BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 1 to 10

Tamiƙe tsaye tana kwaɓe hijabinta, Mama kuma taɓe baki tayi tace

“Da dai bansan halinki bane, yanzu sai ki jagula kibar shi nan”.

Halwa shigewa ɗaki tayi tana ɗaga murya tace

“Mama banda yanzu dai, kibari kigani har ƙari ma sai kinyi min”.

“To bansan surutu kimaza kiɗauko kizo nan kizauna kici”.

Fitowa tayi riƙe da coolar ahannun ta da wayanta, zama tayi tana tanƙwashe ƙafafunta tasoma danna wayan tana faɗin

“Mama har yanzu Yaya be dawo ba?”

“Ni ban ganshi ba, sai ki neme sa ta waya kiji inda yatsaya”. Cewar Mama tana ci gaba da ɓare maggi

Wayan takara akunni tasoma buɗe coolar’n, hannu tasaka tasoma kai loman abincin dai-dai lokacin da aka ɗaga wayan nata tace

“Wai yaya ina kaje ne har yanzu shiru baka dawo ba?”

“Sorry my Dear, Ina nan kusa naje wajen abokina ne, amma yanzu zaki ganni”.

Ɗan shagwaɓe murya tayi tace

“To kayi sauri kaji?”

“Ok karki damu my dear, Yayanki yakusa dawowa”.

Daga haka sukayi sallama ta’aje wayan gefe, taci gaba da cin abincin tana yi tana zuba ma Mama surutu, ita kam sai Umm take ce mata, Mama da tagama ɓare maggin miƙewa tayi tashige kichen, lokacin ne Nura yayi sallama yashigo, ɗago kanta tayi dai-dai lokacin da ta’afa shinkafan cikin baki tana kuma amsa mishi sallaman

“A’a yi ahankali mana karki ƙware, wannan loma haka sai kace abincin zai gudu”.

Nura yafaɗa hakan yana dariya bayan da yaƙaraso kusa da ita yasami wuri yazauna, ɗan yatsina fuska tayi sai kuma tasakar masa harara tana faɗin

“To aina kaga na zuba loma yaya? Ko bakaga yanda naɗibo bane?”

Ɗan sakin murmushi yayi yana ƙare mata kallo yace

“Na gani mana, ba gashi kin ciko hannu ba kamar wanda take gudun shigowan wasu don halin rowa, nasan fa halin ki Sarkin rowa ce”.

Ture abincin tayi tana ɓata fuska, cikin shagwaɓa tace

“Mama kin gansa ko?”

Daga kichen ɗin Mama ta’amsa mata da faɗin

“Ni kin ganni babu ruwana kunfi kusa, karki sako ni cikin zancen ku”.

Nura dariya yasaki yana mata gwalo, ai ko kawai tasakar masa kuka

“Kai wai me tayi maka ne Nura daga zuwanka zaka sa ta kuka? Bansan haka fa tam”. Cewar Mama kenan tana leƙo kai waje

“Wlh Mama Ni ban mata komai ba kinsan halinta ai bata raina abun kuka, to kiyi shiru mana beuaty daga wasa? kinga nakama kunni na ma”.

Dena kukan tayi tana turo baki gaba tace

“Ai kuma mun ɓata tunda Ni kace ma me rowa”.

Haba ƴar ƙanwata abar ƙauna ta, kiyi haƙuri kiyafe ma yayanki, ban sakewa wlh kinji? Matso da kunnin ki ma kiji wata magana?”

“Me zaka faɗamin?” Tafaɗa tana kallon sa

Murmushi yayi mata yana kashe mata ido ɗaya yace

“Kalaman da kikafi so mana” ko in aje kayana baƙya buƙata?”

“Ina so mana yaya”. Tafaɗi hakan dasauri tana matso da kunnen ta kusa dashi

Magana yaraɗa mata tasaki dariya tana janye kunnen ta, ɗage mata giran sa yayi yace

“To muje mana”.

“To bari in sauya kaya, kaje kajira ni a zaure sai ka’aiko yaro ko?”.

“Eh haka zamuyi”. Nura yafaɗi hakan yana miƙewa dasauri

Itama tashi tayi tashige ɗaki, Mama da tafito daga kichen tabi Halwa da tashige ɗaki da kallo, kana tamaida idanunta kan Nura da yasaka takalmin shi yana shirin ficewa waje tace

“To yanzu kuma me kuka shirya ne na ji kuna ƙus-ƙus?”

Dariya Nura yayi yace

“Zance zamuyi mana Mama, amma yau a zaure zamuyi, zan aiko yaro yakira min ƴar taki, dan Allah karki hanata fita”.

Kama haɓa Mama tayi tabi shi da kallo don takasa cewa komai, shi kuma fita yayi yana faɗin

“Sweety kiyi sauri fa, karki shanya Ni kuma don nasan shegen nawan ki”.

Babu jimawa kuwa Halwa tafito riƙe da ɗankwali da Hijab ahannu, tsayawa tayi tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin

Mama tace “eh haƙiƙa yaran nan dagaske kuke yi, yau kuma gaba ɗayan ku kenan haukan taku tamotsa?”

Halwa dake shirin magana sai ganin yaro tayi ya shigo yana faɗin

“Wai Halwa tazo inji Nura”.

Ƙarisa saka Hijabin ta tayi tana faɗin

“Kai kace gata nan zuwa”.

Sai takalli Mama tace

“To Mama Ni nafita”.

Bata jira jin ta bakin Maman ba tafice dasauri, girgiza kanta kawai Mama tayi tana murmushi tace

“Allah yashirya ku, yaran zamani baku da kunya wlh, ai bari Baban naku yadawo sai ya ji komi”.

.

****** ****** *****

Shigowan ta kenan ɗakin taji wayan ta na ringing dasauri taƙarisa taɗauka tana karawa a kunni

“LUBNA kenan”. Cewar Mutumin da yakira ta yana sakin dariya

Shiru tayi tana sauraron shi, sai dai babu inda jikinta baya rawa, har zuciyanta na wani irin tsalle kamar zai faso ƙirjinta

“Har yanzu dai kin ƙi aikata abinda muka sakaki ko? Da alamun kina son kirasa kowa naki ne”.

Kallon inda Nazeefa take akwance tayi wanda sai sharɓan barcin ta take yi ta ƙudundine jikinta cikin bargo, cikin ƙasa da murya tace

“Dan Allah kuyi haƙuri har yanzu Ban samu nasara bane, wlh kullum sai nashiga nayi muku bincike amma baya barin komi”.

“Kina dai wasa da rayuwan Mahaifiyarki da ta ƙannin ki, domin muddin bakiyi abinda mukasa ki ba zaki rasa su, tun yaushe muka baki aikin nan amma kullum magana ɗaya kike faɗa? To ki saurare ni da kyau, akwai wata yarinya da yakawo ta gidan nan kitabbatar da kin fito da ita cikin gidan nan, zan aiko yarana su ɗauke ta”.

Cikin rawan murya Lubna tace

“Meee? Nazeefa?”

“Yess ita, ita nake so naɗauka, kijira umarni na”.

Ƙitt yakashe wayan, yayinda ita kuma taciro wayan daga kunnen ta tana kallon Nazeefa

“Menene alaƙan su da wannan yarinyan? Me tayi musu? Me suke so da ita?”

Dasauri tamatsa bakin gadon tazauna tana ƙare mata kallo, sai kuma taji kawai hawaye na zubo mata, kifa kanta tayi saman gadon tasoma rera kuka mara sauti

“Meyasaka waɗannan mutanen suka shigo rayuwanta? Me tayi musu ne? Meyasaka sai ita ne zasu zaɓa? Meyasa basuyi tunanin bazata iya aikata duk wannan aikin ba musamman ma akan shi? Tabbas tana da rauni bazata taɓa iyawa ba”.

“Waye zai fitar dani cikin wannan ƙangin?”

Tafaɗi hakan lokacin da taɗago kanta idanuwanta sharkab da hawaye

“Allah gani gare ka kataimake ni”.

Kallon Nazeefa tasake yi kafin tamiƙe ahankali tashige toilet.

.

.

_shin su waye waɗannan mutanen ne?_

_Meyasaka suke takura ma Lubna?_

_meye alaƙan su da Nazeefa?_

 ????????‍♀️ ????????????????????????

[8/31/2020, 8:31 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️

   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*

                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*

_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

⚖️ *FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`{{Ɗaya tamkar da Dubu????}}“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *⚜{{F.W.A????}}*

“`ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH“`

_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._

*SADAUKARWA*

_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*

“`NAFEESAT

LABARIN DEEBIZAH

JARUMAI

RAYUWATA

NUSNIM

BUTULCI

SO MAI ZAFI.“`

.

     *CHAPTER 7*

Ahankali yake taka motan kamar koda yaushe, wayan sa dake ajiye ne tasoma ringing, hannu ɗaya yamiƙa yaɗau wayan bayan da yaduba yaga me kira, picking call ɗin yayi tare da saka ta a speaker ???? yamaida ya’ajiye

“Hello Bro”.

Daga can Sameer yace

“Kana ina da Allah?”

“Yanzu gani na taso wajen aiki zan koma gida”.

Sameer yace “yauwa kazo kaɗauke ni Please, motata ce tasami matsala an tafi da ita, ina office Ina jiran ka”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button