ZAIN ABEED 8

Page 8…
Elegant Online Writers
Abeed na ƙoƙarin fita daga cikin ƙofar, Sara ta zame daga riƙon da yay mata kai tsaye kuma ta nufi ƙofar data fito tana kiran sunan “Twin” Abeed ji yay kamar an caka masa mashi a ƙahon zuciyarsa, tashin hankali ya shiga sosai, a hankali ya sanya hannunsa ya dafe forehead nasa dashi, wanda yake jin Tamkar zai rame gida biyu sbd tsananin ciwon da Yake masa, gashi Numfashinsa da ƙyar yake fita, hakan kuma ya fara taimakawa wajan tashin ciwon da yake fama dashi. Shiru yay yana kiran sunan Allah a zuciyarsa, azabar da ya keji a cikin jikinsa ba zai faɗo ba, sai wata zufa yake haɗawa jikinsa na wani irin vibration. Dattijo dake kulawa da yanayin Abeed yace “Muje kawai” sai a lokacin Abeed ya buɗe Manyan idanunsa da suka fara juyewa looking so sickness, kallon Dattijon yake ba tare da yace komai ba, Dattijon ya kama hannun Abeed ya fara tafiya dashi, kamar wanda aka tsikara yay tear out na maganar sa yace “kace zai mt wani abu?” Dattijo yace “Abin bauta kabas ya sahale masa kwanciya da ita, hakan kuma yana nufin ta zama matarsa” Abeed ji yay ya nemi raguwar numfashin nasa na wani lokaci ya rasa, Dattijo na ƙoƙarin magana Abeed ya zame hannunsa, ya nufi hanyar da yaga Sara tafi, yana tafe dafe da kansa. Sarki Mabus kamar yadda tsara yana zuwa yabi ta wani way wanda ba tanan ne yake bi ba, wannan dalilin ya sanya suka samu saɓani dasu Abeed, bedroom ɗin daya ajjiye Sara nan ya shigar da Sairah yana zaunar da ita yace “Duk jama’a ta ne a waje, kina fita za’a yanka ki” wani tsoro ya shiga zuciyar Sairah banda sunan Allah babu abinda take kira a Zuciyarta, Mabus kuma ya nufi wani sashe domin shirya wa, acewarsa zuwa na musamman zai mata. Sara kuma na barin wajan su Abeed ta shiga lalluban ɗaki, kana ganinta kasan ta samu prblm a cikin ƙwaƙwalwarta, tafiyar ma da ƙyar take, hakan ya sanya Abeed ya kusa cimmata, yana shigowa sashen tana shigewa wani bedroom, shi kuma kai tsaye ya miƙe zuwa sashen da Sarki Mabus ya ajjiye Sairah, Time Sairah tana zaune ta kasa ko motsawa banda kuka babu abinda take, motsin da taji yasa tayi saurin miƙewa tsaye, amma babu wanda ta gani kamar daga sama idanunta ya sauka akan wata wuƙa cikin sauri ta ɗauki wuƙar jikinta na rawa. Abeed dake tsaye nesa da ita tun shigowar sa shanyayyun idanunsa suka sauka a kanta, walking slowly ya nufi inda take kamar wanda aka tilasta wa, har daf da ita ya ƙarasa without making any sounds, shiyasa bama taji zuwan nasa ba, hannunsa guda ɗaya ya cire daga kansa ya ɗura a shoulder ɗin Sairah, Innalillahi wani irin ihu Sairah tayi tare da juyowa da sauri ta ɗaga wuƙar hannunta ta cakawa Abeed a cikinsa. “Ya Rabb” shine kalmar da Abeed ya samu damar furta wa, idanunsa akan SAIRAH wacce yay tunanin Sara ce, nan take kuma jini ya fara zuba daga jikinsa jiri na ɗaukan sa, daidai lokacin kuma Sara ta shigo ɗakin, duk da bata hayyacinta amma bai hanata ware idanunta ba, na mamakin ganin Sairah, ko zata mance da kowa banda twins ɗinta. Da ɗan saurin daya rage mata ta shiga cikin bedroom ɗin tana zuwa ta amshi wuƙar hannun Sairah wacce jini ya ɓata ta, daidai lokacin kuma Dattijo ya shigo cikin bedroom ɗin. A matuƙar kuɗi me ya nufi wajan Abeed wanda ya durƙoshe kan ƙafafuwan sa, idanunsa kuma suka shiga rufewa, cikin tashin hankali Dattijo yace “wace ta caka masa wuƙa a cikin su” Shiru Sairah tayi domin sai a lokacin da lura ba Sarki Mabus bane, Sara kuma bakinta ne ya kulle ba komai take iya cewa ba, wata ƙinƙina ta same ta, cikin tsawa Dattijon ya kuma cewa “nace wacece ta caka masa wuƙa a ciki?” Jikin Sairah na rawa ta ɗaga hannunta tare da nuna Sara, Kallon Sara Dattijon yay ga wuƙar nan a hannunta tana ɗigar da jini, Sara da mamakin ƴar uwarta ya kamata ta kasa cewa komai, bata taɓa tunanin a rayuwa Sairah zata iya aikata mata wani abu ba, sai gashi ta haɗata da sharrin da babu mai iya wanka ta, Sairah ta ƙara cewa “ban san me yay mata ba, amma tace idan har bata kashe sa ba hankalinta ba zai kwanta ba” slowly Sara ta dinga girgiza kanta, so take tace ba ita bace, amma ta kasa bakinta sai rawa yake, Dattijon yace “Kin aikata babban kuskure kuma zaki amshi hukuncin ki” yana faɗin hakan ya nufi wajan Abeed da ƙyar ya iya ɗaga sa, domin gaba ɗaya jikinsa ya saki, jansa ya fara yi zuwa waje, suna zuwa daidai inda Sara take Abeed ya miƙa hannunsa, tare da kama hannun Sara da kyau, yadda Dattijo ke jan Abeed haka Abeed ke jan Sara, har suka fita daga cikin sashen kana suka fita daga cikin Masarautar Zahel baki ɗaya..Suna fita Sairah ta saki ajjiyar zuciya, bata da wani zaɓi wanda ya shige tace ƴar uwarta ce ta aikata hakan, domin tasan idan tace itace babu shakka kasheta za’ai, bata taɓa tunanin zata ƙara ganin Sara ba, ashe itama tana gidan, babu mamaki da gayya ta tafi ta barta, fita tayi ɗaga daƙin ta fara tafiya babu jimawa ta haɗu da Kuyangin Gimbiya Noro Wanda ta aiko su duba mata Sairah, suna ganinta kuwa sukai wajan Gimbiya Noro da ita….Cikin ikon Allah inda Abeed ya ajjiye motarsa a nan suka sameta, babu abinda akai mata ba wanda ya lura da ita ma, Abeed wanda bai san me yake faruwa ba, domin ya jima da fita hayyacinsa, Dattijo ya samu wani ganye ya rufe wajan da yake zubar da jini kana ya ɗaure masa wajan da wani yadi, bayan motar ya buɗe ya saka Abeed kana ya saka Sara a gaba, shiga kuma ya shiga mazaunin driver da wani irin gudu yaja motar tare da nausawa cikin jejin ya ɗauki hanyar fita daka garin Zahel baki ɗaya….
Zain ne kwance tun bayan tafiyar Abeed yake bacci, wajan kwana uku ke nan, A hankali ya shiga motsa hannunsa da sukai masa nauyin gaske, idanunsa ya buɗe kallonsa ya sauka akan A.cn bedroom ɗin nasu, ƙara buɗe idanuna yay ganin yanzu 2:30 amma har yanzu yana bacci baiyi ko sallah ba, Miƙewa tsaye yay yana jin jikinsa ba daɗi, mood ɗinsa duk ya sauya, toilet ya shige ya sakarwa kansa shower, kana yay alwala ya ɗaura towel ya fito, he just thinking ina biyuninsa ya shiga? Ko yana wajan Naila? Ko kuma studio ya shiga, da wannan tunanin ya shirya cikin wata tattausan Farin yadi mai kyau, Wayarsa ya duba yaga babu, kai tsaye ya nufi waje, da mmkinsa sai yaji ƙofar a buɗe, girgiza kai yay yace “Na san duk Abeed ne, tunaninsa idan na tashi zan shiga wani wajan na barsa” wani spare key ya gani can bayan deep frizeer, buɗe ƙofar yay ya fita, kai tsaye Masjid ya nufa, bayan ya yi sallah ya koma part ɗin Mai martaba, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga, gaba ɗaya suka ɗaga kai suka kallesa, Naila tace “To sannu waye daga cikin ku? Dan wlh ba wani imani ne daku ba, yanzu sai ku cuci mutum” Zain ya shafa kansa yace “A’a daman Abeed baya nan?” Amma tace “ba tare kuke ba?” Zain na zama ƙasan carpet yace “I’m just woke up, so I hve no idea where he is…” Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas da idanunsa suke kan wasu ducoments, ya gyara zama a sanyaye cike da tarin nutsuwa, ya ɗaga idanunsa ya kalli Zain cikin Muryar nagarta yace “Yaushe duk muka zama sa’aninka Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas?” Zain ya sunkuyar da kansa ƙasa yace “I’m sorry Abba, amma ni daga bacci na tashi” da tarin mamaki Amma da Abba suke kallon Zain, Naila tace “Wai Uban waye a cikinsu su babu ne yanzu? A’a ni bana son harkar munafurci mai yi ma Allah ya tsine..” Amma da jikinta yay sanyi tace “Abeed ne” Miƙewa Naila tayi tace “A’a daman, ai duk na kwana da sanin yaron nan ni kaɗai nake ƙaunar sa, ina tare daku ne kawai,amma bani da tabbaci da zuciyar ku, to idan na yarda Allah ya tsine, yanzu yanzu a fito min dashi” Calmy Amma tace “Zain Abeed da kansa ya kira Abbanku yace kuna da tafiya ta kwana 3 zuwa 4, amma ka nuna like you don’t know anything about..” shiru Zain yay, yama rasa me zai ce, bai san dalilin daya sanya Abeed ɗin yay haka ba, yana ƙoƙarin mgn telephone line nasu ya shiga ringing, Zain ne ya ƙarasa wajan ya ɗauki wayar, daga can ɓangaren aka ce “Aminu Kano teaching hospital ke mgn” gaban Zain ya faɗi, jin yay shiru yasa mutumin yace “Fatan muna magana da familyn King Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas?” Da sauri Zain ya juya suka haɗa ido dasu Amma, Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas kansa a ƙasa, Naila da jikinta har rawa yake tai saurin ƙafa bakinta a wayar tace “Mai ƙarya a ƙona shi a wuta, nifa bana yarda da wannan sailolar, a to! Mane haɗi na ma da ita, ba dangin iya balle na baba masifar bature ce kawai, maza tambaye mai magana ƙilan cewa zatai suka shiga Shelalen nawa” A hankali Zain yace “Am on my way..” yana faɗin hakan ya kashe kiran, juyawa yay fuskarsa ɗauke da Murmushi yace “Abba, Amma kun haifi yara har yanzu kun kasa gane su, ina sane na buga wannan game ɗin, Jiya da daddare muka dawo Abeed na can yana bacci bari naje” Naila tace “Muhammadur Rasulullah s.a.w, maza maza nemi tuba wajan Ubangiji, aini ina sane na nuna sam ban haɗa dangi da kai ba, so nake gantalallun iyayen naka su gane ka da kan ka” Zain ko juyawa bai ba, tsoro duk ya cika zuciyarsa, yaje bakin ƙofa tace “Nace to furar taka fa? Ko na bawa Tattabarunka?” Still shiru yay mata ya fice daga part ɗin… Numfashi Mai martaba ya sauke a hankali yace “liar” Amma tace “Sorry?” Mai martaba yace “he’s laying, akwai abinda yake ɓoyewa” Amma tace “Kana nufin Zain ne wannan?” Mai martaba ya gyara zama yace “Kin taɓa jin Abeddeen yay Mgna mai tsayin haka? Fara’ar da Zain keda ita Abeed babu, ina da tabbacin da Abeed ba zai faɗi ƙarya ba, yana zuwa kuma wajan Naila zashi” Amma tace “something is fishy”.. parking Zain yay a harabar asibitin cikin sauri ya fito yau ko mutum ɗaya babu mai basu tsaro, kai tsaye Emergency ya shiga, ya tambayi Abeed nan take akace “yana male surgical world, room 13” yace “thank you” ya nufi wajan. Abeed da farkawar sa kenan ya kansa kwance akan gadon asibiti ya ruwa a jikinsa, idanunsa ya runtse sosai nan take abinda ya faru ya shiga dawo masa, da ɗan sauri ya buɗe idanunsa ya kalli Dattijo yace “Ina take?” Dattijo yace “she’s outside, yanzu nake shirin bada report akai azo a tafi da ita” wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Abeed ya sauke yana maida idanunsa, kamar ba zai mgn ba sai kuma yace “bar mgnar between i and you” Dattijon yace “To! To Shi ke nan Allah ya baka lafiya” Not too long Dr Adyan ya shigo room ɗin da files a hannunsa, hakan yasa Dattijo ya fita waje zuwa inda Sara ke zaune, Dr Adyan ya zauna akan kujera bayan ya duba drip ɗin dake jikin Abeed a hankali yace “Nai mmkin inda ka sameta, almost 10yrs ina bincike sai gashi kai da kan ka ka sameta, I’m happy for you frnd” Abeed ya taɓe baki har lokacin baya jin daɗin jikinsa kafin yace “I alrdy make my decision” Dr Adyan yace “for…?” Abeed ya numfasa yace “Zan bawa Zain aurenta” wani irin zare ido Dr Adyan yay yace “hve You absolutely lost your mind? Kasan me kke cewa? Sadaukarwa zakai ke nan?” Abeed ya haɗe fuska yace “Mind your own business, ni yanzu duk macan dana aura nan kusa zatai takaba” Shiru Dr Adyan yay zuciyarsa cike da tausayin Abeed, a ɓoye Abeed na son yi aure, amma tausayin halin da zai bar wacce zai aura shine yake nunawa sam bai damu da wani abu aure ba, Amma akwai babban kuskure idan har Zain ya auri yarinyar nan” Dr Adyan yace “Abinda da likita yace ba shine gsky ba, Ubangiji na iya sauya ƙaddararka cikin ƙaramin lokaci kaga an samu maganin ciwonka, amma bawa Zain aurenta ba shine daidai ba, yin hakan na nufin faruwar wani abu” Abeed yace “Uhm” Dr Adyan yace “To a yanzu ma, ai tafi ka buƙatar taimako yanzu time ɗin daya dace ka riƙeta hannu bibbiyu” Abeed ya numfasa yana jin zuciyarsa ba daɗi kafin yace “Zan bawa Zain aurenta, i don’t even know her name, bare kai tunanin wani abu, taimin ƙanƙanta ko aure ne, abinda ko..” Sai kuma yay shiru, Dr Adyan yace “Ko mene? Ni komai na ƴar da ake buƙata babu abinda bai fito a jikinta ba, da dai tun lokacin baya ne” Daidai nan Zain ya buɗe ƙofa ya shigo, cikin sauri yace “what happened to u Biyuni?” Shiru Abeed ya sai riƙe hannunsa kawai da yay, Dr Adyan ne yace “cikin dare ya biyo hanya yaga wata yarinya na buƙatar taimako, shine ya tsaya ashe akwai ƴan ta’adda ɗaya daga cikinsu ya caka masa wuƙa, zama kaga ƙyakkyawar yarinyar a waje” jin Dr Adyan yace Ƙyakƙyawa yasa Abeed watsa masa wani kallo tare da jan tsaki a zuciyarsa, Zain yace “Subuhanallahi, ni Abeed kamar na taɓa ganin photon Yarinyar a wayarka…