BAIWATA 3

Bismillahir rahamanir rahim
_3_
Cikin ladabi Safiya ta kalleshi tace “Abban Hajia.”
“Na’am.” Ya amsa yana kallonta, ci gaba ta yi da cewa “Dama Saleema ce take fad’a min wai tana son shiga koyon d’inki, ka san nan kusa da mu akwai wata dake koyawa mata d’inki.”
Murmushi ta saki a fuskarta ta ci gaba da fad’in “Na fad’a mata ta yi yarinta dayawa, amma kuma na ga tana da k’ok’ari wajen yin d’inki, dan kullum da abubuwan take fama a gidan nan.”
Aje cokalin da yake cin abinci ya yi ya kalleta sosai yace “Safiya, gaba d’aya alamu nuna min suke ke kike hana yarinyar nan maida hankali kan karatunta, ‘yata ta cikina ta yi d’inki? D’inki fa ?”
Girgiza kai yayi dake nuna abun ya ma bashi dariya yace “A tarihin gidanmu ko mai siyar da sutura babu, ta ya zan bar yata ta fara koyon d’inki?”
Kallonta yayi da kyau yace “Kina ji na? Saleema idan har ba ta fito min a matsayin babbar likitar mata ba to ta zo min a matsayin wata engineer ko babbar ‘yar jarida, idan fa hakan ya gagara ne zan so ta zama hazik’ar mace a cikin siyasa.”
Kallon Hadeeya yayi dake cin abinci yace “Me kike so ki zama a rayuwa?”
Cike da iyayi ta waina idonta kafin tace “Abba, ni dai gaskiya irin aikin Momy nake so, irin yanda take shigarta idan za ta tafi, da jajircewarta a kan aiki yana birgeni sosai.”
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa ya kalli Hameeda yace “Ke kuma fa yar Abba?”
Cike da yarinta tace “Abba, ni dai so nake na yi dogon karatu akan harkar tattalin arziki.”
Cike da jin dad’i ya jinjina kai har da murmusawa yace “Da kyau ‘yata, wannan shi ne abinda ya kamata.”
Hamdeeya ya kalla da fara’ a yace “Autata dai na san bata da matsala ko?”
Cike da k’uruciya Hamdeeya tace “Abba ni dai malama zan zama.”
Dariya yayi yace “Hakan ma burine mai kyau.”
Kallon Ardayi yayi wacce duk abun nan da ake hankalinta na kan wayarta yace “Masoyiyata kin ji fa, dan haka sai ki k’ara zage damtse.”
D’an murmushin yak’e tayi dan hankalinta ba nan yake ba tace “Dole mana, kar ka damu masoyi.”
Sai lokacin ya sake kallon Safiya dake ta kallonshi da mamaki yace “Kin dai ji, dan haka ke ma idan za ki d’ora ta a turbar da ta dace ki fara tun yanzu, amma bana son maganar shirmen banza da wofi.”
Bayan kwana biyu
Hannunta ya kamo suna shigowa d’akin ya kalli Safiya dake gyara gadonta yace “Yanzu wannan shirin da shi za mu tafi da ita? Baki ga yanda yan uwanta suka shirya ba?”
Juyowa tayi tana kallonshi sai kuma ta kalli shirin jikin Saleema, doguwar riga ce ta shadda jikinta mai kwalliya sai hijab da ya dace da kayan tare da takalminta masu kyau da tsada, sake kallonshi tayi tace” Me ye aibun shirinta?”
D’an gajeran tsaki yayi yace” Kin wani saka mata manyan kaya, baki ga na yan uwanta bane?”
D’an kawar da kai tayi tace” Ka yi hak’uri, amma gaskiya bana sha’awar koyawa yarinyata fitar da tsiraici tun tana k’arama, gwara ta san hijab shine rufin sirrinta.”
Cikin jin haushi yace” Ke da anyi magana sai ki nuna kin fi kowa tsoron Allah, to wannan ‘yar abar wani ne zai yi sha’awarta ? Ina ma abun yake a nan?”
Wani tsaki ya sake yi yace” Kinga dan Allah d’auko min wasu kayan na canza mata idan ke ba zaki iya ba.”
Jinjina kai tayi ba yanda za ta yi ta d’auko mishi riga ta kanti ta kawo, da kanshi ya fara k’ok’arin taimakawa Saleema, hakan yasa ta fara kakkare jikinta cike da kunya saboda rashin sabo, yana gama taimaka mata ta saka kayan ya kama hannunta za su fita, da sauri ta kalleshi tace “Abba hijabina?”
Harara ya wurga mata yace “Dallah muje malama.”
Haka ya ja hannunta suka fice a gidan tana ta jin ta wata iri ba yanda ta saba fita ba. Wajen taron ma da suka isa kasa sakewa ta yi har matar abokin na shi wacce take murnar shagalin k’arin shekarar d’aya daga cikin yaranta ta masa magana ko me yake damunta, cike da takaicin halin k’auyenci da dabbanci a ganinshi na Saleema yace “Ba komai, iskanci ne kawai.”
Dan a ganinshi k’auyenci ne duba da yan uwanta da sauran yaran yanda suka sake cikin yara yan uwansu suna ta tik’ar rawa dalilin k’aton redion da aka saka musu, sai ita da ba ta waye ba za ta wani had’e wuri d’aya kamar mai jin mugun sanyi.
Dawowarsu ke da wuya ya samu kiran waya daga malamin Saleema, dan ba ya kirashi da malaminsu duka ba saboda su Hadeeya sai sun ga dama suke zuwa makarantar islamiyya, Saleema ce dai babu abinda ke hanata zuwa dan ba ciwo ba, bayan sun gaisa a tsanake da mutumtawa malamin ke fad’a masa “Alhaji dama akan Saleema ne, shiyasa na ce bari na kira muyi magana.”
Gabanshi ne ya fad’i dan abu d’aya tunaninshi ya bashi, wato a islamiyar ma bata gane komai? A nutse malamin ya d’ora da “Dama Saleema na d’aya daga cikin hazik’an yara a islamiyar nan, kuma abun birgewa yanda take da matuk’ar fahimta akan ilimin hadith, to dama akwai lokacin da aka ware ga maye da suke d’aukar karatun hadith, shine nake neman alfarma ko za’a lamunce mata sai ta dinga zuwa lokacin da za’a yi darasin? Zai zama idan an tashi k’arfe sha biyu na rana ita ba za ta koma gida ba za su wuce ajin d’aukar hadith, k’arfe d’aya da rabi sai a sallamesu.”
Shiru Alhaji Yusuf ya yi yana tunanin abinda malamin ya fad’a, sai shed’an ke raya masa to dama tana gane karatun islamiya na boko ne ba ta ganewa? Sai kawai zuciyarshi ta raya mishi ai da gangan ne ta ke k’in aje hankalin a boko, tunda gashi tana gane hadith. Jinjina kai kawai ya yi yace “Shikenan.”
Ya kashe wayar da tunanin matakin da zai d’auka, har ya yanke hukunci bai sanar da kowa abinda zuciyarsa ta yanke masa ba, yana jiran lokaci yayi ya zartar kawai kowa ya gani ya kuma sani.
*Washe gari*
Ganin ta dawo da kuka yasa ta tarbeta cike da kulawa tana tambayarta “Saleema, me ya faru ? Wa ya dakeki?”
D’aga kanta tayi tace “Abba ne a waje yace wai na dawo, kuma wai daga yau ba zan sake zuwa makarantar ba.”
Da mamaki sosai a fuskarta tace “Ban gane ba za ki sake zuwa ba? Me kika masa?”
Cikin kuka tace “Nima ban sani ba, kawai koroni yayi.”
Numfashi ta sauke tana ji akwai dai wani abun, amma haka kawai ba zai hanata zuwa makaranta ba, nuna mata gado tayi tace “Zauna nan, bari na je na ji me ki ka yi.”
Za ta fice a d’akin Saleema tace “Mama idan ya ce wani abu na masa ki bashi hak’uri dan Allah.”
Murmushi ta sakar mata sannan ta fice a d’akin, a farfajiyar ta sameshi zaune da na’urarsa yana dannawa, kujerar gefenshi ta ja ta zauna a nutse tace “Abban Hajia, ta sameni yanzu take fad’a min wai ka hanata zuwa islamiya, shine na ce na san dai wani laifin ta yi ko?”
Ba tare da ya kalleta ba fuska a d’aure yace “Ba ta yi laifi ba, kawai dai na soke zuwa makarantar ne, ba kuma ita kad’ai ba har da yan uwanta.”
Hankali tashe zuciyarta a kid’ime ta furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un!”
Da sauri ya juyo yana kallon da tunanin me ye na salatin? A razane tace “Alhaji, islamiyar fa ka ce ka dakatar da zuwa?”
A k’ufule yace “Haka na fad’a Safiya, ko kina da ja ne?”
Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tace “Me ya yi zafi haka? Islamiya?”
Mik’ewa yayi a hassale ya d’auki wayarshi da na’urar sannan ya kalleta yace “Na riga da na gama yanke hukunci, na kula wannan karatun ne ya ke d’auke mata hankali tana kasa fahimtar wanda nake so ta fahimta, shiyasa na ciresu gaba d’ayansu dan hankalinsu ya tsaya wuri d’aya.”