Baiwata

BAIWATA 11

Lura da kamar ta na tsoron Saleema ya sa ta sakin murmushi tace “Me ye sunanki?”

Da sauri ta ɗago ta kalleta ido har sun cika da ƙwalla tace “Hajia dan Allah ki yi haƙuri, ka da ki tona min asiri, wallahi ba laifina ba ne.”

Cike da raha Saleema tace “Sunanki fa kawai na tambaya, amsa ce mai sauƙi.”

Marairaicewa tayi tace ” Nafissa.”

Kallon tsanake ta mata tace “Nafissa, ba ki san cewa ke mace ba ce? Abinda ki ka aikata jiya zai iya zama silar rugujewar duka zuri’arki, wannan abun da ki ka bashi ba tare da aure ba, shi ɗin dai shi ne mutumcinki da za ki yi tutiya da shi, me ya sa kika bayar da shi a arha haka?”

Sunkuyar da kai ta fara yi cike da nadamar rayuwarta da kuma dana-sani, cikin kukan da ba shi da anfani a yanzun tace”…

Alhamdulillah.

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button