Baiwata

BAIWATA 7

Da mad’aukakin mamaki ya kalleta sosai ya na nazartarta, daga bisani numfashi ya sauke yana ci gaba da kallonta yace” Tashi ki zauna, kina ga fa kallonmu a ke.”

“Ni ban damu ba su kallemu, ka min alk’awari ka ji mijina.” Ta fad’a da alamar fashewa da kuka, jinjina kai ya yi yasake nuna mata wurin zaman da d’aya hannunshi yace “Dan Allah ki zauna sai mu yi magana.”

Da sauri ta mik’e ta zauna ka kujerar ta zuba mi shi ido ta na kallo kamar wanda take son gano ta inda yake fitar da numfashi. A hankali Huzeifa ya d’an girgiza mata kai cikin sanyayyar muryar da hakan d’abi’arsa ce yace mata” Ba zan iya miki wannan alk’awarin ba Sharha, saboda ni d’an adam ne ban san me Allah ya tsara min a gaba ba.”

Jin hakan daga bakinshi ya sa ta fashewa da kuka da iya gaskiyarta kawai ta kifa kanta a kan teburin, cike da damuwa da jin tana muzantashi cikin mutane ya k’ara tausasa murya yace” Dan Allah Sharha ki daina kukan nan, kin ga tashi mu bar nan in dai kuka za ki min.”

Kamar ba ta san ya na yi ba haka ta dakeshi, mik’ewa ya yi ya sake maimaita” Tashi mu je na ce.”

Nan ma shirun ta masa, ranshi ne ya d’an fara b’aci dan haka ya zagaya kusanta ya d’auki jakarta da wayarta da makullai dake aje, bai tsaya jiran komai ba ya finciki hannunta suka fita a wajen dan shi fa duk taushinshi mutum ne kuma da baya son iskanci, sam ba zai lamunci ta mayar da shi wani lusari ba dan baya da kud’i sannan mad’inki ne shi, haka kawai ba za’a raina masa wayo ba, ta ya ma zai mata wannan alk’awarin? Ta san me alk’awari yake nufi a shari’ance? Ta san me zai faru da shi idan Allah bai nufeshi da cikawa ba? Ba ma duk wannan ba shi fa gaskiya mace mai addini ya ke da burin samu, hakan yasa ya ke tunanin ko ya aureta idan bai sameta yanda ya ke buk’ata ba to indai ya samu halin k’ara aure to zai k’ara, sai kuma ta nemi katse masa hanzarinsa da wani tunaninta irin na hayudawa haka kawai.

Tuk’i kawai yake a motar ta ya na kallonta jefi-jefi, yanda ta d’aga hankalinta akan tashin d’aukar mata alk’awarin nan da irin kukan da ta yi, a ganinshi ko iyayenta aka ce sun rasu iya hakan ne kawai za ta yi, idonta sun yi jajir sosai sun kumbura abu ga jar fatar da ba ta saba da hayaniya ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon gabanshi yace “Ki yi shiru Bebe, kukanki fa ya na tab’a min zuciyata sosai.”

“To idan ka hakane ka min alk’awarin mana.” Ta fad’a kamar za ta matso daf da shi ta sumbace shi, d’an tab’e baki kawai ya ui ya girgiza kai bai ce mata komai ba, cikin tausa murya tace “Bebe me ye a ciki ne wai? Alk’awari fa kawai za ka d’auka da fatar baki.”

Wata nauyayyar ajiyar zuciyar ya sake saukewa yace “Sharhasila hadisin Anas d’an Malik fa ya ji daga bakin Manzon Allah (S. A. W) ya ce” Alamomin munafiki guda uku ne, idan zai yi magana sai ya yi k’arya, idan ya yi alk’awari ya sab’a, idan aka amince mi shi ya ci amana…”

Kallonta yayi fuskarshi d’auke da damuwa sosai yace” Duka wannan alamomin za su tabbata a kaina idan na miki abinda kike so yanzu, na farko idan na fad’a miki ni na san k’arya na miki har cikin raina, idan kuma ban cika alk’awarin ba kin ga na sab’a, sannan na ci amanar yardar da kika min, to me ye ribar hakan? Me zai sa na jefa kaina a wannan halakar ? Alk’awari d’aya da zan iya yi miki shine, ko bayan aurenmu zan zama mai mi yi miki uzuri, sannan ko da Allah ya jarabceni da k’ara aure, to zan ci gaba da kare martaba da kimarki a idon d’ayar, ba zan tab’a bari ki zubar da hawaye ta dalilina ba kuma da sanina, sai dai abisa rashin sani, wannan alk’awarina ne gareki.”

Wata arniyar harara ta maka masa ta gefen ido dan ita sam abinda ya fad’a ta kunnen da ya fi kusa da shi ya shiga ko d’ya kunnen bai kai ba ya fita abunshi, ya zai tsareta da wasu zantukanshi na daban kawai da wasu tatsuniyoyi? Ba ta ce mishi k’ala ba har suka isa k’ofar gidansu.

Fita duk sukayi inda ta zauna mazaunin dreba shi kuma ya kalleta yace “Ni zan idasa gida a k’afa, sai da safe.”

A shagwab’e tace “Ba za ka kirani ba?”

Shafa sumar kanshi ya yi yace “E to…kin san fa jibi za mu fara jarabawarmu (BAC) karatu yayi zafi sosai, amma dai zan kok’arta na kiraki.”

Turo d’an k’aramin bakinta ta yi tace “Tom, sai na ji ka.”

Da haka suka rabu ita ma ta shige k’aton gidansu kowa da abinda yake ta sak’awa da warwarewa a zuciyarshi, inda Huzeifa ya fi maida hankali kan irin zaman da zaiyi da yarinyar da take ganin mahaifinta mai kud’i ne, shi kuma d’an ladanin da ya rasu ya barshi da nauyin k’annanshi da mahaifiyarsu wanda ya ke ciyar da su ta hanyar d’inkin da yake d’an samu idan ba ya karatu, yarinyar da aka ma hanya duk da takardunta ba su kai ba amma take aiki a babban reshen kamfanin shiga da fitar kud’i na Al’izza, shi kuma yanzu ne ma yake karatun, dan ko ya samu jarabawar nan yana da burin ci gaba da karatunshi.

Ku yi hak’uri da rashin ganin update jiya, hakan ya faru ne sakamakon wasu uzurirrika.

Alhamdulillah.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button