Baiwata

BAIWATA 8

Jinjina kai ya yi yace “To da kyau, kin gama aikin ki ne yanzu?”

Cikin ladabi tana ta rarraba ido tsakanin Alhaji Auwal ɗin da kuma amaryar sa da ke binta da kallon ƙyama a ɗan tsorace ta amsa da “E na idar.”

“Shikenan za ki iya tafiya.” Ya faɗa yana ci gaba da cin abincin shi, tsaf Saleema ta kula da inda yarinyar ta kalla a matuƙar tsorace, a hankali ta ɗan ƙyallara idonta ta kalli inda idon yarinyar ke kallo. Karaf! Idonta suka sauka kan Mu’awwaz da ke ta ma yarinyar signa da ido, da sauri Saleema ta sake kallon yarinyar ta ga ta juya ta fita, taɓe baki kawai ta yi da tunanin wannan shi ne abinda Mamanta ta faɗa cewa Mu’awwaz ya cika tsantseni, wato shigar da ke jikin yarinyar ya ke ƙyamata? A karo na biyu sake taɓe baki ta yi ta ɗauki cokalinta za ta ci gaba da cin abinci, Mu’awwaz ta ga ya miƙe ya na faɗin “Na ƙoshi.”

Kallonshi amarya tayi tace “Bebe, ba ki ci sosai ba fa?”

Ba tare da ya ko kalleta ba ya kama hanyar fita ya na ɗaukar tuffa ɗaya yace “Ya isheni.”

Da kallo Saleema ta bishi mamaki ya lulluɓe na tunanin wai su mutanen nan ba sa jin kunyar kiran kowa Bebe ne? Haka matar Babansu ma take kiran ubansu Bebe, sai ka ce wani ɗan goye.

Su Hadeeya ma miƙewa sukayi suka ce “Mu je mu shirya kar mu tsayar da Yaya.”

Su uku ne suka nufi ɗakin su dan shiryawa, Saleema kuma da ta kalli Alhaji Auwal ne tace “Abba, ya na ga yanzu gidan babu yara?”

Murmushi ya yi ya saki kallon amarya yace “To ai yaran da kika sani su ne suka girma yanzu, ga Mu’awwaz nan kin gani ya zama saurayi, ga Ummee, Safwan ne kawai kuma ya na ƙasar waje karatu.”

Jinjina kai tayi kawai ta ɗan tsakurar abincin ta na jin duk ba daɗi sai ita kaɗai yanzu a cikin iyayen, fitowar su Hameeda yasa ta juya dan ganin da wace shigar aka fito?

” A’uzubillah!” Ta fara ambata a ranta, dan kuwa a cikin shigar ta Hameeda ce kaɗai ta ga da ɗan dama-dama, saboda ita ce ta sa doguwar riga irin na material ɗin da ake ɗingawa da ɗan-kwalinta, ɗinkin ya bi jikinta yanda ya fito mata da surarta, kallabin kuma ta ɗorashi a kan ne kawai amma ba ta ɗaure ba. Amma shigar Ummee abun ya munana sosai, dan riga da wando ne da suka kamata, wandon ma irin wanda ya ɗan ɗage mata bai sauka ba sosai, sai takalma dake ƙafarta ƙafa ciki, kanta kuma wata ƴar yaloluwar hula ce ta ɗora sai gashinta na doki da ya bayyana.

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli fuskokin iyayen, dukansu fara’a ce a fuskarsu har da tagomashin faɗa musu “Sai kun dawo.”

Da gudu Hamdeeya ta tashi ta bi bayansu tana faɗin “Ni ma zan je.”

Dariya Alhaji Auwal ya ƙyalƙyale da ita yace “Tafi a hankali to kar ki faɗi.”

Suna fita ya ɗauki wayarshi ya turawa Mu’az saƙo cewa ya karɓi makullin morarshi hannun dreba akwai kuɗi ciki sai su tafi.

Saleema da har yanzu ta kasa daina kallonsu da mamaki ne yasa ta ɗan numfasa, a ladabce sosai cikin nutsuwa bayan ta aje cokalin hannunta tace “…

Ku yi haƙuri da wannan.

Alhamdulillah.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button