BAIWATA 11
“Ina za ki je?” Alhaji Auwal ya faɗa daga bayansu yana fitowa, tare suka kalleshi sai da Saleema ta sauke ƙaƙƙarfan numfashi, saida ya ƙaraso gabansu ya tsaya yana kallon Saleema yace “Ina na ke jin kina cewa za ki tafi?”
Tsareshi tayi da ido ta girgiza kai alamar ba komai, kallon Hajia ya yi yace “Me yake faruwa?”
Kallon Saleema tayi sannan ta kalleshi tace “Wai gida za ta tafi, na tambayeta me aka mata ta ce ba komai.”
Kallon Saleema ya yi da ke ta fiƙi-fiƙi da ido yace “Me aka miki?”
A raunane tace “Ba komai Abba, dama kewar Mama na yi.”
Wani kallo ya watsa mata kafin yace “Je ki aaje jakar, ba haka mukayi da Abbanki ba, idan kuma kin dage za ki tafi sai na kira na faɗa masa.”
Da sauri tace “A’a Dan Allah, kaa yi haƙuri Abba na fasa tafiyar.”
Hanyar ɗakin ta kama sai kuma ta juyo tace “Amma Abba Mu’a…”
Sai kuma ta ga kamar bai kyautu ta faɗa musu ba, dan haka ta juya da sauri kawai ta barsu nan tsaye suna binta da kallo har ta shige sannan su ka bar wurin.
*Bayan minti 20*
Hamdeeya ce ta shigo da sauri ɗakin tace “Saleema wai in ji Abba ki zo.”
Kallonta tayi kamar ta ce ba za ta zo ba, dan ta fi jin nutsuwa a zaman ɗakin, amma sai ta jinjina kai tace “Ina zuwa.”
Da gudu Hamdeeya ta fita kafin ta miƙe jiki a sanyaye ta ɗauki hijabinta akan riga da siket ɗin da ta saka yanzu bayan ta yi wanka, cikin nutsuwa da dattako ta shiga taka matakalar, ba ta ɗaga kai ta kalli inda ta ji mutanen suke ba, sai dai daga yanda take ji akwai ido sosai dake yawo a jikinta, bata kuma tantance su waye a wurin ba.
Saida ta gama sauka sannan ta ɗan ɗaga kanta dan ta san inda za ta dosa, fahimtar Alhaji Auwal ya na kan teburin cin abinci ya sa ta nufa can ɗin, tun kafin ta ƙarasa yace “Yawwa zauna.”
Kanta a sunkuye kamar wacce ta aikata abun kunya ta ja kujerar da ta kula ba kowa a kai ta zauna, hannayenta da suka fito waje sanadiyar hijab ɗin ta mai hannu ta ɗora akan teburin ta na wasa da yatsunta cike da kunya da ladabi. Hajia Rabi da ke kallonta cike da birgewa da ƙaunar yarinyar tace “Saleema, ki saki jikinki kin ji, ki ci abinci.”
Sai lokacin ta ɗaga kanta dan kallon Hajiar, sai dai a lokacin ta kula da waɗanda ke wurin, Alhaji Auwal ne da amaryarshi, sai Hamdeeya da ita Hajiar da kuma wannan kuren, ba ta yarda ta haɗa ido da shi ba dan jikinta ya bata kallonta yake, a hankali ta ja farantin gabanta ta ɗauki cokalin ta fara tsakurar abincin. A sace ta kalli Hamdeeya cikin raɗa tace “Ina su Hadeeya?”
Nuna mata wani ɗakin ta yi dake nan ƙasa tace “Suna ɗakin Yaya Mu’awwaz.”
Wani irin faɗuwar gaba ta ji ya ziyarceta, da sauri ta ƙwalalo ido tace “Me suke yi?”
Taɓe baki ta yi tace “Ni ma ban sani ba.”
Ɗaga idonta tayi da niyyar kallon Alhaji Auwal, sai kuma idonta suka sauka cikin na Mu’az da ya rumgume hannaye ya na kallon duk wani motsinta, shi da ma saboda ita ya tsaya wurin ba dan ya ci abinci ba, wani irin kallo ne ya ke mata ya na jin shi dai kawai birgeshi ta yi lokaci ɗaya ba dan kyanta ko nasabarta ba. Suna haɗa ido ya sakar mata murmushi cike da tsokana yace “Za ki ci abincin? Ko na ɗura miki?”
Ɗan waro ido tayi da mamakin rashin kunyarshi, sai kuma ta ɗauke kai ta sake kallon Alhaji za ta nemi izininshi, kafin ta yi magana Mu’az ya sake faɗin “Abba.”
“Na’am.” Ya faɗa yana maida kallonshi ga gareshi, Mu’az kuma Saleema ya ƙurawa ido ba tare da yanayi na wasa a tare da shi ba yace “Na ce ko ka yi wa ƴarka miji ne?”
Shi da Hajia Rabi tare suka saki murmushi suna kallon Saleema, inda amarya ta yatsina fuska ta kalli Mu’az ɗin ta na ganin me ye na wannan tambayar? Sam a ganinta bai ma kamata a ce Mu’az ya yi wannan tunanin akan wannan yarinyar ba, dan ta na da labarin rashin iliminta da wayewarta, yatsina baki tayi tana kallon Alhajin da yake faɗin “A’a, me ya sa ka tambaya aboki? Ko dai ƴar ta wa ta sace tsoka ma fi mahimlanci ne a jikinka?”
Wata ƴar dariya yayi ya sunkuyar da kai sai kuma ya ɗago yace “Ni dai Abba idan ba ka mata miji ba, to ku taimaka min kar na ƙara zama tuzuru a gidan nan, idan shekarar nan ta wyce ban yi aure ba gallabarku zan yi.”
Saleema da ta yi mutuwar zaune da ido kawai ta ke binshi kamar wani sabuwar halitta ne ta gani, Alhaji Auwal kuma dariya kawai ya ke sai Hajia Rabi da ta ɗan dakeshi a kafaɗa tace” Marar kunya kawai, me za ka yi to?”
Saleema ya kalla ido cikin ido ba tare da shayin komai ba yace” Ba zan bari ta zama ta kowa ba, zan mayar da ita mallakina ko ba ta so.”
Yanzu kam da ke ranta ya gama ɓaci na takaicin bawan Allahn nan, zabura ta yi ta miƙe da sauri ta nufi hanyar madafa, dan gani take idan sama za ta hau za ta jima ba ta kai ba, da kallo duk suka bita har ta ɓacewa ganinsu, cike da izgili da raini amarya ta kalli Mu’az tace “Wannan yarinyar fa ba ajinka ba ce, ba ta da ilimi sannan ga ta ƴar ƙauye, ka nemi dai-dai da kai mana.”
Kallonta yayi irin kallon nan na nidai ban saka bakinki ba, sannan ki min shiru ko ki ji ba daɗi, ya mata wannan gargaɗin da ido ne dan kar ta hassala shi ya faɗa mata magana Abbanshi ya ce ya rainata, dan haka yake so ta masa shiru kawai. Fahimtar kallon yasa ta ɗauke kai ta na sake yatsina baki da tunanin “Ita ina ma za ta yarda Mu’awwaz ya ɗauko mata ajawo irin yarinyar can?”
Da haka ma ta yanke shawarar tunkarar lahaifiyar yarinyar da maganar, dan ta san su ɗin amare na musamman ne, idan suka yanke hukuncin to mazan za su ce ya yanku ne kawai.
Alhaji Auwal da farin cikin hakan ya kamashi kallon Mu’az ya yi yace” Karka damu aboki, indai da gaske kake ka shirya za mu je wajen mahaifinta sai mu nemo aurenta.”
Cikin jin daɗi Mu’az ya ba wa mahaifin na shi hannu suka tafa yana faɗin” Yawwa aboki, na ji daɗi, idan mukayi sa’a ma ya amince nan kawai za ta zauna sai dai na mata lefe da gado.”
Dungure masa kai Hajia Rabi tayi tace” Sheɗani, wato ba za ka bata damar sallama da iyayenta ba kenan?”
Sosa ƙeya yayi yace” Wane sallama kuma Mama bayan ga waya? Ta je daga bayan idan ta gama jego.”
Buɗe baki Hajia tayi da mamaki da kuma kunyar maganar sa, Alhaji Auwal na dariya yace” Abokina da alama yanzu kam ƴar manuniya ta fara azalzalarka ka yi aure ko?”
Bushewa sukayi da dariya shi da Mu’az sai Hajia Rabi da ta miƙe tana faɗin” Allah ya shiryaku shirin addinin musulunci.”
Saleema kuma na shiga madafa ta samu mai aikin nan tana wanke-wanke, a hankali ta rage saurin da ta shigo da shi na bala’i da gwaramar da bawan can ke haɗa mata da bata san dalili ba ta fara takawa har zuwa kusa da ita tana kallonta, ƙarara tsoro ya bayyana a matashiyar kamar za ta arta a guje, saida ta samu tabbacin yarinyar da ta gani jiya ce sannan ta shiga ƙare lata kallo daga sama zuwa ƙasa.
Bayan abubuwan nan da ita ma Allah ya hore mata guda biyu, wata cikakken ƙirji da mazaunai ba ta ga wani abu da yarinyar ke da shi da za ta birge Mu’awwaz da ake ikrarin na da tsantseni da ƙyanƙyami ba, numfashi kawai ta sauke da ta tuna wa’azizzika da take saurare da suke magana kan mata da miji, ita kam ta san akwai wani babban tasiri da magana-ɗisu dake da tasiri a jikin namiji wanda a jikin mace kaɗai ake samunsu, dan abun ya girmi tunani ka ga ma’aurata sun yi faɗa baja-baja da rana, amma da dare ya yi su sulhunta kansu, musamman ma namiji da shi ya fi fara neman sulhun. Ko shakka ba ta yi cewa wannan yarinyar ma Allah kaɗai ya san BAIWAR da ke tattare da ita da ya sa har ta ɗauki hankalin Mu’awwaz, yaro ɗan ƙwalisa, ga kyau ga nasaba ga kuɗi da ilimi.