BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

Atare suka gyaɗa mishi kai, har Nazeefa da itama tagama tsorata dashi domin bata taɓa ganin shi ahaka ba, shi mutum ne me sauƙin kai ba kasafai yake nuna fushin shi ba
Juyawa yayi yafice yanufi ɗakinsa, akan gado yazauna yasoma cire Combat ɗin ƙafan sa da socks ɗin sa, sai da yagama yacire farar suit ɗin dake saman farar rigan ciki ya’ajiye, ahankali yazuge necktie ɗin wuyan sa yacire gaba ɗaya ya’ajiye, agogon hannun sa yacire itama ya’ajiye sannan yakwanta yana lumshe idanun sa, yayinda ƙafafunsa ke ajiye a ƙasa gangan jikin sa kaɗai ke saman gadon, tunani kawai yake yi cikin ran sa har be san sanda time yaƙure masa ba, miƙewa yayi ahankali yanufi cikin Toilet, wanka yasoma yi kafin yaɗauro alwala yafito, Direct gaban mirror yanufa yazauna, sai da yawarware shawul ɗin dake kan sa sannan yasoma goge kan, bayan ya gama yabusar da kan da handrayer sannan yasoma shafa Expensive lotions ɗin sa, har gashin kan sa sai da yashafe su da mayuka masu tsananin ƙamshi da ƙara taushin suma, yaɗau kumb yataje gashin yagyara shi yayi matuƙar kyau, kana yamiƙe yanufi sif ɗin sa, wata farar riga me gajeren hannu yaciro sai blue jeans yasaka, da alamu dai shi ma’abocin son fararen kaya ne, wrest watch ɗin sa da Combat ɗin ƙafan sa duk farare ne yasaka, sai da yagama gyara jikin sa yafeshe ko ina na jikin sa da farpume’s ɗin sa masu ƙamshin daɗi kana yaɗau wayan sa da car keey yafito, fita yayi yanufi wajen motan shi yashige yaja yana danna ma me gadi hon, ba ɓata lokaci yabuɗe masa yafice, sai da yatsaya bakin masallaci yafita yayi sallan asar kafin yakoma yaja yatafi
A bakin gidan Brr. Tahir yatsaya yaɗau wayan sa yakira sa, babu jimawa shima yafito yashiga cikin motan yaja suka tafi, a wani madaidaicin gida suka tsaya wani mutum yafito daga gidan yayi musu jagora suka shige ciki, tattaunawa sukai tayi akan aikin su har wajen magrib suna tare, sai da sukayi sallan magriba da isha’i kafin suka rabu, har gida Brr. Khalil yasauke Brr. Tahir kafin shima yakamo hanya zuwa gidan shi.
Koda ya’isa kai tsaye ɗakin shi yawuce, yacire kayan jikin shi yabar wandon da singlate yafito palow, a saman sofa yazauna yana ɗaukan remote yakunna t.v, sai kuma yatashi yanufi kan dainning yahaɗa tea me zafi yadawo yazauna, yana sipping tea ɗin idanunsa na kan t.v, ahaka har yashanye sannan yatashi yamaida cup ɗin saman dainnig, kashe kallon yayi yakashe komi na na’ura dake cikin palon yanufi ɗakin sa, wanka yayi yasauya kayan barci, yazauna bakin gado yasoma aiki cikin computer ɗin shi, wajen ƙarfe 11:56pm yagama sannan yakwanta.
…….. …….. ……….
*WASHE GARI*
Ƙarfe 03:10pm yatashi daga aiki, ya fito cikin office ɗin sa yana rufewa itama Bilkisu tafito daga office ɗin ta, har tagama rufe nata office ɗin shi be gama ba, sai tatsaya tana kallon shi har sanda yagama yajuyo sukai ido huɗu, dasauri yaɗauke kan sa yasoma takawa yana barin wajen, itama biyo bayan shi tayi har zuwa inda ya’ajiye motan sa, yana ninyan buɗe motan yatsinkayi muryan ta abayan shi
“Dan Allah kasauke ni agida mana, yau banzo da tawa motan bane, kuma gashi ana jirana Uncles ɗina sun zo daga garin mu”.
Juyo da kansa yayi yakalle ta sai kuma yataɓe baki yabuɗe motan sa yashige, hakan yasaka itama tazagaya dasauri tabuɗe gaban tashiga, be ce mata komi ba yakunna motan yaja suka fice, shiru cikin motan babu wanda yayi magana, sai dai ita tana yi tana satan kallon shi, sosai yayi mata kyau yau ɗin cikin shigan sa da yasaba yi koda yaushe, suit ne kalan ash da ƴar cikinta milk colour, haka komi da yasanya sun kasance milk ne har ta da Expensive wrest watch ɗin da yaɗaura a hannun sa
A bakin Gate ɗin gidan su yatsai da motan, ita kanta batasan an kawo ba sai da taji tsayuwar motan, kallon gidan su tayi sai kuma takalle shi don bata zata zai iya gane gidan nasu ba duk da zuwan sa sau ɗaya ne, tun farkon fara aikin su tare lokacin tanemi yarage mata hanya, cikin sanyin muryan ta me daɗi tace
“Nagode..”
Sai kuma tayi shiru tana wasa da hannun jakan ta, ɗan ɗago kanta tayi takalle sa idanuwanta na cikowa da hawaye tace
“Har yanzu dai bazan daina nuna maka ƙaunar da nake maka ba, ina ƙaunarka Ib, ina ƙaunar ka sosai, ni kaina bazan iya juran yanayin da natsince kaina aciki ba shiyasa nakasa ɓoye ƙaunar da nake maka, don Allah koda sau ɗaya ne tak a rayuwa kafurta min kana sona ko zuciyata zata sami sukuni, Allah ne yaɗaura min ciwon son ka kuma kai kaɗai ne zaka iya min maganin ta, har yanzu har gobe bazan gaji ba Ib, ina matuƙar matuƙar ƙaunarka”.
Tana kawo nan azancen ta tayi shiru tana jan numfashi, sai kuma tabuɗe ƙofan tafice, idanuwan shi yaɗago yabi ta da kallo, tafiya take yi tana share hawayenta da gefen gyalen ta har tashige cikin gidan nasu, kafin shi kuma yaɗauke idanun shi yana sauke ajiyan zuciya, ya sani duk acikin ƴan matan da suke nuna masa ƙauna ba wacce takai Bilkisu, yasan da cewa ita ɗin ta daban ce cikin mata, tana da hankali da nutsuwa, gata kyakkyawa babu abunda tarasa, sai dai ko kaɗan shi soyayya bata burge shi, tunda yake be taɓa son wata ɗiya mace ba, be san ma ya ake soyayya ba, shi dai kawai yasan da cewa mata suna matuƙar bashi tausayi, sosai yake jin ta cikin ran shi sai dai bazai iya yin abinda take so ba
ahankali yaja motan sa yaci gaba da tafiya, zuciyan sa cike fal da tunanin ta.
.
*Comments*
*Vote*
*Share*
[9/3/2020, 2:24 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*⚜{{F.W.A????}}*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 11*
A Compound ɗin gidan sa yayi packing ɗin motan, tsawon mintuna 5 yaɗauka kafin yabuɗe murfin motan yafito, ahankali yake tafiyan nasa cike da salon burgewa har yakai bakin ƙofan main Palon yabuɗe yashiga yana motsa bakin sa, babu kowa ciki sai ƙaran T.v plasma da yacika cikin Palon sai aiki yake yi shi kaɗai, Direct ɗakin sa yanufa yashige yarufo ƙofan, asaman gado ya’ajiye briefcase ɗin sa, yazaro wayoyin sa dake aljihun wando yazube su akan gadon, sannan yacire links ɗin rigan sa yakuma cire agogon hannun sa yabuɗe drower yasaka, zama yayi saman gadon yaɗau wayan sa yalatsa yakara a kunni
“Kihaɗa ma Nazeefa kayanta kice tajira ni a palow”.
Abinda yafaɗa kenan yatsinke kiran ya’ajiye wayan, tashi yayi yanufi Toilet yasillo wanka yafito ɗaure da towul ajikin sa, duk jikin sa ruwa ne ke ɗiga haka yanufi gaban mirror yazauna a stool, shiru yayi yana kallon kan shi a madubi, kyakykyawan surar jikin sa yake bi da kallo na tsawon lokaci kafin yaɗauke idanun sa, sai kuma yamayar da idanun nasa yana ƙare ma beauty face ɗin sa kallo, ya daɗe ahaka shi kan sa be san meyasaka yake kallon halittan nasa ba, amma dai yasan da cewa shi kan sa yana tsananin burge kan sa, komi nasa me kyau ne musamman ma ƴan manyan idanuwan sa masu ɗaukan hankali farare ƙal dasu, da yawa ƴan mata suna nuna masa matuƙar ƙauna kamar su cinye sa, tun yana ƙarami haka yataso me farin jinin jama’a kowa son sa yake yi ba mazan ba ba kuma matan ba, shi ba mutum bane me yawan shiga abun da babu ruwan sa kuma ba me yawan magana bane shiyasaka wasu suke ce mishi me girman kai, kuma ba haka bane sai dai in baka zauna dashi ba, anan ne zaka fahimci halin sa sosai yake da kirki da sauƙin kai.