Baiwata

BAIWATA 7

           *NA*


_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

  *AHALINA*

GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.) 🤜🤛
(Burinmu d’aga muryoyinmu sama domin anfanar da al’umma had’e da ciyar da adabin hausa.)
[G. M. N. A] ☆ 📖🖊️

Bismillahir rahamanir rahim

              _7_

Tabbas sun yarda Alhaji Auwal ya fi mahaifinsu kud’i nesa ba kusa ba, dan daga irin ginin da ya tarwatsa za ka fahimci haka, da kuma irin kayan alatun da suka k’awata gidan, ba su daina kalle kalle ba har mai aikin da ta musu jagora zuwa cikin gidan suka shigo k’aton falon.

Saleema da ke baya cikin sharb’eb’en hijabinta kallo d’aya ta ma uwar gidan ta saki murmushi saboda tuna shekarun baya da su ka sameta tana cikin ganiyar k’uruciyarta mace yar gayu da wayewa, amma yanzu shekaru sun lak’ume duk wannan ji da kan da k’uruciyar, ba abinda ya rage mata face dattijuwar fuskarta mai d’auke da gilashi.

Kusanta suka fara zuwa inda take zaune, Hadeeya da Hameeda daga tsaye suka gaisheta da “Ina yini?”

Hamdeeya kuma kusanta ta zauna dan ta san matar ita ma tana wangale mata baki sai dai ba ta ce mata komai ba, yayin da Saleema dake gefe ta durk’usa kamar za ta yi zaune tace “Ina wuninku Mama.”

Da fara’a da kuma jin dad’in gaisuwar ta Saleema ta kalleta cike da kulawa tace “Lafiya lauSaleema, kina lafiya?”

“Lafiya lau.” Ta fad’a cike da kunya, maida hankalinsu sukayi kan wata dattijuwar da ke shigowa falon hannunta rik’e da waya, kallo d’aya suka mata ita ma suka gaisheta kasancewarta amaryar gidan. Cike da yauk’i da jan aji ta wani yatsina fuska tace “Lafiya lau, har kun iso ?”

Kafin kowa ya ce wni abu Hameeda ta kalleta tace “Aunty ina Ummeeta?”

Cike da yatsina fuska tace “Ta na ciki.” Ta fad’a tana nuna mata k’ofar da ta fito, mik’ewa Hameeda ta yi ta nufi d’akin suka bi bayanta da kallo, wani d’an murmushi amaryar ta saki saboda sak ta hango Hameeda da d’anta Mu’awwaz a matsayin ma’aurata, a ganinta ba k’aramin kyau za su yi ba. Dan haka ma ta wuce inda za ta je ta na ayyana abubuwa da dama a game da ganin Hameeda, dan sam shigarta ba ta d’auketa bakin komai ba sai kawai wayewa da zamananci, sannan ta na da labarin ilimin yaran daga wajen mahaifiyarsu.

Hajia Rabi ce ta kalli su Hadeeya tace “Ku wuce ciki kuma, kun san ana rana duka yaran su na bacci.”

Tab’e baki Saleema ta yi a ranta ta ayyana “Tunda an saba musu ba.”

Mik’ewa sukayi Hajia Rabi ta kalli mai aikin tana fad’in “Ki nuna musu inda aka gyara musu, idan su ka yi wanka sai ki kai musu abinci.”

Kallonta Saleema ta yi sanda suka kama hanyar d’akin tana mamakin to wankan me za su yi? Ba fa daga wani garin suke ba, tafiya ce da ba ta wuce minti ashirin ba, amma dai ba ta ce k’ala ba suka wuce cikin.

  *_____________*

K’aramin littafin dake d’auke da kala-kalan abincin da aka mik’o masa ya girgiza kai tare d’an murmushi yace “Um-um! Nagode da wannan ma.”

Kyab’e fuska Sharhasila ta yi kamar za ta yi kuka tce “Haba dai Yallab’ai, ka zab’a mana, ni fa zan biya.”

D’an sunkuyar da kai ya yi kamar mai tunani sai kuma ya d’ago ya sake girgiza kai yace “Ya isa haka Baby, kin san bana son zuwa irin wuraren nan cin abinci, hasalima ni na fi jin dad’in cin abincin gida.”

Had’e fuska tayi tare da kawar da kai sam abinda ya fad’a bai mata ba, to ita ina za ta iya wani girki? Tabb’! Kallonshi tayi tace “Yallab’ai, amma dai ka san ba ni zan dinga girki ba idan mun yi aure ko?”

Da mamaki Huzeifa ya kalleta yace “Ban gane ba? To wa zai yi? Ni?”

D’an murmushi ta yi cike da shashanci tace “A’a haba, ina nufin sai mu samu yar aiki.”

Iska ya feso a bakinshi yana jin wani b’acin rai na hauhawa masa, to shi bai san wane irin aure ne za su yi da Sharhasila ba, dan tana tak’amar ita yar mai kud’i ce, kuma ita ta nunashi ta ce tana so, sai ya zama zai zaunata mulkeshi ne? Abubuwa na hauka da kidahumanci ta ke kawo masa fa, wannan wane irin abu ne?

Kallon kyakyawar fuskarta ya yi wacce ta fad’a masa wuni ta yi wajen gyaran jiki da kwalliya wai dan za su had’u wurin cin abincin nan kawai wanda shi a wajenshi bai da wani anfani, cikin tausasa murya yace “To me yasa ke ba za ki dafa ba?”

Turo baki ta yi irin shagwab’ar nan cikin harshen faransanci tace “Amma Bebe ai kasan ni aiki nake zuwa ko? Yaushe zan maka girki sannan na yi aikina? Ba zan iya ba gaskiya.”

Shi ma a harshen faransancin yace “To ai macece ke, kuma ba’a yi auren ba, zaunawa za ki yi kafin lokacin ki tsarawa kan ki rayuwarki, kar ki maida hankali kan abinda ba zai anfani lahirarki ba, Sharhasila wannan aiki da kike moriyarki da shi iya duniya ne kawai, idan ki ka fi k’arfin shed’an ne za ki nemi lahirarki da aikin, dan haka a ganina tun ba’a d’aura aurenmu ba ki tsarawa kanki komai ta yanda za ki ba wa komai lokacinshi yanda ya kamata.”

K’ank’ance ido yayi sosai ya na ci gaba da kallonta yace” Kin san wani abu? Mutum ne ni mai matuk’ar son kulawa, hakan yasa mahaifiyata ke fad’a min wai wasu lokuta kishi nake da k’annaina…”

Yar dariya ya yi ya d’ora da” Gaskiya ne, sai na ji idan ina magana da ita bana so kowa ya mana kutse bare a tilasta mata raba hankalinta gida biyu, sannan ina da matuk’ar son abincin gida, ma’ana ina son abinci irin su tuwo, d’an wake, faten doya, biski, dambu…da sauransu.”

Tsareta ya yi da ido yace” Da fatan dai duk kin iya wannan? Idan ma ba ki iya ba ina fata za ki koya saboda ni.”

Tunda ya fara magana ta zuba masa ido ta na kallo, dogon bayanin nan da ya zauna ya na mata sai ta ji kanta ma ya fara ciwo, to ita kam ta rasa hadisi na nawa ya karanta mata, a gaskiya ba ta ma gama fahimtar zancen shi ba, dan haka ta na buk’atar k’arin bayani.

D’an gyara zama ta yi tana kallonshi tace “Bebe ban gane ba, ka min dalla-dalla mana, ka na nufin ni ma sai na koyi iya tuk’a tuwo kenan?”

Murmushi ya mata yace “B za ki iya ba kenan?”

Kawar da kai ta yi tana nazari na wasu dakik’u, a gaskiya duk yanda take so da k’aunarshi ba za ta iya wannan wahalar ba, amma kuma sanin waye Huzeifa ya sa ta d’an yi wata shawarar, tunda dama ba shi ya fara cewa ya na son ta ba, ita ce ta ji ta na k’aunarshi saboda kyawawan halayenshi har ta masa tayin soyayyarta, da fari kam ya nuna baya ra’ayi saboda kasancewarta ‘yar mai kud’in unguwarsu, amma da ta dage ya kuma shawarci mahaifiyarshi sai ya amince har yanzu suke shirin zama mata da miji nan da kwanakin da ba zasu gaza goma sha biyar ba. Dan haka ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace “Bebe, ai kasan soyayya ta sa na ce ina sonka, dan haka ba abinda ba zan iya yi maka ba.”

Fad’ad’a Murmushin shi ya yi yace “Nagode sosai, ai na d’auka ba za ki yi ba.”

Da irin zolaya tace “Ni na isa? Idan fa ka fasa aurena?”

Dariya ya yi cikin tattausar muryarshi yace “Ba zan fasa aurenki ba, sai dai na miki kishiya bayan auren.”

Zaro ido ta yi ta dafe k’irjinta cike da tashin hankalin da ya ziyarceta lokaci d’aya tace “Bebe, dan Allah ka daina min irin wasar nan bana so…”

Tsal! Ta taso daga kan kujerarta ta dawo kusa da shi sai dai dake babu wata kujerar sai ta durk’usa k’asa ta rik’o hannunshi, da sauri ya d’an jaye hannunshi saboda gudun matsala, dan baya son ya sake shiga halin da ya shiga d’azu daga kallon wata.

Sake rik’o hannun na shi tayi ta rik’e gam tana kallon idonshi da na ta idon da sukayi jajir suka tara ruwa alamar kuka, cikin rikitacciyar murya ta dinga mitsika hannunshi ta na fad’in “Ka na ji ko Bébé ? Dan Allah ka daina irin haka bana so, ka ga ba zan iya kishi da wata a kan ka ba, dan Allah ka min alk’awarin ba za ka tab’a min kishiya ba?”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button