BAIWATA 10

Tausasa murya tayi sosai sannan tace” Abba, yanzu duk lamarin da aka tanadar wa wannan hukuncin bai kamata mu riƙeshi iya ƙarfinmu ba? Manyan Malamai magabata akwai masu fahimtar wanda duk ya bar sallah ta kubce masa da-gangan to ya zama kafiri, idan har zai yi sallah ta gaba ko ya ranka wannan sallar to a ganinsu sai an kuma bashi kalmar shahada, inda wasu malaman ke ganin a’a ba ka kafirta ba, sai dai ko kayi sallar ba lallai ubangiji ya amsheta ba saboda kayi kan lokacinta ba, dan haka wasu suke ganin kar ma kayi shi ya fi.”
Raunana murya tayi kamar za ta fashe da kuka tace” Ta ya bayan na san wannan zan zuba ma ƴan uwana ido suyi wasa da sallah, bayan dukaninmu nan mun san ita ce kawai ta bambamta mu da kafiri, indiyawa su na azumi dan buƙatunsu da al’adunsu, mu ma musulmi munayi, krista suna raba dukiyarsu ga mabuƙata, akwai daga cikin waɗanda ba su da addini da suke zuwa ziyarar ɗakin Allah, imma dan buƙatarsu ko kuma ganin al’ajabin wurin da ɗaukar rahoto, sannan kafirai dayawa sun yarda akwai Allah kuma shi ya haliccesu kamar dai mu, sannan sun yarda Annabi Manzonsa ne, imani da shi ne kawai ba su yi ba, to ku faɗa min a nan me ya rabamu da su? Sallah ce kawai ko arne ya ga mai yin ta zai sa wannan musulmi ba tare da ya yi tambaya ba.”
Kallon Ummee ta yi da jikinta ya mutu sosai tace” Ki tsayar da sallarki, za ta zame miki haske a ƙabarinki, sannan idan sallarki ta yi kyau a sikelin lahira, to hisabi ma bai zama lalle gareki ba.”
Ita kanta amarya da bala’i ne ya kawota sosai jikinta mutu ta ji zuciyarta na dukan tara-tara tunawa da yanda ita ta ɗauki sallarta, sai kawai ta juya jiki a sanyaye ta bar ɗakin, haka Alhaji Auwal da Hajia Rabi ma suka fita suna jin gaba-ɗaya yarinyar ta gama ɗauresu da wasu manya-manyan igiyoyi da ba zasu iya kwance kansu ba.
Ganin haka Saleema ta fita a ɗakin ta hauro ƙasa tare da Hajia babba wacce yanzu ɗakinta ke ƙasa sablda wuyar da hawa saman ke mata, cikin ladabi ta tabayeta “Mama, zan iya shiga madafa?”
Murmushi ta sakar mata tace “Me zai hana Saleema, ki shiga ki ɗauki duk abinda kinke so.”
Girgiza kai Saleema tayi tace “A’a Mama ba dan buƙatata ba ne, abun kari zan haɗa, na ga mai aiki ba a nan take kwana ba.”
Girgiza kai tayi ita ma tace “A’a Saleema, ki bari na gama sallah sai na ɗora, dama sai rana ta yi take zuwa, iya shara da wanke-wanke da sauran ayuka take yi, amma girki mu ke yi sai dai ta taimaka mana da wani abun kawai, dan Alhaji baya son cin abincin mai aiki.”
Ƴar dariya tayi tace” Hakan ya yi kyau, kamar Babana shi ma haka yake, amma ki bari ni zan ɗora, idan da buƙata ku sai ku ɗora na Abba idan kun ida sallah.”
Faɗaɗa murmushi tayi tace” Nagode Saleema, Allah miki albarka.”
Da fara’a ita ma ta amsa da” Nagode Mama, amma me za’a dafa?”
Da fara’a tace” Saleema ko me kika dafa ma ai ya yi, ki duba a madafar akwai duk abun buƙata, idan kuma kin rasa wani abun ki min magana.”
Jinjina kai tayi cike da ladabi ta wuce madafar inda ta fara da abinda ta gani kuma ta iya sarrafawa. Hajia Rabi na idar da sallah ta fito za ta shiga wajen Alhaji dan tambayarshi abinda zai ci, Mu’az ne ya shigo gidan dan bai kwana a gida ba, tsaye tayi har ya ƙaraso yana gaisheta da “Ina kwana Mama.”
Na wasu daƙiƙu ta fara zuba masa ido kafin tace “Ba’a gida ka kwana ba ko?”
Ba tare da damuwar komai ba ya amsa da “E Mama.”
Ba alamar wasa a tare da ita dan bata so ya kawo mata wargi duba da tambayar da za ta mishi ba ta taɓa kwatanta yi masa ita ba sannan tace “Ina ka kwana?”
Da sauri ya saka idonshi a cikin na ta kamar wanda aka ba wa tsoro, sai kuma ya saka fuskar mamaki yace “Mama, me ya sa kika tambaya? Wani abu ya faru ne?”
Sake haɗe fuskarta tayi tace “Sai wani abu ya faru zan tambayeka?”
Ɗan girgiza kai yayi yace “E to Mama, na ga dai haka bai taɓa faruwa ba ai.”
Tsareshi tayi da ido tace “Amsar tambayata?”
Ɗan matse bakinshi yayi yace “Abinci na fara ci a restaurant, sannan na wuce majalisarmu, ba mu tashi a nan ba sai ƙarfe uku na dare, daga nan mu ka ƙarasa gidansu Zeid a can na kwana.”
Wani sakaran murmushi ta yi tace “Ka kwana ko ka rintsa? Ai ka gama kwananka tun a majalisa.”
Gyara tsayuwa ta yi tace “Sallah da, ka yi sallah kafin ka shigo?”
Ƙanƙance ido yayi yana mata kallo mai kama da hangen nesa yana so ya gano me ke damun Mamanshi yau? Cikin mamaki yace “Na yi sallah Mama.”
Harara ta galla masa tace “Yanzu ka yi ko?”
Sosai ƙeya yayi alamar kunya bai ce komai ba, girgiza kai tayi tace “Allah ya shirya.”
“Ameen Mamana.” Ya faɗa yana binta da kallo, ganin za ta yi nisa ya matsa kusanta yace “Mama.”
Juyowa tayi tana kallonshi amma ba ta ce komai ba, da ɗar-ɗar din amsar da za ta bashi yace “Mama wani abu ya faru ne?”
Da mamaki tace “Me ka gani?”
Sunkuyar da kai ya yi yace “Na ga ai kina ta min wasu tambayoyi ne kamar ƙaramin yaro ko wata mace.”
Wani kallo ta mi shi tace “Au! Ina matsayin mahaifiyarka ba zan tambayeka ba tunda ka wuce munzalin?”
Girgiza kai yayi yace “A’a Mama ba haka nake nufi ba, abun dai ne ya zo min wani iri, baki taɓa haka ba fa Mama.”
Jim! Ta yi ta kalleshi kuma ta san gaskiya ya faɗa, gyara tsayuwarta ta sake yi tace “Gaskiya kam, ni ma kuma na san tambayoyin da na maka sabon abu ne, amma dan Allah da na tambayeka ba ka ji daɗi ba?”
Murmushi ya sakar mata tare da dafa duka kafaɗunta ya ɗora haɓarshi a wuyanta yace “Na ji daɗi sosai Mamana, hakan ya nuna min yanda ki ka damu da ni.”
Turo ɗan bakinta tayi gaba cikin shagwaɓa tace “Zuwan yarinyar nan ya zamar mana alkairi, daga jiya zuwa yau ta haska mana abubuwa da dama da suke shige mana duhu, musamman ma a kan sallah da ta tunatar da mu yanzun, sai na ji kamar zan zauna na yi ta kuka saboda kurakuren da muka tabka a baya, amma in sha Allah na ɗauki niyyar gyarawa da wannan nasihar da ta mana.”
Hannu ta zura ta bayanta ta shafi kumcinshi a shagwaɓe sosai tace” Gaskiya yarinyar kirki ce, ina ma za ta zama surukata?”
Da mamaki ya ɗaga kanshi kaɗan yace” Mama, wacece wannan?”
Hararan wasa ta jefa mi shi tace” Wa fa ban da Saleema.”
Wani ƙasaitaccen murmushi ya saki tare da maida haɓarshi a kafaɗarta, haka kawai ya ji wani shauƙi da daɗi na sunan da ta ambata, shiru ya yi ya lumshe ido a kafaɗarta kamar bacck zai ɗauke shi. Tureshi tayi tace” Kai ɗagani, har yanzu ban shiga madafa ba.”
Takwaf-takwaf ya yi da fuska yace” Mama yunwa fa na ke ji, shiyasa na shigo da wuri.”
Nuna mishi ƙofar madafa ta yi tace” Ka shiga madafa ba za ka rasa abun da za ka ci ba.”
Turo baki ya yi gaba ya nufi hanyar madafar ita ma ta ƙarasa in da za ta je sam ta ma manta da Saleema na madafar.
Alhamdulillah.