Baiwata

BAIWATA 6

Da mamaki Maman tace “Su wa kenan?”

Cike da yatsina fuska tace “Yan mazan mana, duk ba su da tarbiya wallahi.”

Rik’e hab’a Maman ta yi da mad’aukakin mamaki tace “Ikon Allah! Saleema yaushe ma ki ka musu sanin da ki ka gane haka? Shin Mu’az d’in da ko shekara bai yi da dawowa daga karatu ba? Ko kuma Mu’awwaz d’in da ke da tsantseni da share mutane?”

Ta na gama saka rigar ta cire hijabin ta na saka zip tace “Dukansu Mama, wallahi kura ce da fatar akuya, dukansu rainawa mutane hankali suke, ba ma kamar tuzurun nan.”

Dariya Maman ta sake har da k’yalk’yalawa tace “Wa ye tuzuru kuma?”

Ba alamar wasa tare da ita tace “Shi Mu’az d’in mana, shekara talatin ba aure amma ya na nuna bai damu da komai da kowa ba, hmmm ! D’an rainin hankali kawai.”

Maman ta dai abun dariya da mamakin yanda ta hak’ik’ance ta na ta sababi take, to ita ba ta ma san yaushe ta musu wannan sanin ba haka? Tabbas sun tab’a zuwa gidan amma fa tun ba ta kai shekara goma ba a duniya, duk da ta san ta bata da mantuwa kan abin da ya shafi rayuwar duniya da karatunta na islamiyya, amma dai ba ta tunanin har yanzu ta na tune da abinda ya faru shekara tara da ta wuce.

Haka ta gama shiryawa amma sam ba ta so haka ba saboda ita ta gama fahimtar duk wani da Abbansu ke alak’a da shi ta kusa sosai to d’an boko ne da ke da wayewa, sai dai na wani ya fi na wani kawai. Ta na gama shiryawa ta fito farfajiyar, a nan ta samu su Hadeeya har da mahaifin na su a tsaye da alama so ya ke ya ga tafiyarsu da kuma Mamansu gefe ta na amsa waya.

Sanye take da doguwar riga wacce gaba d’aya gabanta yake a bud’e, ma’ana aka masa doguwar tsaga har zuwa cibiyarta, sai siket d’in atamfar da ya rufe mata cibayar inda a baya kuma yake yage da tsaga shima har idan tana tafiya kamar za ka hango gwiwoyinta, k’aramar jakarta ta rataya ta tsakiyar wuyanta da hannu, sai takalmin kalar jakar masu d’amara da rufaffiyar sama, kwalliya ce ta ban mamaki ta d’auka sai dai ko d’an kwali babu a kan ta, hasalima d’an kwalin rik’e yake a hannunta, a hakan wai shi ma wani kalan tsarin ne.

Kayan sun matseta sosai yanda suka fito da kyakyawar surarta da kuma kyawun fuskarta, masha Allah kuma abun ka ga farar fata sannan mai kaurin jiki, hakan yasa Hadeeyar ta zama basu da maraba ita da Saleema da ta bata shekara uku da haihuwa saboda su na da kumari.

Cike da rashin jin dad’in yanda ta ga yan uwanta sun shiryo ta kalli Hadeeya a tausashe tace “Haba Hadeeya, wannan wace irin shiga ce? Kina ‘yar musulmai amma ki fita haka kanki babu rufi? Idan ma ba zaki saka hijab ba ko gyale ne ki saka mana.”

Cikin tsiwa da raini da kaud’i Hadeeya ta kalleta tace “Ke kuma malama ina ruwanki da shigata? Kina da matsala da hakane? Ka ji min mata kai, so kike na yi irin shigarki kamar wata matar aure?”

Kafin kowa ya yi magana Ardayi da aka mata kiran gaggawa a wajen aiki ta k’araso da sauri kai tsaye mahaifinsu ta tunkara cikin shagwab’a tace” Bébé, kira ne da wajen aiki ana buk’atata yanzu, zan tafi sai na dawo…”

Ta yi maganar ta na fad’awa jikinshi ta sumbaci labb’anshi tare da d’agowa tace” Ba zan jima ba Bebe, sai na dawo.”

Saleema da tun da ta ga ta nufeshi ta d’auke kanta saboda kunya, shi kan shi yanzu da shekaru su ka k’ara ja ya kan ji nauyi idan irin haka ta faru, sai dai Ardayi ta saba kuma ba ta ganin hakan a matsayin wata matsala.

Hannu kawai ya d’aga mata bai iya furta komai ba har ta k’arasa kusan su Hadeeya da ba ta san akan me suke magana ba ta rumgume su su ma musamman Hamdeeya har tana fad’a mata “Shoyerta (autata) ki kula da kan ki.”

“To Momma.” Ta fad’a cike da farin cikin za ta tafi unguwa na wasu kwanaki, suna kallo ta shiga motarta ta bar gidan.

Sai lokacin Hameeda da ita ma dai wata arniyar shigar riga da siket na shadda ne jikinta tace” Kama da matar auren ma wacce ta haihu, dan wannan hijabi da ta saka sai matan aure masu ‘ya’ya, dubi fa daga nan baya har k’asa yake ja mata.”

Kallon hijabin na ta sukayi kam mai hannaye wanda ya mata kyau sai kawai suka bushe da dariya suka tafa hannu Hadeeya na fad’in” Wa ya ga ta Allah.”

Murgud’a baki Hameeda tayi ta harari Saleema tace” Wai a haka za ta bi mu, ki ga fuskarta ko hoda ba ta murza ba sai k’yallin mai take, mtssss! Ni wallahi da Abba da ma ka hanata zuwa.”

Wani kallo Saleema ta ma Hameeda sai kuma ta kalli mahaifin na su da duk da yana jin me ke faruwa amma hankalinshi na ga waya yana latsawa tace” Abba ka a yaran nan magana mana, dubi fa shigarsu?”

Wayar da ya d’ora a kunne ya sa shi nuna mata su wuce su tafi kawai dreba na jiransu, cike da takaicin halin ko in kula ta fara yin gaba ta shige motar.

Tsaki Hameeda ta sake ja har suka k’arasa kusa da mota inda dreba ke jiransu suka shiga ya jasu zuwa gidan.

*______________*

Alhamdulillah.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button