Baiwata

BAIWATA 3

Mik’ewa tayi tsaye tace “U’uzubillah! Alhaji ka san me kake shirin aikatawa kuwa? Kai tsaye fa kamar kana k’ok’arin ingiza yaranka ne ga mummunar hanyar da ba zata b’illar da su ko ina ba sai halaka.”

Cike da shashantar da zancen ya kalleta sama da k’asa yace “Allah ko?”

Sai kuma ya ja tsaki ya wuce ya barta tsaye yana fad’in “A ganinki kenan.”

Da kallo ta bishi tana jin yanda hankalinta ke sake tashi dan gaskiya wannan babban bala’i neke tunkarosu, islamiya ? Inda za’a koya wa yaran sanin ubangijinsu? Shi ne zai tsigesu saboda karatun da anfaninsa iya duniya ne kawai, shi ma a haka ba kowa da yayi shi ke morarshi ba.

Kamar wasa sai kuwa maganar nan ta zama babba, Safiya da abun ya dameta ta yi iya k’ok’arinta wajen sake tuntub’arshi, amma a k’arshe mummunan kashedi ya kirta mata cewa zai d’auki tsatsauran matakin da ya dace a kan ta idan ta sake mishi maganar nan, hakn yasa ta tuntub’i wanda take ganin sun isa su fad’a masa su ji.

Duk shekarun da suka d’auka haka ba ta tab’a faruwa ba, amma sai dayawa suke ganin laifinta dan su ma bokon suka sha suka k’oshi, dan haka suke ganin me ye a ciki to? Abinda yake ganin ya fi mishi ne ya yi sai su zuba mishi ido, wannan tashin hankalin da zulumin da ta shiga na tsawon sati biyu ya haddasa mata rashin cin abinci da muguwar damuwar da ta kwantar da ita rashin lafiya, wanda daga k’arshe cikin jikinta ya zube a wata asuba ta idar da sallah.

Kamar kowane lokaci idan haka ta faru asibiti ya kaita aka mata wankin ciki, daga bisani lokitocin suka basu shawarar ko dai za’a juyar da mahaifarta ne saboda tana daf da kaiwa matakin da hakan zai iya cutar da ita, amma sam Alhaji Yusuf ya ce bai yarda dan gaskiya har yanzu ya na so ya ga wani sabon jaririn daga wajen Safiya, saboda mata ce da ba ya shakka ko k’yamar sake had’a zuri’a da ita, haka kuma ya yi bak’in cikin rasa wannan cikin da yake ganin har ya wuce wata uku amma gashi shi ma ya tafi, karo na bakwai kenan.

SHEKARA D’AYA

Hankali tashe ta k’araso wajen mai gadin tana fad’in “Sani dan Allah ba ka ga in da Saleema ta yi ba?”

A ladabce ya girgiza kai yace “Tun d’azu data fita dai nan ta yi…” Ya nuna mata hannunshi na dama ya d’ora da “To kuma ban ga dawowarta ba har yanzu.”

Cike da d’imuwa tace “To ka ga dan Allah ka daure ka duba min ita a shagon nan na bayanmu, nan na aiketa ta siyo min madara ga shi har yanzu ba ta dawowa ba, ina tsoron kar wani abun ne ya sameta.”

Cike da son kwantar mata da hankali yace “A’a in sha Allah ma ba abin da ya faru, bari na dubo na gani.”

Cikin damuwa ta amsa da “Yawwa nago…”

Mak’alewa sauran maganar ta yi sakamakon tsayawar motar Alhaji Yusuf a k’ofar gidan, da sauri ta dawo cikin gida ta tunkari komawa falo, ba wai dan babu hijabi a jikinta ba ko tana tunanin ranshi ya b’ace kan tana magana da mai gadin shi, sam wannan ba ya a tsarinshi dama, hasalima da kan shi yake fita tare da su ya zab’ar musu kalar mayafan da yake so su saka. Tashin hankalin shine aikin da ya saka ta yi masa ba ta kammala ba gashi har ya dawo, shi kuma mutum ne da baya son wasa da cikinshi, duk yanda yake girmamaka indai za kai masa wasa da cikinshi to za ku samu matsala, dalilin da yasa kenan ko Ardayi na wajen aikinta ya kan umarceta ta sarrafa mi shi wani abun, dan baya son cin komai a waje.

Tun ba ta gama shigewa falon ba muryarshi ta dakatar da ita sanda yake fad’in “Me kike nema a waje?”

Cak ta tsaya tare da juyowa a hankali tana kallonshi har ya k’araso, zagaya hannunshi yayi ta k’ugunta ya jawota jikinshi yana kallon kyakyawar fuskarta da ta firgice da tsoro, d’an jaye jikinta tayi kad’an saboda k’ofar falon bud’e take, kuma mai aiki da su Hadeeya na nan zaune suna aiki, sannan ga mai gadi dake rufe k’ofar wanda shi ma zai iya hangosu.

Jin ba ta ce komai ba yasa shi sake fad’in “Je t’écoute (ina saurarenki).”

A duburbuce ta fara fad’in “Dama… Sani ne na ce ya d..uba min Sal…eema waje.”

Kallon tuhuma ya mata yace “Ina Saleemar ta je?”

Hannunta ta kai ga wuyanta ta d’an shafo tace “Aiken ta na yi nan baya ta siyo min madara, …shi ne fa…har yanzu ba ta..dawo ba.”

Da mamaki a fuskarshi ya sake k’ura mata ido ya ja baya kad’an yace “Hajiar ta wa kika aika waje?”

Marairaicewa tayi tace “Ka yi hak’uri dan Allah.”

A tsawace yace “Na yi hak’urin me? Ban fad’a muku kar wacce ta tura min yara waje ba idan ba makaranta za su tafi ba?”

Kamar za ta fashe da kuka ta sake fad’in “Ka yi hak’uri, ka kira ka ce na maka kunun madara ne, sai da na duba na ga babu madara a mangaza, kuma na fad’a maka amma ka manta, shine…”

A hassale ya sake fad’in “Shi ne kika aika min yarinya waje a wannan ranar? Ina mai aikin gidan take?”

A ladabce tace “Ka san yau girkin Ardayi ne, tana mata girki ne tunda ita tana wajen aiki.”

A tsawace yace “To mai gadi fa? Shi ba mutum ba ne ?”

A sanyaye tace “To ai kai ka fad’a mana mai gadi iya aikinshi gadi ne kawai, kar wacce ta mishi aiken da zai sa ya bar bakin k’ofa.”

Nunata yayi da yatsa yace “Wallahi idan wani abu ya samu ‘yata kan ki zan huce.”

Baki wangale tace “Kai na kuma? Dan na aike ta?”

Jinjna kai yayi yace “Kina wasa kenan?”

Saleema ce ta shigo gidan rik’e da leda a hannu sai Sani mai gadi a bayanta, da sauri suka nufeta in da Alhaji Yusuf ke duba duka jikinta yana fad’in “Uwata ba abinda ya sameki ko?”

Da mamaki Saleema ta kalleshi ta girgiza kai a hankali tace “A’a Abba.”

“To me ya tsayar da ke?” Cewar Safiya na kallonta da kyau, sunkuyar da kai tayi tana rarraba ido, Sani ya kalla yace “Ina ka ganta?”

Cikin ladabi yace “Wani gida ne nan kusa da shagon da aka aiketa ta shiga shan ruwa.”

Da mamaki Alhaji Yusuf ya kalli Saleema yace “…

Alhamdulillah.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button