BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

Ajiyan zuciya yasaki yasoma shafa Lotions ajikin sa, bayan ya gama sai yaɗau kumb yataje suman kan sa yakwanta luf sai shaining yake yi, kai da gani kasan sosai kan yake shan kuɗi wajen gyara, miƙewa yayi yanufi sif ɗin sa yaciro kayan sa, sanya wa yayi yana gyara wuyan rigan tare da ɓame bottles ɗin, yadi ne fari ƙal tamkar tissue har singlate ɗin da yasaka ciki ana gani, sun bala’in ɗaukan golden skin sa, sosai sukai mishi kyau, sai da yafeshe jikin sa da farpume’s ɗin sa sannan yasaka Black cover shoes a ƙafafun sa, yanufi gaban gadon sa yaɗau wayoyin sa da mukullin mota yatako yabuɗe kofa yafita

Dasauri taɗago kanta takai duban ta gare sa, haɗa idanun da sukayi yasaka hawayen dake maƙale a kurmin idanun ta daman zubowa, saurin ɗauke kanta tayi taduƙar dashi ƙasa, sosai tashiga damuwa tun sanda Lubna tasanar mata da abinda yace, duk da batasan ina zai kai ta ba but ko kaɗan bata son rabuwa dashi, bata son tayi nesa dashi, a ɗan zaman da tayi na kwana uku rak cikin gidan sa yafiye mata sauran tsawon shekarun da tayi a duniya, zaman ta gidan sa tamkar wani haske ne cikin zuciyarta

Muryan sa da yadoki kunnin ta shi yadawo da ita duniyar da taburma

“Tashi muje”.

Abinda yafaɗa kenan yayi gaba, itama kuma ahankali tamiƙe tajanyo trollyn kayan ta tabi bayan sa, lokacin da ta’isa jikin motan har ya shige ya bar mata Boot abuɗe, ɗaya daga cikin ɗan aikin gidan shi ya’amsa trolly ɗin yasaka a Boot ita kuma tabuɗe gaban motan tashiga, keey yayi ma motan yaja ahankali yafice daga gidan, cikin motan ma babu wanda ke magana cikin su, Nazeefa kaɗan-kaɗan take ɗago kanta takalle shi tana sharan hawaye, tuƙin sa yake amma duk yana lura da ita, kuma akan idanun sa ɗazu hawayen ta yazuba, ahankali cikin cool voice ɗin sa yace

“Lafiya kike kuka?”

Tambayan ba kaɗai yashige ta ba don batayi zaton yasan tana yi ba, ɗago kai tayi takalle shi, sosai yayi mata kwarjini da cika idanu, sauke kanta ƙasa tayi tana ɗan saka yatsa tashare sauran hawayen nata, bata iya buɗe baki ba bare tabashi  amsa, hakan yasaka tayi shiru don batasan me zatace ba, shima ɗin be sake tambayan ta ba, sai can kuma da sukayi nisa yace

“Ko dai ciwon ki ne ke miki zafi?” Yafaɗa maganan kamar me raɗa yana kallon ta

Sai da taɗago kai takalle sa sannan yakau da kanshi, cike da sanyin murya tace

“A’a, bana son rabuwa da kai ne yaya”.

Jin maganan yayi ta ɗan duke shi, hakan yasaka yasake kallon ta sai kuma yaɗauke kai yamaida ga titi

“Kidena damuwa Nazeefa ba wani waje zan kai ki ba, wajen Mahaifiyata zan mayar dake zaki fi samun kulawa, ke yarinya ce yakamata ace akwai wacce zata riƙa kula dake, zaman ki gidana akwai takura da yawa, ki kwantar da hankalinki nasan kina tunanin ko mun rabu kenan”.

Ahankali tagyaɗa masa kai tana ƙara share sauran hawayen nata da suka zubo mata, sosai taji zuciyar ta tayi sanyi, sai dai tafi ƙaunar zama agidan sa fiye da wani waje

A bakin Gate ɗin gidan yatsaya yayi hon kafin aka buɗe masa yashiga, bayan yayi parcking fitowa sukayi, sai da yabuɗe Boot yaciro mata trolly ɗin ta kafin suka nufi cikin gidan, Mom na zaune a palow suka shigo da sallama, amsa musu tayi tana kallon su, sai kuma tasaki murmushi tana faɗin

“Bari in cinka baƙuwa ta, ƴata Nazeefa sannu da zuwa”.

Ita Nazeefa kallon Mom kawai take yi cike da burgewa, sosai taga kamannin Khalil a fuskarta duk da skin ɗin su ba ɗaya bane, take kuma taji sauran farin cikinta ya dawo mata da ganin matar, muryan Khalil ne yakatse mata tunanin ta

“Mom ai dama kinsan da zuwan ta, ba wani cinka da kika”. Ya faɗa maganar ne lokacin da ya’isa gare ta yazauna agefen ta, ƙara sakin murmushi Mom tayi tace

“To ai bansan ta a fuska ba dai, tunda rowanta kake ta min sai yanzu da kaga daman kawo ta, kinji ƴata ƙariso taho kizauna anan”.

Kanta aƙasa tataho ahankali cike da kunyar matar tazauna agefen ƙafarta

“Ah kin zauna a ƙasa kuma? Taso kizauna anan mana, tashi maza”.

Babu musu kuwa tatashi tazauna agefen ta, yayinda suka saka Mom ɗin a tsakiya, cikin sanyin murya tace

“Ina wuni Mama”.

“Lafiya lau Nazeefa, ya jiki da fatan yanzu kinji sauƙi sosai ko?”

Gyaɗa kanta tayi sai kuma tace

“Alhmadulillah dasauƙi”.

“Allah yasawaƙe, kinga yanzu kin dawo gidan mu, ina fata zakiji daɗin zama dani? Kizauna anan tamkar ƴata daga yau kin zama ƴar gidan nan kema”.

Murmushi kawai Nazeefa tayi tana wasa da yatsunta

“Bari in saka anuna miki inda zaki zauna ko? Kisaki jikin ki kinji daga yanzu na zama mahaifiya gare ki”.

Gyaɗa kanta tayi tana jindaɗi aranta, sosai matar tayi mata, gata mace me fara’a ko kaɗan ba ƙyama a ranta, nan Mom tayi kiran me aikinta, tana zuwa tace “tatafi da Nazeefa takai ta ɗakin da tasanya ta gyarawa, bayan sun tafi ne takalli Khalil da tun soma maganar nasu yaciro wayansa yana latsawa tace

“Kai masha Allah, yarinyan gata kyakykyawa, daga gani tana da hankali da nutsuwa, da alama dai zanji daɗin zama da ita, har naji tashiga raina sosai wlh tamkar ƴata ta cikina”.

Ɗan ɗago kan sa yayi yakalle ta, sai kuma yamaida idanun sa kan wayan yaɗan latsa ta kaɗan yasaka cikin aljihun gaban rigan sa yace

“Ni zan tafi Mom, ba zama zanyi ba ina da wani aiki kinsan gobe ne tafiyana, ina son inje wani waje ne”. Yaƙarike maganar yana miƙewa tsaye

Mom tace “to shikenan, amma dai zaka dawo ko zuwa anjima ne don muyi hira, bana son katafi bamu sake haɗuwa ba kaji ko?”

Murmushi yasaki me kyau da burgewa, yaduƙo gaban ta yasakar mata kiss agoshi yaɗago yana kallon ta yace

“Mom ai dole ne nadawo muyi sallama, idan ma ban sami dawowa yau ba da safe zan dawo kinji”.

Itama murmushi tayi tace

Ok Autana, kasan yanzu ma drever yatafi ɗauko Dad ɗin ku a airport”.

Ɗan waro idanu yayi yace

“Dagaske Mom?”

Hararan sa tayi tana jan kumatun sa tace

“Da ƙarya”.

Dariya yayi yace

“Sorry Mom, bari in zauna to in jira sa”.

“A’a tashi katafi, kai da baka da lokaci, katafi zuwa anjiman in kadawo sai kazo ko kuma goben kamar yanda kace”.

“Ok Mom ni na tafi, ki miƙa masa gaisuwa ta kafin nadawo, kice masa kuma ya’ajiye min tsarabata da kyau zanzo in amsa da kaina, kar yasoma yaba Bro”.

Dariya sukayi gaba ɗayan su, sai da yasake mata kiss a goshi kafin yafice yana faɗin

“Mom byeee”.

.

******* ******* ****

Ƙarfe 05:11pm. Halwa ce zaune bakin ƙofa tana yankan ƙunba wani yaro yashigo gidan yace

“Wai ance Halwa tazo?”

Ɗago kai tayi takalli yaron sai tamayar da idanunta kan yankan ƙunban da take yi tace

“In ji wane?”

“Wani ne a mota”.

Shiru tayi taci gaba da abinda take yi, yaron kuma yatsaya yana kallon ta, daga cikin ɗaki Mama tace

“Wai inace dake akeyi Halwa?”

“Mama ƙyale shi yatafi, kai kaje kace bata nan”. Tafaɗi hakan lokacin da tasake ɗago kanta takalli yaron

Har ya juya zai tafi Mama tace

“Kai yaron nan yimaza kaje kace gata nan zuwa”.

“To”. Yaron yafaɗa yana rugawa waje da gudu

“Kitashi kiwuce kitafi da Allah bansan wulaƙanci”.

Zumɓuro baki tayi kamar Maman tana ganin ta tamiƙe tashige ɗaki sai magana take yi ƙasa-ƙasa, Mama kamar taji me take cewa tace

“Ke kenan kullum koran samari, inace dai dole sai an ɗaura miki aure da Nuran shine kin zama mallakin shi? Kaji min shashashan yarinya haka ake yi”.

Halwa da tafito daga ɗaki riƙe da gyale a hannu tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button