NOVELSUncategorized

DA AURENA 2

Page 2 

Cikin sauri tafada wani gida ta maido kofa ta rufe ta cire hijab dinta ta fada dakinta ta kwanta saman kujera 
Tabbas ina matuqar Qaunarka Yusuf amma yaxan da wannan jarabawa data sameni 

Anya inada hankali kuwa da nafara sonka tabbas akwai tashin hankali sosai agabana Wanda bansan iyakar inda xai tsayaba 
Tib tib taji alamar shigowan mutum a falon tai masa kallo daya ta maida kanta ta kwantas saboda idan tana cikin tunanin Yusuf bata Qaunar ko kadan taga gilmawai Amadu a idonta 
Mintuna kadan ya fito yasake gittawa ta gabanta ya fice ta girgixa kai ta koma tunanin hanyar da xata sake ganin Yusuf 
Sallamarsa taji cikin matuqar murna ta rufe eyes dinta alamar barci take tanajinsa ya daga labulen dakin ya xubamata ido yana murmushi yasake wata sallamai amma taqi motsawa cikin tafiyansa ta isa da taqama yashigo falon ya duqo fuskansa dai dai nata yana jin yanda take fidda numfashin ta ya lumshe ido yasa hannu ya shafa fuskarta yai mata kiss a kumatunta ina matuqar qaunarki wadda bansan sanda na afka cikintaba yasake shafa mata fuska yana qarema fuskanta kallo ita kuma taqi bude idonta wai barci take da Gaske 
Murmushi yayi nasan kina jina sai dai nima baxanso kifarkaba Dan kada nadaina ganin wannan kyakykyawan fuska nakiba Dan sainaga kinfi kyau ahakan yana magana yana shafa fuskanta ahankali yana xagaye bakinta da yatsansa 
Ganinba xai dainaba ta bude idonta dontasan baqaramin aikinsabane yai abunda yafi hakanba
Dariya yai mai qarama fuskansa kyau dama nasan ba barci kikeba Dan naga fitarsa yanxu ai baki isayin barciba kawai kinamun rowan ganin wannan idanuwan masu saukar da nishadi garenine kawai
Dariya tayi sosai Wanda yasaki baki da hanci yana kallonta ji yake tamkar ya rumgumeta yanda dariyanta kesaukar masa da kasala a jiki amma yasan baxata bariba koda yake xai jure akwai lokaci
Ahankali ta daina dariyan ta dauke hannunsa dake bisa cinyarta tamike tsaye taje wajen wani lungu ta dauko wata kula ta miqa masa batare datai maganaba kin ansa yayi kinsan baxan ansaba saikin bude naga miye ko 


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Murmushi tayi ta bude kulan saiga faran shinkafa da mai da yaji da maggi mai Star guda bisa kagani saika ansa ko malam dariya yayi baxan ansaba kije kidauko cokali kixo muci Dan yunwa nakeji daman sosai 
Kallon kafiye rigima taimasa kasanfa naci nawa wannan nakane daxun naso nafadama muka rabu ba bankwana 
Yatsine fuska yayi kekika jiyo nidai anji abunda nafada Dan haka in anaso naci aimun yanda nace idan kuma bakiso to wlh xan kwana da yunwa nasan xakiyi farin ciki ko ya kalleta sosai yanason yaji abun da xatace 
Kallon dai taimasa na kafiye rigima ta aje kulan ta nufi wani qaramin daki ta dauko cokali biyu ta dawo 
Dariya yasa mata kina nufin kowa da nasa wai baki isaba da guda xamui amfani nidake sannan kexakiban Nima na baki Indai kinason da gaske naci abincin ga yunwa inaji kinsan inada ulcer shiru tayi kanta a qasa tanajin rigimar da yakemata yau kuma tasan baxata iya barinsa da yunwa ba gara ace ta kwana bata cibada ya kwana da yunwa saboda shine kawai kesata farin ciki yaxama dole itama tasakasa koda bata son abunda yasata yaxama tilas ta jure taimasa 
Kallonta kawai yake yana qara yaba kyan jikinta Dan ba qarya Huwailat kyakykyawace ajin farko a cikin mata Allah yabasa dama r cika burinsa kanta koda yake bakowane namiji xai samu kamar Huwailat yarabu da itaba sai marai rabo amma kuma ai ba a maraya sai raggo Dan haka xai jure xai dake harya sameta cikin nuna jin haushi yatashi ya nufi qofa bata San sanda ta jawo rigansaba yadawo baya pls Karka tafixan baka murmushi yai yadawo yaxauna yabude bakinsa dariya tayi ta girgixa kai baka gudun wani yashigone kallon ko a jikina yaimata ahankali taxuba masa abincin a bakinsa cikin taqama yake cin abincin yanata basarwa ya ciko cokali yanufi bakinta batada yanda xatai tabude bakinta yasaka mata ahaka dai sukaita cin abincin harya qare tabashi ruwa yasha 
Yakalleta xanje wani waje nida Abbas saina dawo cikin shagwaba tace firako 
Haba wane fira xani inada kamarki ba firabane sainadawo xan fadamaki har bakin kofar gidan ta rakasa tana daga masa hannu shima yana dago mata har suka daina ganin juna takoma ta hada kayan ta wanke 


Wacece Huwailat waye Yusuf waye Amadu 


Kubiyoni Haupha danjin wannan amsar 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button