BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

“Tunda kinfi son sai nafaɗa miki dalla-dalla to shikenan, Ni sunana Yazeed tunda Ni kinyi min ruwan sunan ki, kuma abinda yatsai dani wajen ki so da ƙauna ne, tun sanda naƙyalla idanu na naganki naji zuciyata ta kamu da matsananciyan ƙaunarki, kuma wlh ba da wasa nake miki ba, ina son kibani dama Dan Allah na nuna miki irin yanda kika shiga zuciyata kika mamaye min ita acikin mintuna ƙalilan kinji dan Allah”.
Ɗan gajeren murmushi tayi kana tace
“Ayya Malam Yazeed Nagode da ƙaunarka gare ni, sai dai ina tunanin ka makaro domin Ni ɗin nan da kake gani tuni na zama mallakin wanin ka, ina faɗa maka wannan maganan ne don kar nawahal da kai”.
Murmushi yasaki cike da rashin yarda yace
“To shikenan amma dai kizo muje nasauke ki mana, dan Allah karkice a’a plz ƴar kyakykyawa”.
Batasan sanda tasaki murmushi ba takalle sa tace
“Uhm kana son kayi min daɗin baki ko?”.
“Ai gaskiya nafaɗa ƴan mata, ko makaho yashafa yasan akwai kyau anan”.
Taɓe bakinta tayi tace “to muje”.
Gaba yayi yabuɗe mata gaban motan tashige, shima yazaga yashiga yaja motan, sai da yadaidaita motar tasa asaman kwalta ɗin kafin yace
“Har yanzu dai anƙi sanar dani sunan Gimbiyan, sai faman rowa ake min” .
Murmushi kawai tayi ataƙaice tace
“HALWA”.
“Wow nice name, Gaskiya sunan yadace dake sosai, Masha Allah suna me daɗi”.
“Ko?”
Yace “eh mana, ko bakisan da haka bane?”
Batayi magana ba sai murmushi da tasaki me sauti, daga haka yayi ta jan ta da surutu ita kuma tana amsa mishi wasu kuma iyakan tayi murmushi kawai, har bakin layin gidan su yakaita tace “ya aje ta nan”.
Bayan yayi packing ɗin motan yajuyo yana kallonta yace
“To bakiso nakai ki har ƙofar gida ne?”
Ɗan kallon sa tayi tagyaɗa masa kai
“Meyasa to?”
“Babu komi”. Ta’amsa mishi ataƙaice
“Uhmmm ko dai bakiso nahaɗu da saurayin ki ne?”
Turo bakin ta gaba tayi sai kuma tataɓe shi tace
“Ba laifi bane hakan ai tunda na sanar da kai dama”.
Murmushi yayi yace
“Gaskiya ne, to yanzu bani Numbanki mana tunda kinga ban sauke ki har gida ba, kar kuma yanzu in kin tafi shikenan na rasa ki”.
“Hmm tunda har kakawo ni nan ai kamar kakawo Ni gida ne, babu wanda zaka tambaya anan wajen be kai ka gidan mu ba idan har kafaɗa masa suna na, kuma gidan mu ai ba ɓoyayye bane, kana cewa gidan Malam Ayuba za’a kawo ka”.
Yazeed yace “to NUMBAN kuma fa bazan samu ba kenan? Please”. Yaƙarike maganar yana ɗan marairaice fuska
Cike da ƙosawa tace “bani da waya, sai anjima nagode sosai”.
Tabuɗe motan tafito, shi kuma yana ɗaga mata hannu tare da faɗin
“Sai kin ganni kenan ko?”
Kawai gyaɗa masa kai tayi tawuce abin ta, shi kuma yaja motan sa yatafi fuskarsa cike da nishaɗi.
Da sallama tashiga gidan, matar dake zaune tana tatan koko ta’amsa mata tana faɗin
“ƴan makaranta an dawo?”
Cike da gajiyawa taƙarisa kusa da ita tazauna saman turmi tace
“Eh wlh Umma, kin ganni sai yanzu”.
Umma tace “gaskiya ne kinsha hanya, ga uban rana da ake ƙwalla wa ai yau ko da gani kin gaji”.
“Uhmmm Umma bari ke dai, wlh yau nasha wahala ga wuyan abun hawa da ban samu da wuri ba”. Cewar Halwan tana tashi ta’aje jakan ta saman turmin tanufi wajen randan ruwa tabuɗe tana ninyan ɗiba
Umma tace “karki sha wannan ruwan, je ɗakina kiɗauko fure water yanzu na’aiki yara suka siyo min”.
“To Umma”.
Ɗakin tashige sai gata tafito riƙe da fure water’n ahannu tana faɗin
“Umma ya jikin Zainab ɗin?”
“Alhamdulillah dasauƙi sosai, zazzaɓin ya saukar mata ai, tana nan kwance cikin ɗaki inaga ko barci take yi ne?”
“Ok bari in shiga in ganta”.
Ɗaukan jakan ta tayi tashige ɗakin Zainab ɗin, kamar yanda Umma tace kuwa tana kwance tana sharɓan barci duk tayi ɗai-ɗai saman katifan ta sai baza hanci take” bakin gadon tasamu waje tazauna tatsiyaya ruwan ahannun ta tazuba mata a fuska, jin sanyi ya ratsa mata fuska atake tabuɗe idanunta da suka ƙanƙance suka yi ja tana maida su tana rufewa
“To kasa tashi haka barcin ya isa, don nasan ba tun yanzu kike yi ba”.
Ɗan yamutsa fuska Zainab tayi taƙara ware idanunta tana kallon HALWA kana tatashi zaune tana sakin hamma, cike da kasala tace
“Har kin dawo?”
Halwa tace “eh na dawo, ya jikin naki? Umma tace “kin samu sauƙi ko?”
“Eh dasauƙi sosai, dama wlh don kaina ya matsa min ne da babu abinda zai sa naƙi zuwa makaranta”. Zainab ɗin tafaɗi hakan tana zamewa takoma takwanta
“Gaskiya gwara da kika zauna ɗin don yau babu abunda akayi, Monday ma za’a fara test, amma fa ina faɗamiki show ya wuce ki”.
“Dan Allah fa? Ke da mutumin naki?”
Harara Halwa tasakar mata tana yatsina tace
“Banson iskanci fa Zainab, wlh yanzu sai mu ɓata idan kika sake kiran min ɗan iskan nan, mtwww”.
Taja tsaki tana ɗaure fuska tare da huro hanci
Ita kam Zainab dariya tayi tace
“Sorry ƙawalliya roman jaɓa wasa nake miki fa, kinsan ni dake bamu haka, bani labari to me yafaru?”
“Ai kuma baki isa ba wlh tunda kika taɓo ni nafasa baki labarin, kinga Ni tafiya ma zanyi dama na biyo ne don naduba jikin naki, tunda yanzu na ganki garas to kinga tafiyata”.
Tashi tayi tasaɓa jakan ta a kafaɗa tafice, Zainab na kiran ta amma ko waige batayi ba, tana fita taga Umma har yanzu bata gama tatan ba tace
“Umma na tafi”.
“To har zaki tafi? Ina jiran in sauke Dambu nasawo muku kuma?” Umma tace hakan tana kallon Halwa
“A’a Umma kibar sa kawai yau banjin tsayawa ne”.
“To shikenan kigaida gida, kigaishe min da Maman naku”.
“To zataji”.
Daga haka tafice
[8/31/2020, 8:29 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*⚜{{F.W.A????}}*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
“`NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.“`
.
*CHAPTER 6*
Shiga tayi cikin gidan nasu da sallama a bakin ta, Mama da fitowar ta kenan daga ɗaki riƙe da kwano ahannu ta’amsa mata tana kallon ta, ƙarisowa Halwa tayi tana kallon Maman nata da tasami waje saman tabarma tazauna tace
“Mamana sannu da gida”.
“Yauwa ƴata takaina, kin dawo?”.
“Washh.. nagaji wlh Mama”.
Halwa tafaɗa tana zama gefen Maman
“Ai daga ganin yanayin ki nasan da haka, da fatan dai ba wahalan mota ce tatsai dake ba?”
“Shine wlh Mama, kuma sai nabiya gidan su Zainab na je duba jikinta”.
Mama kallonta tayi tace
“To ya ya jikin nata? Ta samu sauƙi dai ko?”
“Alhamdulillah Mama jikin nata ya warware ai sosai, Umma ma na gaishe ki”.
“Tom Ina amsawa, naso ma in shiga in gaishe ta Allah be yiba, sai ki tashi kije kiɗau abincin ki yana ɗakin ki, don nasan tunda kika langaɓe anan sai kizauna kiyi ta zuba bazaki ci ba, kuma nasan da yunwa atattare dake”.
Dariya Halwa tayi tace
“Wlh Mamana shiyasa nake ƙara son ki sabida ƙaunar da kike nuna min, uhm ai yau bazan iya wasa da abinci ba sabida yanda naji hanjin cikina suna kaɗawa, bari dai inje in ɗauko”.