BAIWATA 9
*NA*
_SAMIRA HAROUNA
SADAUKARWA GA
*AHALINA*
GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.) 🤜🤛
(Burinmu d’aga muryoyinmu sama domin anfanar da al’umma had’e da ciyar da adabin hausa.)
☆ [G. M. N. A] ☆ 📖🖊️
Bismillahir rahamanir rahim
_9_
A ladabce sosai cikin nutsuwa bayan ta aje cokalin hannunta tace “Abba, ku yi haƙuri dan Allah idan abinda zan faɗa zai ɓata muku rai…”
Da hannunta ta ɗanyi alama tace “Sai na ga kamar ba ku damu da yanda su ka fita ba kamar dai yanda yanke faruwa a gidanmu, Abba a ganinku haka dai-dai garesu a matsayinsu na ƴaƴa mata? Ina ganin kamar rufin asirinku da na su shine ku tayasu kare mutumcinsu…”
Ganin duk sun ƙura mata kamar mamakinta suke ko kuma dai wani abun sai ta tsagaita, ɗan sake kallonsu tayi cike da kunya musamman ma amarya da ta ga kamar ta na mata kallon jin haushi, sunkuyar da kanta tayi ƙasa tace” Ina ƙara baku haƙuri, na yi aiki da faɗar Manzon Allah (S. A. W) ne, ya koya mana hani ga mummunan aiki idan ka na da iko, sannan ya faɗa mana idan za ka iya ka hana da hannayenka, idan ba zaka iya ba da harshenka, idan ba zaka iya ba ya ce to da zuciyarka, ma’ana ka ƙyamaci abun a zuciyarka, shiyasa na mu ku magana amma ban yi da raini ko ɓata muku ba.”
Mamar Ummee da take ganin kamar da ƴarta Ummee ne take, dan ita bata ga aibun shigar su Hadeeya ba ma sam, cikin fushin da ta kasa ɓoyewa ta kalli Saleema tace” Kinga ƴan mata ki yi abinda ya shafeki, bana son mutum mai shiga sabgar da babu ruwansa, ina aibun shigarsu a nan? Yaranki ne mu da za ki zaunar da mu kina mana wannan maganganun? Oho! Idan na fahimceki so ki ke ki ce mu ɗin ba mu san abinda ya dace ba sai ke.”
Dogon tsaki ta ja ta miƙe tsaye tana ɗaukar wayarta ta juya ta bar wurin, da kallo Alhaji Auwal ya bita kafin ya maido kallonshi kan Saleema da ba ta ji daɗi ba tace” Abba dan Allah ka bata haƙuri, ita dama gaskiya ɗaci ne da ita, mafi alkairin mutane kuma shi ne wanda za’a faɗa ma gaskiya ya ɗauka har ya yi anfani da ita.”
Ajiyar zuciya ta sauke jiki a sanyaye ta miƙe tsaye ta kallesu tace” A ci lafiya.”
Juyawa ta yi za ta fita a falon Hajia Rabi tace” Ina kuma za ki je?”
Juyowa tayi da fara’a tace” Zan fita waje ne.”
Jinjina kai Alhaji Auwal ya yi yace” To, amma ki kula da kanki.”
Ƴar dariya tayi tace” Ba ƙofar gida zan fita ba, iya farfajiya ne kawai.”
A tare suka jinjina kai cike da jin ƙaunar yarinyar, in har suka ƙi abinda ta faɗa to ba su da wata hujja ta ƙin ta, sannan ba ita su ka ƙi ba sai gaskiyar da ta faɗa, dan haka ma suka ji ta birgesu duk da su ma ba su ga aibun shigar ta su ba sai yanzu ne da ta faɗa hotunan shigarsu ke dawo musu a kai, musamman ma ta Ummee da ta fi munana.
Ta na fita a hankali ta shiga ɗan zagayawa ta na jin ina ma tana da waya da ta kira Mamanta, amma sai ta yanke shawarar idan Hadeeya ta dawo za ta karɓi ta ta sai ta kira dan su gaisa, saida ta kai ƙarshen katangar da a saninta nan ɗin bayan gida ne sai ta dakata saboda akwai duhu wurin, juyawa ta yi da nufin ƙarasawa wajen motoci da ta ga akwai haske ta ko ina. Sai dai kamar gizo kunnuwanta su ke jiyo mata abun da ya kayar mata da gaba duk da ba ta san me ye ba? Amma dai ta shiga zulumi da ɗumbin mamakin wa ye haka? Me kuma ya same shi da yake irin haka? Alhalin daga ji muryar ƙosasshen namiji ne.
Cikin sanɗa ta ɗan fara leƙa kanta, ba ta ga komai ba sai dai ta ɗan ƙara jin sautin kusa da ita, tako ta yi da bai wuce uku zuwa huɗu ba ta sake leƙawa dan a tsorace take. Da bala’in sauri ta rufe bakinta da tafin hannunta na hagu ta saki siririn numfashin da ya fitar da sauti kamar wacce ta sha yaji, gaba ɗaya ta ƙwalalo idonta tsabar kaɗuwar da ta yi na ganin wannan lamari, take jikinta ya ɗauki rawa tamkar mazari, da mugun gudu zuciyarta ta shiga bugawa, dan a rayuwarta ba ta taɓa mummunan gani irin wannan ba na yau.
Tabbas ba ta tsiraicinsu ba saboda duhun da ke mamaye a wurin, sai dai hasken wata wanda dama ɗaya ne a cikin dalilin da ya sa ubangiji ya saka mana shi dan ya haska mana abunda ya shigarana duhu a yanar idonmu, ta hakane ta gane su waye a wurin da kuma abinda suke aikatawa. Riskar yanayin da bai taɓa samu ba yasa su kansu suka tsorata sosai, yarinyar durƙushewa ta yi ita kanta jikinta ya ɗauki ɓari, inda shi ma ya shiga kiciniyar saka wandonshi, jikinta na makyarkyata ta juya da sauri sosai ta tunkari komawa inda ta fito, tana jin ya biyota yana kiran “Sssaleema, Saleema dan Allah… Saleema dan Allah tsaya ki saurare ni, na roƙeki S…”
Shigewar da ta yi falon da sauri ya sa dole ya ja birki ya tsaya ya na hangenta, ganin ta nufi sama alamar masaukinsu za ta shiga ya sa ya daki iska yana buga ƙafarshi da mugun haushi ya furta” Shiiiit!”
Dafe kanshi ya yi ɗaya hannun kuma ya riƙe ƙugu ya na safa da marwa a ƙofar ɗakin ya rasa me zai yi, juyowar da zaiyi yarinyar ta taho har yanzu jikinta ɓari yake duk ta rufe fuskarta da tsohon hijabinta alamar kuka take, saida ta zo kusa da shi ta durƙusa cikin kuka tace “Dan Allah na roƙeka ka ƴantani hakanan, na gaji da wannan rayuwar, yanzu haka ni da mhaifiyata da ƴan uwana muna samun abun da za mu ci dai-dai gwargwado.”
A rikice Mu’awwaz ya zuba hannayenshi biyu cikin aljihu ya lalaba ya ciro kuɗi, miƙo mata yayi cikin tashin hankali yace” Karɓi, daga yau kar na sake ganinki gidan nan, ki tafi kar ki sake zuwa.”
A razane ta ɗago ta kalleshi sannan ta kalli kuɗin, a ƙalla za ta iya jan jari da su, da haka za ta tsira daga sharrinshi, karɓa ta yi ta miƙe tana faɗin” Nagode.”
Juyawa ta yi za ta fice sai kuma ya canza shawara, da gudu ya tari gabanta yana faɗin” Kin ga! Gobe ma ki dawo, saboda nasan halin Abba da sa ido a kan komai, idan ya ji ba ki zo ba zai sa a bincika masa, ni kuma ina tsoron kar yarinyar can ta faɗa masa abinda ta gani.”
Ƙasa ta yi da kanta alamar hukuncin nan bai mata ba, ita kam da ya barta ta tafiyarta shikenan, amma ita kanta kunya ba za ta barta ta zo gobe ba, cikin taushin murya ya sake faɗin” Dan Allah ki zo gobe kin ji, bana so Abba ya yi zargin wani abu aka miki.”
Kallonshi ta sake yi irin kallon nan na da ke nuni ko dai wani abun za ka sake min? Kamar ya fahimci kallon kuwa sai yace” Na rantse miki da Allah ba abinda zan miki, wallahi haka ba za ta sake faruwa ba.”
Fuska a gintse ta ɗaga kai alamar to, sannan ta raɓashi ta wuce ta bar gidan tana kuka na takaicin yanda ta rasa mutumcinta dan kawai ta ciyar da ahalinta, yanzu gashi dalilin haka ba ta san me zai faru ba a gaba.
10:46 su Hadeeya suka dawo gidan, har sun fito daga motar Mu’az ya bi Hadeeya da wani kallo yace “Ƙanwata zo ki ji.”
Juyowa tayi ta na sakar masa fari da ido ta dawo ta zauna, ganin bata rufe ƙofar ba yasa shi zura hannu ta gabanta kamar wanda zai taɓa mata ƙirji ya rufe ƙofar yana kallonta yace “Sirri za mu yi.”
Murmushi tayi ta sassauta murya tace “To Yayana ina jin ka.”
Daf da ita ya matso sosai ya na wani kashe mata ido yace “Ki na da saurayi?”
Ɗan jim ta yi kafin ta kalleshi ta na ɗan lumshe idonta saboda kusancin ya yi yawa sosai tace “Ina da, amma…”
“Amma me? Kina nufin ki ce Yayan na ki ba zai samu shiga ba?” Yanda ya yi maganar ya na kamo hannunta yana matsawa ya sa ta kasa cewa komai sai rarraba ido take, sake matsowa ya yi har numfashinsu ya fara gyauraya sannan yace “Uhumm! Ina jin ki.”