BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

“Sannu da zuwa yaya”.
Tace dashi tana gyara zaman ta dakyau
“Yauwa.. kinci abinci?”
“Eh Yaya”.
“Ok.”
Shiru yagibta a tsakanin su na ɗan wani lokaci kafin yaɗago da kansa daga duba wayan sa yana kallon ta yace
“Kije kikwanta dare yayi, ki kira min Lubna”.
tace “to”.
Tamiƙe tawuce ciki, Lubna ce tafito taƙariso kusa dashi
“Kihaɗa min Coffee”.
Amsa mishi tayi kawai tawuce cikin kichen, shima tashi yayi yanufi ɗakin sa, ko 2mint be yi ba yafito riƙe da briafcase ɗin sa, yana zama itama tafito tamiƙa mishi takoma ciki, ahankali yasoma aikin sa cikin Computer yana yi yana sipping ɗin Coffee ɗin, har wajen ƙarfe 11:00pm yana nan zaune cikin Palon be gama abinda yake ba, can yaji ihu cikin ɗakin su Lubna, ɗan tsakaitawa yayi daga latsa Computern da yake yi yana kasa kunne.
[8/31/2020, 8:26 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*⚜{{F.W.A????}}*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
_wannan shafin naku ne masoya Littafina, ina jin daɗin yanda kuke nuna ma Book ɗina ƙauna, thank you._ ❤️
.
*CHAPTER 5*
Tashi yayi yanufi ɗakin yabuɗe yashiga, duhu ne ako ina hakan yasaka yalaluba makunnin wutan ɗakin yakunna ko ina yagame da haske, akan ta yasauke idanun sa tana zaune saman gadon babu inda jikinta baya rawa, gefen ta yakalla yaga Nazeefa na kwance sai sharan barcin ta take yi ko motsi batayi ba, maida kyawawan idanun sa yayi akanta da itama tazuba nata cikin nashi sai ɓari take yi, ahankali kamar baya son magana yace
“Menene kike ihu cikin dare? Lafiyan ki ƙalau kuwa?”
Cikin rawan murya tace
“Mafarki nayi”.
Tsare ta da idanu yayi yana nazarin ta, gaba ɗaya tsoro da firgici ne yabayyana a fuskarta, ɗan numfashi yaja sannan yace
“Wani irin mafarki ne haka da yabaki tsoro?”.
Sharto gumin fuskanta tayi still cikin rawan baki tace
“Am uhm Mafarki nayi ak..akan Mamana”.
“Kina son kije gida kenan?”
Yaje ho mata tambayan tare da ci gaba da faɗin
“Sai in saka drever yakai ki yanzu in kinaso”.
Dasauri tagirgiza mishi kai tana faɗin
“A’a”.
“Ok koma kikwanta, kitabbatar kinyi addu’a tukun”.
Daga haka yajuya yafita bayan yakashe wutan ɗakin, ahankali tasulale takoma takwanta tana jin hawaye na sulalo mata a fuska, cikin raunin murya tace
“Dan Allah karku kashe min su, zan yi duk abinda kukeso”.
Sai kuma tasaka hannu tashare hawayen fuskanta tana tuno fuskar sa a yanzu da yashigo, take wasu hawayen suka shiga sintiri saman fuskanta ahankali tafurta
“Ina matuƙar ƙaunar ka”.
……. ……. ……… ……
Shi kuwa koda yakoma cikin Palon aikin sa yaci gaba da yi, be fi 20minutes ba yatashi yashige ɗakin sa, sai da yayi wanka yashirya cikin kayan barci farare sol yafeshe jikinsa da turare sai zuba ƙamshi yake yi kamar wanda yayi wanka dashi, kwanciya yayi yayinda fuskar sa ke kallon cilling ɗin ɗakin, yaɗaura kan sa saman dantsen hannun sa yayi matashi tare da lumshe idanun sa, ahankali yabuɗe idanunsa yana ƙure cilling ɗin ɗakin da ido, tunani yake yi cikin ransa, ya daɗe ahaka batare da yaji barci yazo mishi ba, ganin haka yasaka shi tashi yanufi Toilet yaɗauro alwala yazo yatada sallah yafara jero nafiloli, sai da yadaɗe yana Sallah kafin yasoma jin barci yatashi yahau gado yayi addu’a yarufe idanunsa, ba jimawa kuwa barci yasure sa.
.
****** ****** ******
Tsaye take a bakin titi tana jiran keke napep, tana sanye da uniform ɗin makaranta, riga da wando farare, sai ɗan ƙaramin Hijab kalan ruwan goro, sosai kayan suka yi mata kyau kuma suka ƙara fito da zallan yarintan ta da kyawun surar ta, school bag ɗin ta dake rataye a kafaɗan ta tazamo shi cike da gajiyawa, sosai ranan wajen yake dukan ta, tun ɗazu tana tsaye amma har yanzu bata sami abin hawa ba, gashi har abokan tafiyanta sun watse ita tana nan tsaye ba yau ba gobe, yatsina fuskarta tayi taɗan ɗaga face ɗin ta tana kallon ƙwallelen ranan da yasake fantsamo wa, bata kai ga sauke kanta ba taji hon ɗin mota a gefen ta, dasauri tasauke kanta taɗaura idanunta saman motan dake tsaye ɗan nesa da ita, cikin socond ɗin da be wuce 3 ba takalli motan taɗauke kanta, wanda ke cikin motan ne yafito ɗan kyakkyawan sauri ne yatunkaro inda take
“Assalamu alaikum”. Yayi mata sallama yana kallon fuskarta da yake a yatsine
Bata kalle sa ba taɗan yamutsa fuska tana motsa ƙaramin bakin ta, hakan yasaka yaɗan saki murmushi yace
“Baiwar Allah da fatan dai ba laifi nayi ba da ban samu an amsa min sallama ba? Duk da nasan be dace natare ki anan ba, amma kuma babu yanda na iya ne tunda bazan iya bari kisuɓuce min ba”.
Kallon sa tayi fuskanta a yatsine ga duk kan alamu hakan ya zame mata jiki ne, batace komi ba sai gyara zaman jakan ta da tayi tana kallon hanya
“Baiwar Allah ko dai ke kurma ce?” Yasake tambayan ta still yana kallon ta
Ahankali tagyaɗa masa kai tana ɗan kwaɓe fuska kamar zata yi kuka
“Ayya sorry rashin sani akace yafi dare duhu, kiyi haƙuri but ina son insan sunan ki gashi kuma ina son narage miki hanya, to ya za’ayi yanzu?”
Cikin sanyi da muryanta me daɗi tace
“Ce maka akayi ina buƙata?”
Sai kuma tayi saurin kallon sa tana ɗaura hannu abaki tare da zaro idanu waje tace
“Na manta”.
Don ko kaɗan tamanta da yanzu tayi masa ƙaryan ita kurma ce, shi kuwa da yasaki baki yana kallon ta be san sanda yatuntsire da dariya ba yace
“Kai Allah Nagode maka, kinga lokaci ɗaya Allah ya kamaki, sai yasaka ki kika manta kika yi magana, Uhm babu rabon ki wahalar dani kenan, kuma banda abinki ai ƙarya be kamace ki ba, ko kadan bakiyi zubi da masu faɗan magana wanda ba dai-dai ba shiyasa na’amince dake nan take”.
Murmushi kawai tayi tana jin kunya na kama ta, ba haka taso ba, taso in yagane ita kurma ce yatafi yabata waje amma kuma sai gashi asirinta ya tonu
“To yanzu dan Allah kitaimaka kifaɗamin sunan ki, kuma dan Allah karki ƙi tayina muje nasauke ki gida kinga akwai rana kar yayi miki illa, kamar ki kyakkyawa be kamata kina tsaye rana na gasa ki ba, ko ba haka ba?”
Ɗan taɓe baki tayi tace
“Ni fa bansan meyasaka kake faɗamin waɗannan kalaman ba, kuma bansan meyasaka kakeson taimako na ba, meyasa zaka damu idan rana tagasa ni? Baka tunanin nafison hakan ne shiyasaka nazaɓi tsayuwa anan ɗin?”
Murmusawa yayi yace
“Ai banga aibu ba idan har nataimake ki, kuma kinsan da cewa duk namiji idan har yaga mace ahanya yanemi yataimake ta to akwai abinda yake so wajenta ne, kuma kema kinsan da haka sai dai in bazaki faɗa ba”.
“Zai fi kyau dai kasanar dani da bakinka, tunda nasan da cewa Maza kala da iri ne kuma ko wannen su da abinda ke kawo su wajen yarinya, to kai kuma bansan menene yakawo ka ba”.
Ɗan numfashi yaja yana kallon ta cike da burgewa yace