BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

Yana fita Lubna tafito daga cikin Toilet ɗaure da showel ajikin ta, kai tsaye inda kayanta yake a sif tanufa taciro wata baƙar doguwar riga me ƙyalƙyalin kwalliya tasaka, tana cikin shafa lotions bayan da tazauna gefen gadon ta taji wayanta yasoma Ringing, dasauri takalli wayan sai da gabanta yafaɗi ganin wanda ke kiran, jikinta na rawa taɗau wayan takara a kunne, bata kai ga cewa komai ba taji muryan sa yana faɗin
“Da fatan kin aikata abinda muka saki?”
Cikin rawan murya tace
“Ban samu dama ba har yanzu”.
“Kina so kice min har yanzu babu wani ci gaba?”
“Ee, har yanzu be bani..”
Katse ta yayi cikin kakkausan murya yace
“Kin san abinda zai biyo baya, karki manta Mahaifiyarki da ƙannin ki..”
Sai kuma yakece da dariya
“Uhmm kinsan sauran, kuma kinsan bazan tsaya jiranki har lokacin da time zai ƙure mana ba, dake na dogara..”
Daga haka yadatse kiran batare da yabari tasake magana ba, ahankali ta’aje wayan cike da sanyin jiki, kasa ci gaba tayi da shafa man sai ma tashi da tayi tafara zagaye ɗakin tana me cike da tunani, so take tasamu mafita amma har yau zuciyarta tagaza barin ta, tsananin tausayin sa take ji aranta duk da ita zata cutu, wani ɓangare na zuciyanta tace
“Haba Lubna kifarka daga mafarkin da kike yi, karki manta fa babu abunda yahaɗa ki dashi, kuma kimanta da wata alaƙan dake tsakanin zuciyarki dashi, ki ceto Mahaifiyarki da ƙannin ki daga halaka, idan har kinyi hakan babu cutarwa a wajen shi, kuma hakan shine dai-dai”.
Wannan tunanin yasaka tayi saurin fita tadoshi ɗakin sa cike da tunani kala-kala.
[8/30/2020, 9:14 PM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*⚜{{F.W.A????}}*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 3*
Har ta kama handle ɗin ƙofan zata murɗa sai kuma tayi saurin saki tajuya dasauri tasauke idanunta kan tanƙamemen agogon dake manne can saman bango, ƙarfe 07:25am hakan yasaka tasauke ajiyan zuciya don tasan babu shi yariga ya fita, ahankali tamurɗa tashige tasoma dube-duben drowers da sif ɗin sa, ta daɗe tana dube-dube cikin ɗakin bata ga komi ba, ƙarisawa tayi jikin ƙofan da yake shiga yayi aikin sa tare da aje duk wasu muhimman abubuwan sa, tana taɓa ƙofan kamar ko yaushe a kulle yake hakan yasaka tajuya jiki a sanyaye tasoma gyaran cikin bedroom ɗin, bayan ta gama tawanke toilet sannan tafito palow, nan ma sai da tagyara ko ina kafin tanufi ɗakin ta.
…. …. ….. …. …. ….
Nocking ƙofan da akayi ne yasaka shi ɗan tsakaitawa daga aikin da yake cikin Computer
“Yas come in”. Yabada umarni yana ci gaba da aikin sa
Ahankali taturo ƙofan tashigo, sai da tajingina da ƙofan tana ƙare mishi kallo na 30soconds kafin daga bisani tasoma takowa cikin office ɗin tanemi kujera tazauna inda aka tanada don baƙi, shiru tayi taci gaba da kallon sa batare da tayi magana ba, sam bata gajiya da kallon shi sabida sosai take mutuwar ƙaunar shi, komi nashi me kyau ne ba inda yake da makusa, ya haɗu ne tako ina duk da kasancewar shi baya da farar fata but skin ɗin sa irin golden colour ɗin nan ne me shaining, yana da kyawun fuska wanda yake zagaye da ɗan siririn saje baƙi siɗik gunun sha’awa, idanuwansa farare ne ƙal kamar zaiba, yana da dogon hanci har zuwa ɗan madaidaicin bakin sa me ban sha’awa da ƙananun lips, shi ma’abocin barin suma ne me tarin yawa, don haka koda yaushe sai dai kaganshi yayi gyaran fuska ba dai yayi aski ba, yana da tsayi sosai da faɗin chest kuma yana da ɗan jiki don baza’a kira sa siriri ba.
“Wai lafiya kika tasani gaba kike kallona?” Muryan shi takatse mata tunanin ta da take yi a kansa
Ɗan firgigit tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin tasaki yalwataccen murmushin da yaƙara ma face ɗin ta kyau, cikin sanyin murya tace
“Koda yaushe bana gajiya da kallon ka ne My Ib, Burina ako yaushe kakasance mallakina ni Ni kaɗai, ina Son ka da yawa My Ib, har yaushe ne zan ta jiranka kayarda dani a matsayin wacce zata zama abokiyar rayuwanka? Yaushe ne nima zaka nuna min ƙauna kamar yanda nake tsananin ƙaunarka da begen ka? Yaushe zaka tausaya min kaji ƙaina kagane babu wacce tafini ƙaunarka a faɗin duniyar nan?”.
Duk maganar da take yin nan idanuwanta na kansa batare da ko kaɗan ta ƙifta su ba, hakan yasaka har ƙwalla suka taru cikin idanun suna shirin zubowa
Sai lokacin yaɗago kanshi yasauke idanunshi cikin nata, dai-dai da lokacin da wasu siraran hawaye suka ɗigo saman kuncin ta, tsira mata idanun sa masu matuƙar kaifi da kyawu yayi na ɗan wani lokaci kafin yaɗauke kai yaci gaba da aikin sa, cikin sweet voice ɗin sa yace
“Bilkisu wai yaushe ne zaki fahimce ni nima? Kigane nifa bazan iya ɓata time ɗina kan wani soyayya ba”.
Ɗan tsakaitawa da maganan yayi kafin yace
“Please ki dena ɓata lokacin ki akan wanann batun, yanzu ki koma kije kiyi aikin ki, ina Son yau ki kamalla komi ki kawo min”.
Lumshe idanuwanta tayi tabuɗe su akan shi, duk maganganun da yafaɗa bakin sa kawai take kallo, sosai take jin daɗi idan yakira sunan ta don ji take yi kamar yafi kowa iya faɗan sunan
Nocking door ɗin akayi yabada umarnin shigowa, abokin sa Brr. Tahir ne yashigo, ita kuma Bilkisu tatashi tafice batare da tasake cewa komi ba, inda tatashi yazauna yana sakin murmushi yace
“Guy ya naga ta fita kuma? Kar dai ace laifina ne na katse muku jindaɗin ku?”
Brr. Khalil ɗago kan sa yayi yasauke mishi wani kallo kafin yace
“Wai meyasa kai in bakayi tsegumi kamar mace bane baka jindaɗi?”
Barr. Tahir dariya yayi yace
“To menene na tsegumi kuma? Akan kai da Billy ne zan yi tsegumi? Uhmm gaskiya ce fa kai na kula baka son ta ko kaɗan, Ni wlh na rasa meyasaka yarinyan nan tanace akan dole sai tasame ka, meye amfanin tsayawa wajen da ake wulaƙanta ta, ga waɗanda suka dace da ita suke son ta tsakani da Allah but taƙi su tana tusa kanta inda bazata taɓa karɓuwa ba”.
“Ok na gane, kafito fili kawai kace min kai kana ciki ba wai katsaya kana faɗamin baƙa ba”.
Brr. Khalil yafaɗi hakan yana yatsina fuska
“Ohh sorry abokina wasa fa nake maka, Ni dama nasan kana son yarinyan nan, kawai halinka ne yasaka bazaka iya nuna mata ba, but ni dai shawaran da zan baka Please and please Ib kadena wahal da yarinyan nan katausaya mata,
Tsaki Brr. Khalil yayi yana kau da kansa yaci gaba da aikin sa, shi kuma Brr. Tahir murmusawa yayi yace
“Uhmm kai dai gaskiya ne baka so abokina amma ni banga makusa kan Billy da har zaka ƙi ta ba, yakamata kadawo tunanin ka kasan masoyin ka Ib”.
“Please kafita kabani waje kana damuwana da banzan surutunka”.
Brr. Khalil yafaɗi hakan yana ɗago kan sa fuskarshi a ɗaure
Dariya Brr. Tahir yayi yace