BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

“To Mama meye amfanin fitan nawa tunda inada wanda nake so?”

“Kinci gidan ku, ai babu yanda Allah baya sanja ƙuduran sa, kuma fitan ki ai ba zai hana kisami wanda kikeso ba, Ni wulaƙanci ne bana so wlh, in kin fita sai kice mishi kar yasake dawowa ba shikenan ba?”.

Yafa gyalen tayi kan doguwar rigan ta na atamfa me ruwan toka da akai mishi sirki da ja da milk, slippers tasanya tafice batare da tabi takan Mama dake ta surutu ba.

[9/3/2020, 7:51 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*????

         *⚜{{F.W.A????}}*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 12*

Tana fitowa suka haɗa idanu da Yazeed da yake jingine jikin motan sa, tun sanda tafito yasoma murmushi har ta ƙari so wajen sa da sallama a bakin ta, amsa mata yayi still yana murmushi yace

“Barka da fitowa gimbiyar Mata kyakykyawar yarinya”.

Murmushi tayi tace “fatan kazo lafiya?”

Yace “tun sanda dai muka haɗu dake ban sake jin lafiya ajikina ba, har kuwa fitowar da nayi daga gida nazo gare ki, but yanzu da nagan ki agabana sai naji kamar an kwaso duk lafiyan mutanen duniya ne an ɗaura min ni kaɗai, kinga kuwa yanzu zan iya ce miki lafiya ƙalau kenan”.

Murmusawa tayi tana kallon shi tace

“Na kula dai kai ɗin nan kana da son wasa da yawa”.

Shima murmushin yayi yace

“Gaskiya ne ƴan mata, to fatan kina lafiya kema? Ya su Mama da kowa da kowa? Kinga ban zo ba sai yau ko? Wlh kwana biyun nan aiki ne yayi min yawa, amma baki ji yanda na azabtu ba da rashin ki, ji nake kamar na shekara ɗari tare dake, sosai nashiga damuwa Burina kawai nazo nasake tozali da kyakykyawar fuskar nan taki”.

Ita dai batace komi ba sai murmushi da take yi

“Ƴan mata da fatan dai za’a bani matsuguni acikin zuciyar ki, wlh sosai nakamu da ƙaunar ki, ina fata dai babu wanda yariga ni?”

Halwa tace “ai tun farko kamar in ban manta ba sai da nafaɗa maka ni ɗin mallakin wani ne, sai dai in baka haƙuri Malam Yazeed domin ma fitowan nan da nayi nazo ne nasanar maka an riga da anyi min miji”.

Cikin fuskar damuwa yace

“Dan Allah wai dagaske kike yi?”

“Wlh dagske nake maka, ina da mijin aure kuma nan ba da daɗewa ba za’a sanya mana ranan aure ni dashi”.

Cike da rashin jin daɗi Yazeed yace

“Yanzu shikenan wani ya rigani? Shikenan kina nufin zan rasa ki? Wlh Halwa sosai na kamu da ƙaunar ki a lokaci guda, yanzu kuma bansan ya zanyi in cire son ki cikin zuciyata ba”.

Cike da tausayin sa saboda sosai tayarda dashi kuma ta ga tsantsan gaskiyar sa a fuskar sa tace

“Kayi haƙuri a sannu zaka manta dani ai, dama baka daɗe da sani na ba, don haka insha Allahu nan ba da jimawa ba zaka neme ni karasa ko tuna ni bazaka sake yi ba”.

Ɗan murmushin gefen baki yasaki yace

“Kayya a naki fahimtar kenan Halwa, wlh bakisan yanda nake jin ki cikin zuciyata bane zai yi wuya nacire ki sabida ƙaunar da nake miki ya wuce tunanin ki, ni kinga ban iya saka abu cikin rai ba, kuma zan faɗamiki gaskiya ta kece macen da nafara so nafara kulawa a matsayin wacce nake ƙauna, taya kike tunanin lokaci ɗaya kuma zan inya manta ki?”

Girgiza kan shi yayi sannan yace

“Nagode sosai da faɗamin gaskiya da kikayi, Nagode da baki bar ni nasha wahala ba kinji?”

Gyaɗa masa kai kawai tayi

“To yanzu sai yaushe kuma? Ko bazamu sake haɗuwa ba? Yakamata muyi zumunci don Allah kibani numbanki”.

Bata musa ba tace “ok babu damuwa”.

Takaranto mishi numaban kafin tace

“Ni zan shiga gida, sai wani lokacin kuma”.

Yace “to Nagode sai kin ji ni a wayan kenan, kigaida su Mama”.

Kanta kawai tagyaɗa masa tajuya zata tafi, kawai tayi tuntuɓe da dutse hakan yasaka tayi taga-taga zata faɗi shi kuma yayi saurin taro ta, dai-dai lokacin da Nura yashanyo kwana yagansu ahaka Yazeed ya riƙo ta, kuma sun ƙame ahaka suna kallon juna, wani irin baƙin ciki ne yatokari zuciyar shi, take yaji kishi ya kama shi, tsayawa kawai yayi yana kallon su har sanda yasake ta suka yi magana ita kuma tashige ciki, take yaji zuciyar shi tana faɗin

“Daman yaudaran ka take yi abinda take aikatawa kenan, yau Allah ya toni asirin ta”.

Take kuma yatuna da abinda yafaru jiya, nan yaharhaɗa abubuwan nan da nan yaji zuciyar shi na tafarfasa, aransa yace

“Tabbas dole nayi tunani akan maganar ka, wannan dama ce tasame ni”.

Daga haka yasoma takowa yanufi gidan nasu, yana shiga suka haɗa idanu da Halwa dake tsaye bakin ƙofa tana magana da Mama da har yanzu take cikin ɗaki, murmushi tasakar mishi tace

“Yaya har ka dawo?”

Ɗan dai-dai ta fuskar sa yayi shima yasakar mata murmushin yanufo ta yana faɗin

“Kinga na dawo da wuri ko?”

“A’a Yaya, amma dai Allah yasa an dace?”

Mama da tafito daga ɗaki itama tace

“Da fatan dai an sami abinda akaje nema?”

Shiru yayi na ɗan wani lokaci, yayinda duk kan su suka zuba mishi idanu suna jiran amsan shi, sai kuma yasaki murmushi yace

“Yau dai an dace, na sami aiki insha Allah komi ya wuce”.

“Alhamdulillah”.

Atare suka faɗa hakan, Mama har da shafa hannu saman fuskarta, yayinda Halwa tasaki fara’a tana me cike da farin ciki da jindaɗi

Sallaman Baba yakatse Mama dake faɗin

“Masha Allah. Allah Ubangiji yasanya alkhairi”.

Amsa mishi sallaman suka yi, yaƙariso yana kallon su yace

“Ya naga kunyi cirko-cirko daku, wani abun ya faru ne?”

“Malam ɗan ka yau yasamu aikin dai da yadaɗe yana shan wahala, yau an dace”.

Fara’a Baba yasaki yace

“Ah masha Allah, da kyau Allah yatabbatar da alkhairi”.

“Ameen duk kan su suka amsa, kafin Mama tace

“Bari in kawo maka tabarma Malam”.

Ɗaki tashige taɗauko tashimfiɗa masa yazauna, itama tazauna gefen shi yayinda Halwa tazauna kan dokin ƙofa tana cire gyalen jikinta tajefa ɗaki, Yaya Nura ma zama yayi a saman kujera ƴar zuƙune dake wurin

Baba yace “ina tayaka murna, yau dai gashi ranan da muke jira tazo, to Allah yataimaka yasa kafara a Sa’a”.

Gaba ɗaya suka amsa da “ameen” Baba yaci gaba da cewa

“To yanzu fa an sami abinda ake nema sai kuma aure kenan?”.

Duƙar da kai Nura yayi, ita kuma Halwa wani farin ciki ne yasake kama ta jin maganar Baban

Mama murmusawa tayi tace “gaskiya ne Malam tunda babu abinda za’a jira”.

Baba yace “to insha Allahu nan ba da daɗewa ba za’a tsai da ranan auren, kuma ba wani daɗewa za’ayi ba tunda dama kana aikin ka, mun dai fi so ne kakama na gwamnatin hakan zai fi, tunda gashi an samu shikenan magana ta ƙare zuwa gobe insha Allahu ko jibi za’a tsai da ranan”.

Sosa kai Nura yayi yamiƙe yana faɗin

“Bari inje wajen abokina”.

Dariya Mama tayi tace” ko dai kunya ne zai kora ka?”

Dariya shima yayi yace

“A’a Mama akwai dai abinda zanyi can ne, ni na tafi”. Yafaɗi hakan yana ficewa dasauri

“Ɗan nema za ma kadawo ne, ke kuma me kike jira, ko ke kunyan bata kore ki bane?” Mama tafaɗi hakan tana mayar da idanunta kan Halwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button