BAIWATA 2

Tsakanin mata da miji dama aka ce sai Allah, damuwa da hakanyasa shi dawowa gidan bayan ya tabbatar yaran na makaranta kuma Ardayi na wajen aikinta, a d’aki ya sameta kwance da alamar bata jin dad’in jikinta, k’arasawa yayi ya zauna kusa da ita yana kallon kyakyawar fuskarta wacce tana d’aya daga cikin abinda yasa har yau yake tare da ita da kyautatawa.
Hannu ya kai ya tab’a wuyanta yace “Me yake damunki ne?”
A hankali ta yunk’ura ta gyara zamanta kafin tace “Ba komai.”
Da sauri ya fuskanceta sosai ya rik’o hannunta yace “Safiya hushi kike da ni akan abinda ya faru? Kiyi hak’uri kinji, b’acin rai ne ya sa da kula son da nake ma Saleema, ina so na ga ita ma ta zama kamar ‘yan uwanta, shiyasa kika ga ina haka.”
A tausashe ya d’an fara lumshe ido ya kwanto da ita jikinshi cikin muryar da ta fahimci kan zancen yace” Kiyi hak’uri kinji Sofee.”
D’an murmushi tayi ta d’ago daga jikinshi za ta yi magana, sai kuma ta yi saurin rufe bakinta saboda aman da ya tuk’ota, da sauri ta sake toshe bakin tana had’eshi gudun kwafsawa, cike da kulawa ya kalleta yace” Oh! Baki da lafiya ne? Me yake damunki ne?”
Sunkuyar da kai tayi cike da kunya ta girgiza kai, d’an kawar da kai yayi a ranshi yana mamakin kunya irin ta Safiya, shekara goma sha d’aya da aure amma har yau kunyarshi take, shi ba zai iya tuna ranar da ta nuna mishi buk’atarta ba sai dai ya karanta a tsakiyar idonta ko daga jin sautin muryarta, hakan na birgeshi matuk’a a game da ita, sai dai kuma a matsayinsu na ma’aurata yana so ya ga tana komai b’aro b’aro, duk da dai hakan ba wata matsala ba ce dan kunyar tana taimakonshi sosai. Sake kallonta ya sake yi yace “Safiyyyyya.”
Yanda ya ja sunan na ta ya sa ta d’agowa ta kalleshi, da murmushi a fuskarshi yace “Ko dai ciki gareki?”
Da sauri ta rufe fuskarta ta sake duk’ar da kanta tana ji kamar ta nutse k’asa, cike da farin ciki ya jawota jikinshi yana fad’in “Masha Allah Sofee na, dama kullum addu’ata Allah yasa ke ce za ki haifa min auta a gidan nan, kin san na fad’a muku yara shida na ke da buk’ata a rayuwata, idan ma zan samu k’ari to kar su wuce bakwai.”
Ita dai rufe fuskarta tayi da da rigarshi tana mamakin tsari irin na shi, in banda abun shi ko wa ya fad’a masaana wa Ubangiji iyaka? Wato shi ne ma zai k’ayyade yaran da yake so ya haifa a duniya.
D’agota yayi yana lek’a fuskarta yace” Amma dai ki shirya mu je asibiti dan a duba lafiyarku, bana so na rasa wannan Safiya kamar yanda na rasa sauran.”
Narai narai tayi da manyan idonta tace” Bana tunanin wannan ma zai tsaya, kamar sauran shima na san zai tafi ne.”
Girgiza kai yayi yace” A’a ki daina fad’in haka, in sha Allah za ki haifeshi. “
Kamar za ta fashe da kuka ta kalleshi tace” Abban Hajia shida fa, shida na samu duka suna zubewa, har hutu aka bani ko hakan zai sa a dace amma har yanzu shiru.”
Cike da jimami da tausaya mata ya k’ara rumgumeta a jikinshi yana rarrashinta, kasancewar d’akin a bud’e take yasa Saleema da ta taso daga islamiyya shigowa kan ta tsaye ba tare da tunanin za ta samu mahaifinta a d’akin ba duba da kwana uku kenan ma ko magana ba ta ga sunayi da mahaifin na ta ba, sai dai tana ganinshi ta zabura ta juya za ta koma waje, inda Safiya ma ta firgita da sauri ta mik’e daga jikinshi tana son matsawa nesa da shi, da mamaki ya kalli uwar ya kuma kalli ‘yar, sai ya rasa duk me ye haka d’in? Kamar wani wanda aka kamada wata matar? Da fa Ardayi ce ba ruwanta, hasalima ita har kayan baccin take sakawa kuma a gaban yaran, idan ta kama ma har rumgumeshi za ta fara yi a hakan kuma a gabansu, a ganinsu dai ai iyalinsu ne ba komai.
Alhamdulillah.