BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

“Kenan kinaso kice min in barshi ya taɓa min jiki a banza? Kinsan halin sa ɗan iska ne idan har ban taka mishi birki ba gobe ma sakewa zai yi, yaje yayi duk abinda zai yi ta Allah ba tashi ba, mtswww ke kike jin tsoron sa”.

Tana faɗin hakan tawuce tabar ta nan, biyo bayan ta itama tayi tana kiran sunan ta, ita ko bata kula ta ba tabuɗe Gate ɗin tashige, babu wasu mutane cikin school ɗin sai ƴan tsiraru, Direct class ɗin su da yakasance s.s3 suka wuce.

.

_To fa me zai faru?_????

*Comments & share plz*

[9/1/2020, 4:35 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *⚜{{F.W.A????}}*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 9*

“Mom wai yaushe Dad zai dawo?”

Shafo suman kanshi tayi tace

“Inaga sai gobe zai dawo, amma kaneme shi ta waya mana”.

“Ok”.

Mom tace “ɗazu Sameer yake sanar dani jibi tafiyan ka ko?”

Gyaɗa mata kai kawai yayi yana gyara zaman shi

“Ok Allah yakaika lafiya, kadai ta addu’a banaso kana wasa da addu’a, kasan aikin nan naka akwai maƙiya sosai dole sai kariƙa neman kariya wajen Allah, nima ina nan ina tayaka, Allah yamaka albarka yasa kafi haka Autana”.

Murmushi Khalil yayi yace

“Ameen Mom, dama Ina so ince miki zan dawo da Nazeefa wurinki sai tazauna anan”.

“Ok ai babu damuwa kadawo da ita, dama nan ɗin yafi dacewa kakawo ta, yanzu katashi muje kaci abinci tunda an gama”.

Be musa mata ba yamiƙe yanufi wajen dainning ɗin, itama biyo shi tayi suka zauna a jere sannan tayi saving ɗin sa, yasoma cin abincin ita kuma tana masa hira, shi kuma sai dai yasaurare ta da kunni kawai wani lokacin kuma yana gyaɗa mata kai.

         ******

Shigowan ta sau biyu cikin ɗakin tana ganin ta kwance, sai dai ta kasa aiwatar da abinda tazo yi ɗin, yanzun ma har zata koma sai kuma tayanke shawaran kawai zuwa, ahankali tatako tazo bakin gadon tasami waje tazauna, shiru tayi don ta rasa ta ina zata fara, ba kasafai suke magana ba tun kwana biyu da zuwanta cikin gidan, daurewa tayi dai ahankali takira sunan ta

Nazeefa da idanuwanta ke kulle sai dai ba barci take yi ba, hakan yasaka tabuɗe idanunta tabi Lubnan da kallo, sai tasakar mata murmushi tace

“Na ganki shiru ne tun ɗazu, shiyasaka nace ko zakizo kiraka ni zanje gidan mu kar in fita in barki ke kaɗai”.

Itama murmushi tayi mata sannan tatashi zaune tace

“Ai babu damuwa anty, muje in rakaki, dama zaman ya ishe ni haka”.

Murmushin samun nasara Lubna tayi tatashi tana faɗin

“To muje ko”.

Miƙewa Nazeefa tayi taɗau hijabinta dake ajiye saman gadon tasaka, tabi bayan Lubna da har tasoma tafiya zata fice a ɗakin, ahankali take takawa sai dai tafiyan ta ba normal take yin sa ba sabida aikin dake cikin, hakan yasaka take ɗan duƙawa kaɗan, fitowa sukayi daga cikin gidan suka tunkari bakin Gate, har suka ƙarisa babu kowa, shima me gadi ya zagaya baya, don haka kai tsaye suka tunkari ƙofan Lubna tabuɗe suka fice

Daga can nesa wata baƙar mota ce aka faka, ba’a ganin cikinta ko kaɗan, tunda suka fito Lubna tahango motan don haka Direct wajen suka nufa, ita dai Nazeefa sai bin bayanta take yi tana yi tana kalle-kallen tsarin wajen, gaba ɗaya layin gidajen masu kuɗi ne kamar g.r.a haka layin yake.

.

_shin me zai faru????? Ina Lubna zatakai Nazeefa?_

_ku bini asannu don jin me zai faru._

*More comments more post* ????????????????????????????????????????????????????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️

[9/2/2020, 1:47 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *⚜{{F.W.A????}}*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

    *CHAPTER 10*

Har sunyi rabin wajen motan sun kusa isowa sai ga motan Khalil ta shanyo kwana, ahankali ya’iso wajen su yatsai da motan yana zuge glass ɗin motan, tsananin ruɗewa Lubna tayi har batasan sanda tazaro idanu waje ba tana kallon shi kamar yanda shima ɗin yake bin su da kallo, sai da yagama ƙare musu kallo kafin yasauke idanunshi kan Lubna wacce tagama tsurewa yace

“Me yafito daku nan?”

Gaba ɗaya ta rasa ma me zatace sai duƙar da kanta da tayi tana jin ƙirjinta na bugawa kamar zai faso waje

“Kushiga mota”. Yace dasu yana ɗauke kan shi daga kallon su

Nazeefa ce tafara buɗe gaban motan tashige, ita kuma Lubna jikinta na rawa tabuɗe baya tashige, jan motan yayi slowsly yanufi gida, sai da yayi hon har sau biyu kafin Gateman yabuɗe masa, kutsa hancin motan yayi ciki ya’isa har packing space, bayan ya tsai da motan gaba ɗayan su suka fita sukayi cikin gidan, yayinda shi kuma yatsaya cire wayan sa dake chagi yafito, Direct wajen me gadi yanufa, tun sanda me gadi yahango shi yanufo shi dasauri yana faɗin

“Ranka yadaɗe Barka da zuwa, sannu da dawowa”.

Fuskar shi aɗaure yace dashi

“Meyasaka kabar Nazeefa tafice cikin gidan nan?”

Me gadi da mamaki yacika shi yace

“Nazeefa kuma ranka yadaɗe? Ai banga tafita ba, wlh bansani ba ranka yadaɗe”.

“Kenan wasa kake yi da aikinka ko? Ina kaje har tafita cikin gidan nan baka sani ba?”

“Wlh ranka yadaɗe wlh bansan tafita ba, kuma wlh babu inda naje in banda zagayawa da nayi”.

Khalil soka hannun sa yayi cikin aljihu yana kallon sa yace

“Kakula da aikinka bana son wasa, idan har kana min irin haka tabbas zamu sami matsala ni da kai”.

“To ranka yadaɗe insha Allah, ayi haƙuri bazan sake ba”.

Be sake cewa komai ba yajuya yatafi, yana shiga cikin Palon babu kowa Direct ɗakin su yanufa, yabuɗe yashiga yana bin su da kallo har yanzu fuskar shi a ɗaure, yayinda su ma kallon shi suke yi suna zaune tsamo-tsamo saman gado musamman ma Lubna da tagama tsorata da yanayin shi

“Meyasaka kuka fita cikin gidan nan? Ina zakuje?” Yayi tambayan yana kallon Lubna da idanuwansa masu kaifi da burgewa

Cikin rawan murya tabuɗi baki tace

“Uhm dama.. dama zamuje gidan mu ne”.

Wani kallo yayi mata me cike da ma’anoni sannan yace

“Kar in ƙara ganin kun fita cikin gidan nan, idan har gida kikeso kije kifaɗamin zan saka drever yakai ki, kuma ke kaɗai zaki fita karki soma janta kufita tare, kina jina?” Yaƙarike maganar da kakkausan murya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button