

Akuyar d’aure ta samu sake!
Tun bayan da suka fito daga gidan Shafa kowacce ta shige Gidanta amma banda Saratu,kawai sai ta shige gidan Amarya da ta tarar ana dandazon Shiga duk dangin amarya da Ango sun cika layin,ta nemi guri ta rashe har aka kawo amarya,ita a ganinta tunda Salisu Katsina ya tafi sai Can dare zai dawo,bata san cewa tuni ya dawo ba kuma ya tarar bata nan,hakan ya harzuk’ashi ya tafi gidansu Saratun ya fad’awa Mahaifinta duk irin wulak’anci da rashin mutuncin da take yi,Sosai ran Malam Munzali me almajirai ya b’aci,ya umarci Salisu ya tashi su tawo gidan tare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button