BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

“Kai fa?”
“No Mom.. ni sai da aka cika min ciki kafin nafito, kidai ji da wannan sanƙamemen da yaƙi aure yatsaya ɗaura ma mutane ɗawainiya”.
Mom tace “me kake ci na baka na zuba.. kuma wlh kadena takura masa ko yanzu nakora ka inda kafito”.
Dariya yayi yace “oh Mom wasa nake wlh, shi da ma yake da zuƙeƙiyar budurwa sai ma kin ganta Mom”.
Khalil da yake ɗan tsakuran abincin da aka kawo masa ɗago kanshi yayi yana kallon Sameer yace
“Mom karki yarda da maganar sa wlh”.
“A’a bar Ni yafaɗa min, Ni da nakeson inga kayi aure? Kaji bani nasha inajin ka, aina take ne yarinyan?”
“Uhmm awajen aikin su mana Mom, sai kin ganta ma Mom ta bala’in dacewa da ɗan naki, yanda tahaɗu haka tadace da sunan ta, Bilkisu me gadon zinare”.
Washe baki Mom tayi tace “masha Allah.. kace na kusa samun suruka kenan? To Allah yanuna min nidai wannan ranan”.
“Ameen Mom ai nima na ƙosa ranan tazo”.
“Son yaushe zaka kawo min ita naganta?”
Ɓata fuska Khalil yayi yace
“Mom nima ba wani sonta nake ba itace take sona”.
“To ai kaima a sannu zaka so ta karka damu kaji”. Mom tafaɗi hakan tana shafa kanshi
Dariya Sameer yayi yace “hmm Mom ke kin yarda dashi ko? Ni da nakama su suna zance, kullum kikaje fa office ɗin sa sai kin gansu tare”.
Buga abincin Khalil yayi saman table yamiƙe tsaye zai tafi, dasauri Mom tariƙe sa tana faɗin
“Sorry son karka tafi, bari shi in kore sa”.
Juyawa tayi tana kallon Sameer har da ɗan ɗaure fuska tace
“Kama hanya katafi”.
Dariya yayi yace “to Mom amma baki bani abinda yakawo ni ba”.
“Ok yanzu ne kasan da tambayana? Kaje sai anjima zan haɗa sai kazo ka amsar mata, tunda dama kaƙi kadawo da ita nan kai wahala yasama”.
Sameer yace “Mom to me zatazo tayi miki anan? Tunda acan ɗin ma ina kula da ita”.
“To kema Mom kibar masa matar sa mana, inace shi ɗin likita ne kuma yafiki sanin yanda zai kula da ita”.
Khalil yafaɗi hakan yana kai spoon bakin sa, sai kace bashi ne yayi maganar ba”.
Mom tace “rufe min baki, tun kafin a haife ku gaba ɗayan ku nake kula da masu ciki, koda shi likita ne bazai fini sanin yanda zai kula da ita ba, ku kanku babu wanda yataimake Ni lokacin da nake da cikin ku har sanda nahaife ku kuwa”.
“To fa Mom ke da ɗan gaban goshin naki kuma har kun soma ɓatawa?” Sameer yace hakan yana gumtse dariyan sa
Atare suka banko mishi harara yayi saurin tashi yana sakin dariya, yayinda yaɗaga hannayen sa sama yana faɗin
“Babu ruwana nayi nan”.
Yafice da sauri, duk kansu sai da suka murmusa kana sukaci gaba da ɗan taɓa hira a tsakanin su, duk da Khalil baya wani amsa mata wayansa kawai yake latsawa, be wani jima ba shima yayi mata sallama yatafi.
[8/30/2020, 9:09 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*⚜{{F.W.A????}}*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 2*
Ahankali yatura kan motan sa cikin gidan nashi, yaƙarisa parcking space yatsaya, yaɗau 3mint kafin yabuɗe motan yafito, tun sanda yatunkari Compound ɗin gidan yahango bayan ta tana zaune ƙarshen farandan, ga duk kan alamu bata ma san da shigowan sa ba, har zai wuce sai kuma yatsaya yana kallon ta duk da baya ganin face ɗin ta sai bayanta but yasan da akwai abinda ke damunta, shi mutum ne da yake saurin gane damuwar mutum, sau tari aɗan kwanakin nan yana ganin ta cikin wannan hali, sai dai yasan ba hurumin shi bane shiga abun da babu ruwansa, yanzun ma har yafara takawa zuwa wajenta sai kuma yaja yatsaya kana kuma yajuya yashige cikin Palon sa, dai-dai lokacin da ita kuma tasanya hannunta tagoge hawayen da suka zubo kan fuskarta, sosai in kakalle ta zaka hango tsantsan damuwa a tattare da ita, ahankali tamiƙe tanufi cikin gidan, direct kichen tanufa tafara aikin ta, ta ɗau tsawon minti 30 kafin tagama girkin tazuba cikin coolar taje tajera su kan dainning table dake cikin ƙayataccen palon, bayan ta gama tsayawa tayi awajen tayi shiru tana kallon ƙofan ɗakin sa, ta daɗe ahaka sai da taji idanunta sun cicciko da hawaye kafin taɗauke idanunta dasauri tanufi hanyan ɗakinta, akan gadon ta tafaɗa tasaki kuka me tsuma ran me sauraro, ita kaɗai tasan me ke damunta, kuma tasan babu wanda zai iya cire ta daga cikin matsalan da take ciki sai rabbi, domin ita kanta batasan ta ina zata fara aikin da aka sanya ta ba, sai da tayi kukan ta ma’ishi kafin tamiƙe tashige toilet dan ɗauro alwala.
Tunda yashiga ɗakin sa yacire kayan jikinsa direct yashige toilet, ya ɗau tsawon lokaci kafin yafito, yasoma shirya wa cikin sauri, ƙananan kaya yasanya riga sky blue me gajeren hannu wanda tamatse masa Arms ɗin sa, kana yasaka Black trouser, sosai yayi kyau cikin shigan nasa, flate cover shoes yasaka baƙi yafito yanufi masallaci, da tazara sosai da inda gidan sa yake zuwa masallacin, bayan yayi sallan direct gida yanufa yashige ɗakin sa, wani ƙofa yabuɗe yashige, cikin ɗakin kamar Labrary yake, anan yake karatun sa yake duk wani bincike abinda yashafi aikinsa, akan Hill chair yazauna yajawo lapton ɗin sa dake saman table ɗin yabuɗe yasoma aikin sa.
Wajen ƙarfe 06:00pm tafito daga ɗakin ta tanufi kan dainnig table ɗin, gani tayi babu abinda aka taɓa awajen, aran ta tunani take yi ko be dawo bane? Bata da masaniya, dan haka tayanke shawaran fita taduba motan da yafita da ita, koda tafita ta hangi motan yana nan a inda yake, ga kuma sauran nan da alama dai yana gidan, komawa tayi jiki a sanyaye tashige ɗakin ta, dama tafito da ninyan tagirka mishi abincin dare ne.
Sai da yaji an kira sallan magriba kafin yatashi yafito, direct toilet yanufa yaɗauro alwala yafita masallaci, be dawo ba sai da akayi sallan isha’i, koda yashigo gidan kan dainning yanufa yazauna, yahaɗa ma kan sa Black tea yasha, bayan ya gama yaɗan ci abincin kaɗan yatashi yashige ɗaki, sai da yayi wanka yasanya sleeping dress yafeshe jikinsa da farpume’s ɗin sa sannan yazauna gefen gado, briefcase ɗin sa dake ajiye asaman gadon yajawo yaciro wata Black Computer, buɗe wa yayi yasoma aiki, sai da ƙarfe 11:00pm yayi kafin yarufe yakwanta lokacin tuni dama barci yasoma cin ƙarfin sa, yana shafa addu’ar da yayi ko minti 5 be ƙara ba barci yatafi dashi.
……… ………… ………
Washe gari ƙarfe 07:00am Brr. Khalil yagama Shirin sa, yayi shigansa cikin suit black colour, ta cikin kuma white ne, ya sanya socks and black cover shoes, ya gyara gashin kansa sai ƙyalli yake yi gunun sha’awa, gaba ɗaya in banda ƙamshi babu abinda yake tashi ajikin sa, briafcase ɗin sa yaɗauka yafita da sauri ko kallon dainning ɗin da Lubna tagama jera masa break fast be yi ba yafice, ɗaya daga cikin motocin sa kalan sky blue yashiga yaja yafice bayan da Gateman yawangale masa Gate.