BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

Itama tashi tayi da gudu tashige ɗaki tana dariya
Baba yace “ahh ya haka kibar ta mana tazauna, kunyan wa zataji bayan mu ne iyayen ta?”
Dariya Mama tayi tace “bari dai in kawo maka ruwa kashare waɗannan yaran duk gulma ne irin nasu”.
Koda takawo mishi ruwan hira sukaci gaba da yi duk akan maganar samun aikin Nura, da kuma saka ranan su.
.
.
_shin wani abu ne yafaru jiya da har Nura yatuna?_
_Wanene yafaɗa masa maganar da har yace zai yi tunani akai?_
_wani ma magana ce?_
_JIKAR LAWALI CE_ ????
[9/3/2020, 10:48 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written: By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`
*JIKAR LAWALI CE*
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*{{F.W.A????}}*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 13*
*WASHE GARI*
ƙarfe 02:45pm. Drever’n Brr. Ibrahim Khalil yatafi kai shi airport, suna isa ba ɓata lokaci jirgin su yaɗaga dasu zuwa ƙasan Egypt.
_Sai muce Allah yaba da sa’a BARRISTER_????
……. ……. …….. …..
Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, tun sanda yafice gidan tazauna anan palow take ta rizgan kuka, sosai take cikin damuwa abubuwan duk sun haɗe mata, har yau takasa samun mafita, ta kasa samun nasara akan abinda aka saka ta, gashi yanzu mutanen nan sun sako ta gaba, sosai suke mata barazana, gefe ɗaya kuma zuciyarta ta azalzale ta da ƙaunar mutumin da besan tana yi ba, haka kawai take jin baƙin cikin tafiyan nan nasa, shikenan bazata sake ganin sa ba sai sanda yadawo? kuma batasan ranan dawowarsa ba, sai kuma tasake fashewa da kuka tuno mahaifiyar ta da tayi, yanzu da waɗannan mugayen basu ɗauke taba da tuni takoma gida, acan zata zauna har yadawo, “take tatuna sanda yakira ta yana zaune a palow tazo tazuƙuna gaban sa, sai da yagama latsa wayan sa kafin yaɗago kai yakalle ta yace
“Gobe zan yi tafiya, zaki iya komawa gida har sanda zan dawo, kiriƙe wannan ko zaki buƙaci wani abun”.
Yamiƙo mata wasu maƙudan kuɗi, ahankali tasaka hannu ta’amsa tana jin zuciyarta babu daɗi, godiya tayi masa, sannan yabata umarnin “tafiya”
Shiru tayi tana ajiyan zuciya, rufe idanuwanta tayi tana sauraron bugun zuciyarta
“Meyasaka ban faɗamasa halin da nake ciki ba da yatambaye ni zuwa gida? Wataƙil yataimake ni, ya zanyi da waɗannan mutanen”.
Take tasake tuno wayan da sukayi yanzu fitan shi, mutumin da yake kiran ta, shine dai yasake kiran ta yana tambayan ta, “ance zai yi tafiya, ko tasan ina zashi?”
Runtse idanunta tayi wasu hawaye na sulmiyo mata tuna amsan da tabashi
“A’a bansani ba, bansan ma zai yi tafiya ba”.
Mutumin be ce mata komi ba sai yakashe wayan, da alamun kamar wani abun ne yataso shiyasaka yakatse kiran batare da sun gama magana ba, sake runtse idanun ta tayi zuciyarta na ci gaba da bugawa, tasani dole zai sake kira, amma batasan me zai biyo baya ba idan har sukasan ya tafi?
“Wataƙil ma su zo da kansu suyi binciken abinda suke nema”.
Tafaɗi hakan afili tana buɗe idanuwanta, ɗaura kan ta saman kujera tayi tarufe idanunta tana ci gaba da tunani kamar yanda yazame mata jiki yanzu.
.
****** ****** *****
“My dear tashi muje kiraka ni”.
“Ina yaya?” Tatambaye shi tana kallon shi
“Ke dai kitashi kiraka ni, zan amso sabon ɗinki na ne, kuma daga nan sai mu yawata kinsan mun daɗe bamu fita ba”.
Washe baki tayi tace
“hakane Yaya, bari to in sauya kayan jikina”.
“Ok” yace da ita yana zaro wayan sa a aljihu yasoma dannawa
Ita kuma tashige ɗakinta dasauri, tasoma sauya kayan jikinta, wata black and peach colour material me taushi taɗauko daga cikin kayan ta, riga da sket ne sunyi kyau sosai tasaka ajikinta, hakan yasaka kyawun kayan suka sake fitowa sosai sabida yanda yahaɗe da kyan ta, sai da tashafa powder tazizara lipstick a baki sannan tasaka hijabin ta sky maroon da iya kacin sa gwiwa, babu ɗankwali akan ta sai gashinta da tatufke a can ƙasan ƙeyan ta, kasancewar hijabin me hula ne don haka ba’a ganin gashin kanta, flate shoes tasaka kalan baƙi da kwalliyan tuntu asaman me ruwan zamba, fitowa tayi tana faɗin
“Yaya na fito, muje to”.
Ɗago kan sa yayi yana ƙare mata kallo, sai yasaki murmushi yace
“Baby kinyi kyau, kinga yanda yarintan ki yasake fitowa?”
Fari tayi da idanun ta tace
“Dagske yayana?”
“Dagaske mana Dear”.
“Ina kuma zakuje haka?” Cewar Mama da tafito daga ɗaki tana kallon su
“Mama raka ni zatayi, zan amso ɗinkina”.
“To kar dai kudaɗe, nima fita zanyi zuwa sunan Asabe, saura kuma kuje kuzauna inta jiran ki baki dawo ba”.
Nura yace “Mama bazamu daɗe ba ai, sai mun dawo”
Gaba yayi itama Halwa tabi bayan shi tana faɗin
“Mama sai mun dawo”.
“Adawo lafiya”.
Tafiya suke yi a ƙasa suna yi suna hiran su cike da nishaɗi, kallon ta Nura yayi yace
“Ko dai mutaka a ƙasan ne? Naga kamar tafiyan na miki daɗi?”
Ɗan waro idanunta masu kyau tayi tace
“A’a Yaya tare mana dai napep, akwai rana fa a gari”.
“Ok my dear, dama bana son Kisha wahala, gwara dai mutari napep duk da nan kusa ne”.
Lokacin sun iso bakin titi wani me keke napep dake fake ɗan nesa dasu, yatuƙo yaƙariso wajen su yana faɗin
“Tafiya ne?”
Nura ɗan kallon sa yayi suka haɗa ido yace
“Eh bakin kasuwa zaka kai mu?”
“Ok kushiga kuɗin ku saba’in ne”.
“Ai mun sani”. Cewar Halwa tana turo baki gaba
Murmushi Nura yayi yace
“Ke dai da neman magana kike, menene laifin sa anan don yafaɗa miki kuɗin sa?”
“Ai Yaya babu wanda be san kuɗin haka bane, tunda ba yau suka saba kai mu ba, wannan fa doka ce da suka saka kuma kowa yasan da hakan ba sai sun sake maimaita mana ba”. Ta faɗi maganar ne tana shigewa cikin napep ɗin
Me napep ɗin yace
“Baiwar Allah kiyi haƙuri ni baƙo ne ai, nayi tunanin ko baku sani bane”.
Taɓe baki tayi takalli Nura da shima yashigo yazauna a gefen ta tace
“Yaya daga nan mubiya cikin kasuwan mana zan siya kayan kwalliya, nawa sun ƙare”.
“An gama ranki yadaɗe, komi ma kikeso sai kisiya tunda Allah ya kawo mu ko?”
Murmushi tasaki cikin jindaɗi tace
“Eh Yayana, Nagode sosai, ina jindaɗin yanda kake kula dani”.
“Babu komi ai, ke ɗin ƙanwata ce kuma Matata insha Allahu”.
Dariya tayi tana jin farin ciki a zuciyarta, daga nan hira suka soma yi, yayinda me napep tuni yasoma tafiya dama, gab da zasu kawo wajen da za’a sauke su napep ɗin tatsaya
“Oh shitt.. dan Allah kuyi haƙuri bari in duba naga me yafaru”.
Nura yace “ai babu komi, bari musauka anan kawai tunda babu nis..”.
Be gama faɗin abinda yakeson faɗa ba yaji ya shaƙi wani abu cikin hancin sa, ko sceonds biyar basu sake ba gaba ɗaya suka ɓingire cikin motan daga shi har Halwa har suna gwara kai, murmushi me napep ɗin yasaki yajuya yagyara zaman sa yatada keke napep ɗin yaci gaba da tafiya.
.
_Tofa ???? me kuke tunanin zai faru?_
Share this
[ad_2]