BAIWATA 9
Dake hakan bai taɓa faruwa da ita ba, duk yanda take samun kusanci da namiji ba ya wuce ƴar gaisuwa da hannu ko dafa kafaɗar juna da dai irin haka, kaa cew komai ta yi, hakan yasa shi sake faɗin ” Deeya.”
A hankali ta ɗan ɗago kanta da niyyar saka idonta cikin na shi ta faɗa masa wacece za ta ƙi namiji kamar shi? Sai dai kafin ta gama ɗagowar ya yi wuf da bakinta ya sumbata.
Ɗuf! Hadeeya ta yi dan yau ta gamu da gamonta, zazzaro ido ta yi a tsorace sai dai ba ta yi yunƙurin dakatar da shi ba, a hankali ya raba bakinshi da na ta yana kallon yanayin da ya jefata alamar dai sabon shiga ce, sake kashe mata jiki yayi da faɗin “Ki na sona Deeya?”
Yanda ta yi kiskirim ta kasa motsawa ya sa shi sakin murmushi yace “Haba dai babbar yarinya, ya ki ke abu kamar ba ki waye ba, kar ki badani mana.”
Ƴar dariya yayi mai sauti ya jawo kanta gaba-ɗaya ya manna a ƙirjinshi yana shafa kanta yace “Shikenan to ƙanwata, yanzu ki shiga ciki gobe da safe sai ki faɗa min shawarar da ki ka yanke.”
Ɗagata ya yi daga jikinshi ya buɗe mata ƙofar, jiki a mace ta fita kamar wacce aka ma dukan tsiya, saida ya ga shigewarta ya jawo ƙofar ya rufe yana wani munafikin murmushi ta gefen laɓɓa yana ayyana” Na san ma za ki amince, wannan tarkon ya fi ƙarfin tsallakewarki, da sannu zan samu sabuwar babyn da za ta dinga ɗebe min kewa.”
Dantse leɓɓenshi yayi yana jinjina kai sannan ya ja motar ya bar gidan, dan yau kam ba ya jin a zai kwana a gidan, duk da ba mata yake nema ba, shi dai barshi da ƴan wasannin nan da mace, dan a zaman da ya yi ƙasar waje ya koyi hakan, dan mutum ne mai ƙyamar hakan kasancewarshi likitan da ya karanci mecece mace? Yana matuƙar jin ƙyamar shiga hurumin da ba na shi ba, amma Hadeeya ya ga yarinya ce ɗanya shakaf, dan haka zai yi ƙoƙarin yi mata wayo ya fara buɗe hanyar da kan shi kafin ya gama tantancewa ya samo matar da ta dace da tsari da zubin yanayinshi da kuma tunaninshi. Duk da ya ga Ƴaƴar su Hadeeya ta ɗazu (Saleema) ta na da irin ƙirar da yake so, wato kakkauran jiki da kuma manyan mazaunai har ma da ƙirji, ama zai fara tabbatarwa kanshi wani bai fara kai ko da hannunshi a kan kayan ba kafin ya sallama mata.
Saida tatabbatar su Hadeeya sun yi bacci sannan ta miƙe daga kwancin da ta yi tana ta hango abunda idonta suka gane mata, ita a zahiri dai ba ta taɓa ganin kusancin mace da namiji fiye da haka ba bayan na matar Babansu da shi Baban na su sai yau, ƙiri-ƙiri Allah ya nuna mata Mu’awwaz da yarinyar da ba ta gama sanin me ye aikinta ba a gidan yana saduwa da ita a tsaye, a tsayen ma a jikin bango bayan ba matarsa ba ce. Alwala ta ɗauro ta zo ta kabarta sallah kamar yanda ta wa mamanta alƙawarin za ta ci gaba da addu’a dan Allah ya bata nasara a kan jarabawar da sukayi, sau biyu kenan ta na rasa wannan jarabawar, idan ta sake faɗuwa yanzu Hadeeya kuma ta yi nasara ba ta san me Abbanta zai mata ba.
Ƙarfe 02:30 na dare ta samu ta canza kayanta ta saka riga da wando na bacci sakakki sannan ta nufi inda Hameeda take dan gadon ɗaya Hadeeya ce da Ummee, ta kwanta kenan za ta ɗan ja bargo saboda sanyin acn ɗakin kawai ta ji an murɗa ƙofar alamar za’a shigo.
Zazzaro ido tayi mugun tsoro ya kamata da tunanin wa ye a wannan daren? Me ya zo ɗakin ƴan matan a wannan lokacin? Ƙurawa ƙofar ido ta yi saida ta ga an buɗo da gaske dai ana shigowa ta matsa da sauri ta haɗe a jikin bayan gadon ta kai hannu ta ɗan zungurar Hameeda dan ta tashi. Dake da kanta ta kashe wutar ɗakin sai mai ƙaramin haske, hakan yasa ya na shigowa suka haɗa ido, ai zabura ta yi tana neman durkowa a gadon tana faɗin “Kkk… Kai kuma? Malam…”
“Shiiiiiiii!” Ya ɗora yatsarshi a laɓɓanshi alamar tayi shiru, ta kan Hameeda ta wuntsila ta sauka a gadon tana sake nunoshi da yatsa tace “Ka ga malam ka fita a nan, ni ban ga komai ba kuma ba wanda zan faɗa ma, idan ma kasheni ka zo yi to ka yi haƙuri.”
Takawa ya ƙara yi har ya kai daf da gadon cikin raɗa yace “Saleema ki zo dan Allah za mu yi magana, ba cutar da ke zan yi ba.”
Da mamaki tace “Magana…” Da yatsa ya sake mata alamar “Shiiiii! Yi magana a hankali.”
Sassauta murya tayi tace “Maganar me za mu yi a wannan lokacin? Ka ga ni ba zan saurareka ba, kawai ka fita a nan wallahi ko na maka ihu.”
Da sauri ya durƙusa ƙasa yace “Dan Allah Saleema kar kiyi, ki zo muje mu yi magana, iya nan ƙofar ɗakina saboda bana so mu tashesu.”
Ƙura masa ido tayi kamar mai nazari, amma sai yayi saurin katseta ta hanyar haɗe hannayenshi alamar roƙo yace “Dan girman Allah Saleema?”
Da sauri ta ɗaga masa hannu tace “Shikenan to na ji, ka daina haɗani da ubangijina kan ƙaramin abu.”
Zagayowa tayi tace “Mu je to.”
Da sauri ya miƙe ya fita ƙofar ɗakin ya tsaya, jim kaɗan ta fito sam rikicewa ya sa ta manta ba ta fito da hijabi ba sai hular dake kanta kawai mu raga-raga irin ta bacci, sa’arta ɗaya kayan a sake suke basu fito da surarta ba.
Tsayawa ta yi jikin bango ta na satar kallonshi, ita wallahi kunyar kallonshi ma take ji, amma shi da alama ba haka ba tunda har ya zo inda ta ke, ɗan matsowa ya yi kusanta yace “Saleee..”
Ba ta bari ya ƙarasa ba ta ja baya tace “Ka ga ka faɗa min komai daga nan.”
Murmushi ya yi ya ɗan ƙarewa surarta kallo, to ai kayan da ke jikinta wanda bai san mace ba ne kawai ba zai fahimci irin kayan alatun da ke ɓoye a cikin suturar ba, amma shi da ya gama sanin sirrin ya gama hango komai, cikin sakin fuska yace” Saleema, abunda kika gani ɗazu na ke so ki manta dan Allah, sam ba abinda kike tunani bane, kuskure ne wallahi kula jiya ne ya fara faruwa, amma na miki alƙawarin ba zai sake faruwa ba, kuma dan Allah ki min alƙawarin ba za ki faɗa ma kowa ba?”
Wani kallo ta jefo masa da mamakin kalamansa tace” Kuskure? Mu’awwaz zina ka kira kuskure? Kasan kywa da Allah ma cewa ya yi karmu kusanceta bare har mu je ga inda take, kai ka je kusa da ita kuma ka abka, amma za ka ce kuskure?”
Girgiza kai tayi cike da takaici ta sake kallonshi tace”…
Allah ya na tsare duk wanda ya kamalta kare kanshi daga aikata alfasha.
Alhamdulillah.