BAIWATA 6

_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA G
*AHALINA
GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.) 🤜🤛
(Burinmu d’aga muryoyinmu sama domin anfanar da al’umma had’e da ciyar da adabin hausa.)
☆ [G. M. N. A] ☆ 📖🖊️
Bismillahir rahamanir rahim
_6_
12:20 suka fito daga aji sun gama zana jarabawarsu, ranar da ake kwantsamawa ya sa ta nufi inda ke da ruwa dan sha ko ta ji sanyi saboda kakarewar da jarabawar ta mata a aji, dama dai ita ba wasu k’awaye gareta ba, to ta ya ma za su yi k’awaye? Bayan mahaifinsu ba kowace k’awa ya ke barinsu da ita ba sai mai ilimi irin na su, idan kuma ba ki da to ko kin zo wajensu zai sa mai gadi ya hanasu shiga, hakan ya sa ma tsakaninta da k’awa makaranta a gaisa a yi raha kawai a wuce wurin, ita ba waya gareta ba duk da shekarunta goma sha takwas a duniya, amma mahaifinta ya hana mata waya ya ce a haka za ta ji haushi ta yi k’ok’ari ita ma saboda ya ga yanda waya ke da tasiri a rayuwar matasan yanzu, hakan yasa ya siya ma su Hadeeya manyan wayoyi uta da Hameeda amma ban da ita, wai a dole sai ta ji haushi, amma abunda bai sani ba shi ne ko a jikinta, tunda dai ta na aiki da ta Mamanta ai shikenan.
Ta na zuwa gaban fanfon sai da ta aje yar jakarta k’arama sannan ta cire hijabinta ta zauna bakin dandamalin ta fara d’aura alwala, a iya saninta da ganinta dai ba kowa wajen, dan haka ma ta dinga alwalarta a tsanake har da ture d’an kwalinta ta shafa kai.
Ta na idawa ta mik’e ta na karkad’e hijabin na ta da ya d’auki lemar ruwa, a cikin karkad’eshin da take ne ta d’an juyo da kan ta kad’an. Kwatsam idonta su ka sark’e da na balagaggen namijin da ba ta tsammaci ya na wurin ba, da mugun sauri ta durmiya hijabinta ta juya bayanta cike da mad’aukakiyar kunyar da ta kasa misaltawa, gaban Mamanta kad’ai ta ke iya zama da yar rigar nan da ke jikinta, gashi yau ta yi saken da waccen Alhudahuda ya gama kalle mata jiki.
Da k’yar ta sunkuya ta d’auki jakarta ba tare da ta yarda ta sake kallon wajen ba, dan irin kallon da ta ga ya na mata abun ya bata tsoro, gashi ta na jin kunyarshi sosai, saboda wasu lokuta ana turoshi ajinsu ya kula da su idan babu malami, dalilinta na kiranshi alhudahuda kuma shi ne irin darasin da yake koya musu na lissafi mai matuk’ar wuya, hakan ya sa da an turoshi ajin za ka ga yan mata da samari kowa na kawo masa rub’abb’en lissafin da ya kakare masa a kwanya dan ya warware masa. Ita kam tsakaninta da shi ido ne shi ma a akasi idan sun sark’e, kamar yanda ba ta damu da shiga abinda bai shafeta ba, haka ta kula shi ma ba ya shiga sabgar da ba’a saka da shi ba, dalilin da yasa kenan ko sannu ba ta tab’a had’asu ba, kuma ta ji ma an ce shi ne shugaban matasa na makarantar.
Sum sum sum! Ta nufo hanyar wucewa wacce dole ta gefenshi za ta ratsa ta wuce, hakan yasa ta k’ara sadda kanta k’asa dan ba ta so su had’a ido, sai da ta zo daf da shi har ta d’an wuce kad’an Huzeifa da ya shiga halin d’imuwa da tashin hankalin da bai tab’a riskar kanshi ba ya yi k’arfin halin d’an matsawa kad’an da tunanin kar ta k’arasa warware masa alwalarsa ya na ambaton “A’uzubillah!”
Duk da ba ta tsaya ba amma sai da ta saci kallonshi ta gefen ido da son gano me ya ke wa a’uziyya? Ido suka sake had’awa dan shi mamakinshi bai wuce “Wai dama haka ta ke a cikin dogon hijabin nan?” Ba, shi ya na ganinta ba ruwanta ashe bama-bamai ne a cikin hijabi, tsakani da Allah da Annabi ya d’auro alwalawarsa ya zo da niyyar d’an tab’a karatu kafin 12:30 ta yi ya yi sallah, sai kawai ya wani sameta zigidir haka daga ita sai siket da k’aramar riga, anya kuwa ta san halin da ta sakashi a ciki? Shi fa idan ka cire matan banza da ya ke gani a tv wanda ya ke iya k’ok’arinshi wajen ganin ya kare kanshi daga kallonsu, da kuma ko da ya kallesu ba abinda yake ji, shi bai tab’a ganin irin haka ba, k’annan shi ma mummunan kashedi ya kirta musu kan zama haka a cikin gida. Yanzu ga shi yarinyar da ko sunanta bai sani ba ta gayyato masa da wata larurar da bai san ya na da ita ba.
Wannan kallon mamakin da Saleema ta hango a k’wayar idon shi ya sa ta tunanin ko dai ji yake shi ma malaminsu ne ? Nufinshi kuma ta gaisheshi? Sai kawai zuciyarta ta raya mata ai ba komai ba ne, gaishe shi ya ci albarkacin malaman. D’an tsayawa ta yi ta sake kallon inda ya ke amma ba ta kalli fuskarshi ba tace “Ina wuni.”
Tsura masa ido ta sake yi ganin mak’walaton wuyanshi ya yi sama da k’arfi alamar ya had’iyi yawu sannan ya yi k’asa kamar wanda ya had’iyi kunama, da sauri ta d’aga k’afafunta za ta bar wurin ta ji rikitacciyar muryarshi mai bala’in sanyi da taushi wacce ta dace da yanayinshi na sahihin namiji mai sassauk’ar k’ira yace ” Ya sunanki?”
Cak ta tsaya tare da juyowa a hankali ta sauke ido a kan shi, kamar ba za ta amsa mi shi ba sai kuma a sanyaye ita ma sosai cike da ladabi da kamun kai tace “Sunana kuma?”
Ido kawai ya iya lumshewa alamar e, d’an kawar da kanta tayi gefe sannan tace ” Haleematu Yusuf Saddi.”
A kan labb’anshi ba tare da ya san maganar za ta fito fili ba ya sake furta “Haleematu.”
Kallonshi ta yi da kyau sai kuma ta juya ta ci gaba da tafiyarta, bai daina kallonta ba har said ya ji zuciyarshi na tambayarshi “Haba Huzeifa, wannan kallo ai ya wuce k’ai’da.”
Da sauri ya d’auke kan shi yana jan d’an gemunshi da ya tara dan koyi da sunna tare da fad’in “Astagfirullah! Allah na tuba ka yafe min, a’uzubillah, shaid’an me ka yi haka? Ya aka yi ka samu nasara a kai na yau?”
Dab’as ya zauna a dakali ya na ci gaba da furta neman tuba ga mahaliccinshi kan ya gafarta masa, dan ya tabbata da shi ta ke fuskata da ta ji kallon ya fara cutar da ita, wanda kuma aka hana a shari’a cewa ” Bai halata ka dinga kallon musulmi ba kallo wanda zai cutar da shi, sai dai in ya kasance fasik’i ne, to k’aurace masa ya zama wajibi.”
In da a farkon karatun littafin Akhdari kuma aka lissafi a jerin abubuwan da baligi kuma ak’ili ya kama ya kiyaye shi ne ” Kallon ajnabiya (manisanciya-wacce ta ke ba muharramar ka ba), sannan ka kiyaye jin dad’in zancenta.
Yau kam suna cikin farin ciki na gama jarabawarsu, ko ba komai sun samu hutu su ma daga ranar da ake k’wlawa, musamman ma Saleema da take ganin wahalar banza take, sai dai farin cikin na ta ya koma ciki sanda mahaifin na su ya umarcesu da su shirya zai sa dreba ya kaisu gidan Alhaji Auwal wanda zai iya cewa mai gidanshi ne a fannin siyasa, dan shi ya kama hannunshi ya durmiya a cikin tafiyar, duk da a girme ya girmeshi nesa ba kusa ba, dan ko Yayan Alhaji Yusuf d’in ya girma amma suna mutumci da mutumta junansu.
A tsanake mamanta ta kalleta tace “Saleema, lafiya ki ke ta had’e fuska?”
K’ara turo baki ta yi gaba ta na k’ok’arin saka rigarta duk da sanye take da hijab saboda kunyar Maman da ta ke ji ba za ta iya tub’ewa a gabanta ba tace “Ni wallahi Mama ba na son zuwa gidan nan, dan kar Abba ya ce na rainashi zan tafi kawai.”
Murmushi Safiya ta yi da mamakin wai Saleema ba za ta iya saka riga a gabanta ba dan kar ta lafiyayyen k’irjin da ya cika mata gaba tace “To wai me ya sa ba kya so? Can ma gidan hutu ne fiye ma da na mahaifinku.”
Juyowa Saleema ta yi ta kalleta tace “Mama, ba wannan ne matsalar ba, kin san ko k’auye zan iya rayuwa, kawai dai yaran nan na sa ne ni wallahi ba su kwanta min a rai ba.”