BAIWATA 5

A tsawace yace “Kin ji me na fad’a?” Da sauri ta d’aga kai alamar e, nuna mata k’ofa ya yi yace “Wuce.”
Juyawa ta yi jiki a sab’ule ta fita a d’akin ta na jin ba dad’i sam, saboda burinta ne ake neman hanata cimma shi, amma ya zata yi da ya wuce ta hak’ura kawai.
Tafiya ta yi nisa, amma har yanzu babu abinda ya canza daga rayuwar su, islamiya sun cire rai da sake komawa, saidai Saleema dake mai wayo ce har yanzu ta na d’aukar karatunta wajen kanwar malaminsu, wanda a shekarun nan ta k’ara sanin abubuwa dayawa, musamman da yanzu ta k’ara wayo da shekaru, sai ya zama har wayar mahaifiyarta take d’auka ta kira malamin su sake tattaunawa kan karatunta. A karatunta na boko ma har yanzu ba abinda ya sauya, duk yanda take son ta birge mahaifinsu ita ma wajen ganin ta yi k’ok’ari abun ya ci tura, sai ma k’ara lalacewa da lamarin ke yi saboda ta hak’ura ta d’auke hankalinta daga karatun na boko, tana yi ne kawai ba dan ranta na so ba sai dan mahaifinsu, hakan ya sa shekara biyu ta na maimaita wani ajin har Hadeeya ta risketa, shima kuma sai Hadeeyar ta yi gaba tana neman barinta, abinda Alhaji Yusuf bai tab’a yi bane ya yi a wannan karan, wato bayar da cin hanci da kuma neman alfarma aka izasu tare da Hadeeya dan baya so ta barta a nan.
Yanzu dai haka suna ajin zana jarabawar BEPC, ya ma ta k’wak’waran kashedi in har ba ta ci jarabawar nan ba to shi kad’ai ya san me zai mata, hakan yasa ta d’an sake maida hankalinta ta na son ganin bai mata abinda ya bar wa ran na shi ba, sai daia inda ta koyi abun a nan take tashi ta barshi, ta na shiga d’aki za ta nemeshi ta rasa.
Farkawa ta yi don yin fitsarin da ya addabeta, ta na tashi zaune idonta suka sauka kan Mamanta ta d’ora goshinta k’asa ta na kai kukanta ga sarkin sarakuna mai kowa mai komai, da alama ba ta kwanta ba kenan tun da suka rabu da sai da safe, dama kuma idan ba kwanan Mamanta ba ne d’akinta take kwana dan ta fi jin dad’in hakan. Sauko da k’afafunta ta yi ta na ci gaba da kallon mahaifiyarta wacce ta ke da yak’inin ita kawai take wa addu’a, dan watannin nan ta cika saka damuwa a kan ta wanda ba ta san dalili ba, haka kuma da ta ga tana yawan tsayuwar dare da azumin nafila sai ta ce ta na yi ne saboda ta na so ta yi nasara a karatunta ita ma mahaifinta ya yi alfahari da ita.
Mik’ewa ta yi ta shiga ban d’akin ta yi abinda za ta yi ta fito, zaune ta sake yi bakin gadon ta na kallon mamanta da sai yanzu kad’ai ta d’aga. Bayan wasu mintuna ta sallame sallar dan ta ji me ya sa Saleema ba ta koma ta kwanta ba? Kallonta ta yi murya a tausashe sosai saboda daren da ya tsala yace “Lafiya ba ki koma ki ka kwanta ba?”
Numfashi sosai Saleema ta ja kafin tace “Mama, ki kwanta ki huta mana, gobe za mu fara jarabawar, idan Allah ya k’addara zan samu zan samu.”
Ajiyar zuciya Mamanta ta sauke ta na d’an murmushi na dattako tace “Ko da kun gama jarabawa Saleema ba zan daina yi miki addu’a ba, ina so na ga kema mahaifinki ya baki kyauta ko sau d’aya ne.”
Girgiza kai Saleema ta yi tace “Mama, wai me yasa ni Abba ba ya so na ne? Saboda ba na da k’ok’ari a makaranta?”
Girgiza kai Mamanta ta yi tace “Ba haka bane, ya na so dai ya ga ke ma kina k’ok’ari ne.”
Cike da damuwa a fuskarta tace “To amma Mama ilimi ba na Allah bane? Na yi iya k’ok’arina dan ganin nima na zama kamar su Hadeeya, amma abun ya gagara.”
Cike da gasgatawa maman tace “Hakane Saleema, ilimi na Allah kula ya na ba wa wanda ya so, amma wasu lokutan idan ka sa wasa sai Allah ya bar ka da shirmenka.”
Da tuhumammen kallo ta bita tace “Mama kina ganin ni ba na jajircewa ne? Ina fa k’ok’ari sosai, kawai dai abunda na sani na fi son karatun islamiyya saboda shi na fi ganewa a sauk’ak’e.”
Murmushi ta sake yi cike da dattako tace “To shikenan, Allah dai ya bamu nasara wannan karan.”
“Ameen Mama, zo ki kwanta to.” Girgiza kai ta yi tace “A’ a, ke ki je ki kwanta, ni zan ci gaba daga in da na tsaya.”
Ita ma girgiza kai ta yi tace “A’a, ni ma bari in tayaki, ba zan iya bacci ba alhalin ki na tsaye a kaina.”
D’an murmushi ta sake yi ta mik’e tsaye dan ci gaba daga in da ta tsaya, ba jimawa Saleema ta fito bayan ta d’auro alwala ta zo ta shinfid’a sallaya ita ma ta bi sahu a gefen mahaifiyarta.
Saboda comment d’in da ku ke suburbud’awa🥰🥰 ga mai so ta yi magana dan shiga grp d’ina
Alhamdulillah.